Arewa mufarka

Arewa mufarka Yan mufarka 🙏🙏🙏


Nigeria. ✊✊✊


Yanci zallah 👊👊👊

In Sha Allah. 🥰🥰🥰

04/05/2026

Yanzu Yanzu Social Media Zata Dauka
Muhammadur Rasolillah

04/05/2026

Muhammad Rasulullah

Tsohon da aka dasawa ƴan Arewa yana tasiriIdan manyan shugabannin ƙasa da yan ƙasa suna tsoron shugaban ƙasa, wannan yaw...
03/04/2026

Tsohon da aka dasawa ƴan Arewa yana tasiri

Idan manyan shugabannin ƙasa da yan ƙasa suna tsoron shugaban ƙasa, wannan yawanci yana haifar da raguwar daidaito da tsari na dimokuradiyya, inda gwamnati ke komawa tsarin mulki na tsakiya, wato mulkin k**a-karya. Wannan yanayin, wanda ake kira “jagoranci bisa tsoro,” yana haifar da wasu sak**ako na siyasa da na hukuma.
Dangane da ƙa’idojin kimiyyar siyasa da halayyar kungiya,
ga abin da yakan faru
Biyayya da Rashin Musuƙanci: Masu ƙarƙashin jagoranci (membobin majalisa, ministoci, jami’ai) suna daina bayar da ra’ayoyi na gaskiya ko adawa da mummunan shawara, wanda ake kira al’adar “e, e” ko bin uwar daka.
Ƙarfi yana taruwa a hannun shugaban ƙasa, wanda ke sa yanke shawara ya yi sauri amma yana toshe sabbin hanyoyin aiki da ƙirƙira.Jami’ai suna fi mai da hankali kan ceton kansu fiye da muradin jama’a, wanda ke janyo raguwar amincewa a cikin hukumomi.
Canjin Ma’aikata Akai-akai: Jagoranci bisa tsoro yana haifar da yawan sauyin manyan jami’ai waɗanda ake korar su ko kuma su kan bar hukuma saboda matsin lamba.
Gazawar Manufofi: Rashin samun s**ar gina-gina yana sa gwamnati ta fuskanci sak**akon kuskuren wanda ke yanke shawara shi kaɗai.
Boyewa ko Rufe Bayanan: Shugabanni na iya ɓoye labarai marasa kyau ko matsaloli daga shugaban ƙasa, wanda ke haifar da ra’ayi mara gaskiya, mai rufe kansa, da haɗari.
Ƙara Hadarin Siyasa: Dogaro da tsoro da rashin tsayayyen hukuma na iya janyo matsaloli na dogon lokaci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na ƙasa.
A takaice, idan shugabanni da yan ƙasa suna tsoron shugaban ƙasa, gwamnati tana aiki ne ta hanyar tsoratarwa maimakon haɗin kai, wanda zai iya haifar da rugujewar ingancin manufofi da rashin ɗaukar alhakin dimokuradiyya.

Idan zamu farka mufarka idan kuma bazamu farkaba, tabbas zamu wuce barzahu daga bacci.

Mai yasa yaƙin Iran da Amurka da Israel zai shafi Nigeria!?Najeriya babbar ƙasa ce mai fitar da ɗanyen mai, tana ɗaya da...
03/04/2026

Mai yasa yaƙin Iran da Amurka da Israel zai shafi Nigeria!?

Najeriya babbar ƙasa ce mai fitar da ɗanyen mai, tana ɗaya daga cikin manyan masu fitar da mai a duniya. A shekarar 2024, darajar fitar da ɗanyen mai ta haura dala biliyan 40, inda yawan mai da ake fitarwa a kullum ke wucewa ganga miliyan 1.5. Najeriya ita ce mafi girma a Afirka wajen samar da mai, kuma manyan ƙasashen da ke siya sun haɗa da Spain, India, Faransa, da Amurka.
A ƙarshen 2024, rahotanni sun nuna cewa Najeriya na fitar da kusan ganga miliyan 1.5 a rana.
A 2024, Najeriya ta fitar da ɗanyen mai mai darajar dala biliyan 40.5.
Kudaden Shiga a 2025: Najeriya ta samu kusan ₦47.43 tiriliyan daga fitar da ɗanyen mai a 2025.
Manyan Masu Siya: Spain, Amurka, Faransa, India, da Indunusiya.
Najeriya ita ce ta 10 a jerin manyan masu fitar da ɗanyen mai a duniya.
Dalilin Fitarwa: Ɗanyen mai yana wakiltar kusan kaso 80% na darajar dukkan fitarwar Najeriya a farkon 2024.
Ci Gaban Sabon Tsari: Najeriya na ci gaba da haɓaka kayan aiki, k**ar FSO Cawthorne, don ƙara ƙarfin fitarwa.
Ko da yaƙin gabas ta tsakiya zai shafemu, to bazai shafemu da ƙarfi hakaba.

