05/16/2024
Wadanda s**a zabi a tura musu NotCoin dinsu a OKX da Bybit tuni ya sauka wasu kuma nasu yana kan sauka yanzun haka, saura wadanda s**a zabi Binance da Telegram Wallet ba'a fara sauke musu ba, amma na kowa zai sauka kafin listing kamar yadda masu NotCoin s**ayi alkawari In sha Allah.
Shawara ga waɗanda s**a zaɓi a tura musu nasu a Telegram wallet idan an fara turawa, ku kaishi Exchange ɗin da basa cikin Exchanges ɗin da Notcoin s**a saka su ayi amfani dasu (wato Binance, OKX, da Bybit), domin za'a samu congestion a wadannan Exchanges ɗin.
Tun jiya da daddare Mukhtar M. Adam yace ya tura TON, da USDT takan Ton Blockchain zuwa Bybit amma har yanzu basu sauka ba, zai iya faruwa da kai idan ka tura Not ɗinka zuwa wannan Exchanges ɗin saboda congestion yayi yawa, shawara mutun ya tura Kucoin, Bitget, MEXC, Gate.io ko dai wata Exchange ɗin wacce bata shiga cikin wanda Notcoin s**a zaɓa ba.
A kula da kyau a saka Memo da wallet address daidai a wajen turawa.
Allah ya bamu sa'a da rabo mai amfani, Amin.
By Chairman ammar 24 and crypto