17/02/2026
SAƘON TAYA MURNA
Ni, Mustapha Bashiru, a matsayina na Chairman na DURUMBU FOUNDATION, ina miƙa saƙon taya murna na musamman ga Comrade Anas Haidara (Kaura Namoda – Durunbu Sabon Gari) bisa samun ƙaruwa da Allah Ya yi masa na haihuwar ɗa namiji.
Wannan babban ni’ima ce daga Allah (SWT), kuma muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya jaririn ya zama mai albarka, Ya ba shi tsawon rai, lafiya, da kyakkyawan tarbiyya bisa koyarwar Musulunci. Allah Ya sanya shi farin ciki ga iyayensa da al’umma baki ɗaya.
Muna addu’ar Allah Ya raya shi cikin imani da tsoronSa, Ya kuma sanya shi daga cikin bayinSa nagari.
Ameen Ya Rabbal Alameen 🤲
ibraheem mk
DURUMBU FOUNDATION