01/01/2026
JIBWIS YOBE STATE
Lafiya da zaman lafiya sune ginshikokin jin dadin rayuwa
Shugaban Jibwis na Jihar Yobe
Sheikh Imam Yusuf Adam Muhammad Damaturu
Ya yi kira ga dukkan 'ya 'yan kungiyar Izalah reshen Jihar Yobe baki ɗaya, akan su ƙara cigaba da Addu'o'i, Istigfari, sadaka, taimakon Al'umma da yin Alqunutu a masallatan kungiyar domin neman Allah ya bamu zaman lafiya a Jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Lalle muna Godiya ga Allah ya bawa jihar mu kariya da zaman lafiya, to mu ƙara cigaba da Addu'o'i ka'in da na'in sannan kuma 'yan Agajin mu su kara tsaurara tsaro a dukkan masallatan mu na Juma'ah da na Khamsul Salawat da sauran wuraren Ibada da Tarurruka.
Lalle a kula da dukkan shige da fice na Al'umma da Ababan hawa da kuma sa ido akan dukkan abinda ba'a amince da shi ba tare bada haɗin kai ga jami'an tsaro da iyayen ƙasa domin samun nasara.
Allah ya bamu zaman lafiya, Allah ya tsare mu daga dukkan sharrin masu Sharri da makirai da munafukai.
Jibwis Yobe State
Jibwis Social media Yobe State Directorate
12 Rajab, 1447
1 January, 2026