19/08/2026
STILL ON, CLASH BETWEEN THE CAMP OF REVERED SUNNI ISLAMIC SCHORLAR SHEIKH MURTALA BELLO ASSADA SOKOTO , Sheikh Musa Ayuba Lukawa and the Camp of Mai Barewa.
The ongoing clash between the camps of revered Sunni Islamic scholars, Sheikh Murtala Bello Asada of Sokoto, Sheikh Musa Ayuba Lukawa, and Mai Barewa, has taken a new turn.
In a newly released video shared on Mai Barewa’s TikTok handle, he responds to the circulating video showing Sheikh Murtala Bello Asada shooting a short gun in an open field. Mai Barewa maintained that he is not intimidated by what he described as a “time bomb,” insisting that not even a short gun would stop him from defending the honour of the Noble Prophet Muhammad (S.A.W.).
The controversy reportedly began during a lecture when Sheikh Musa Ayuba Lukawa translated a Hadith of the Prophet (S.A.W.), which Mai Barewa considered derogatory to the personality and honour of the Prophet.
The dispute continues to generate reactions among followers of the two camps.
..............................................................................
Lamarin da ke ci gaba da gudana tsakanin bangarorin fitattun malaman Sunnah, Sheikh Murtala Bello Asada na Sakkwato, Sheikh Musa Ayuba Lukawa da kuma Mai Barewa, ya dauki sabon salo.
A cikin wani sabon bidiyo da anka yi posting a shafin TikTok na Mai Barewa, ya mayar da martani kan wani bidiyon da ke yawo, wanda aka ga Sheikh Murtala Bello Asada yana harbin bindiga a wani fili.
Mai Barewa ya bayyana cewa ba ya jin tsoron abin da ya kira “time bomb”, yana mai cewa ko da gajeriyar bindiga ba za ta hana shi kare mutunci da martabar Manzon Allah Muhammad (S.A.W.) ba.
Rikicin dai ya samo asali ne yayin wani karatu, lokacin da Sheikh Musa Ayuba Lukawa ke fassara wani Hadisi na Manzon Allah (S.A.W.), inda Mai Barewa ya yi zargin cewa kalmomin da aka yi amfani da su sun kasance na batanci ga mutunci da martabar Manzon Allah.
Lamarin na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce da martani daga mabiyan bangarorin biyu.