Idan zamu farka mufarka idan kuma bazamu farkaba tabbas zamu wuce barzahu daga bacci.

Kiristocin Jos 1. Gwamnan Jos Kirista ne2. Mataimakin gwamnan Jos kirista ne3. Kwamishinoni 21 duk kiristoci ne4. Darakt...
02/04/2026

Kiristocin Jos

1. Gwamnan Jos Kirista ne

2. Mataimakin gwamnan Jos kirista ne

3. Kwamishinoni 21 duk kiristoci ne

4. Daraktoci 9 a fadin ma'aikatu duk kiristoci ne

5. Masu ba gwamna shawara na musamman mutum (20) acikinsu duk kiristoci ne

6. Acikin hukumomin tsaro guda (8), kaso 99 na jami'an tsaro duk kiristoci ne

7. Shugabannin dukkan hukumomin tsaro kiristoci ne

8. Addinin da ya fi rinjaye kirista ne

DUK DA HAKA KUKE CEWA MUSULMI SUNA KASHE KU. Bana tsammanin akwai wani mutum mai tunani mai hankali wanda zai yarda da wannan zance naku. Shawarata ga Musulmin Jihar Filato ita ce ina ganin lokaci ya yi da za ku tashi ku yi fafutukar kare haƙƙunankamu. Ku shiga siyasa, ku daina wannan tunanin na cewa, "kun bar musu ofisoshin siyasa domin samun zaman lafiya" ku tsaida ɗan takara mafi kyau wanda zai kare rayukanku, domin daga yadda abubuwa ke tafiya, waɗannan mutanen ba za su taɓa barin ku ku huta ba.

- Sun kashe matafiya, amma an yafe musu.

- Sun kashe kansu kuma har yanzu suna ɗora laifin a kanku, suna neman gwamnatinsu ta gurfanar da ku a gaban hukuma, duk da cewa yawancinsu sun shaida cewa ba a san waɗanda s**a aikata laifin ba. Amma idan aka k**a masu laifin kuma aka samu cewa su Kiristoci ne, sai a rufe zancen.

Me ya sa ba sa faɗin komai game da k**a Rev. Father saboda samar wa 'yan ta'adda mak**ai?📌

Me ya faru da ma'ajin cocin da ya sace fastocinsa tare da abokansa? Aka ce musulmi ne 📌

Me ya faru da faston da ya ɗauki hayar mutane don su kashe mahaifin Gwamna?📌

Me ya faru da masu kisan Janar Alkali Ali? 📌

Me ya faru da masu kisan matafiya 26 na Maulud a 2021? 📌

Me ya faru da masu kisan matafiya kan hanyar su ta zuwa daurin aure daga Zariya a 2024? 📌

Me ya faru da wadanda s**a kashe 'yan kasuwa Musulmi 5 da aka kashe a lokacin azumi a shekarar 2026? 📌

Me ya faru da wadanda s**a kashe Musulmi 5 da aka kashe a wani gidan mai?📌
Allah ka kare yan uwan mu Musulmin Jihar Filato da Najeriya 🇳🇬

Rubutun Umar Abusufyan Yusuf

Idan zamu farka mufarka idan kuma bazamu farkaba tabbas zamu wuce barzahu daga bacci.

Sun barshi ya gudu wannan mutumin shine wanda ake zargin sun aikata ta'addancin a garin jos, wanda s**ayu sanadiyyar mut...
02/04/2026

Sun barshi ya gudu

wannan mutumin shine wanda ake zargin sun aikata ta'addancin a garin jos, wanda s**ayu sanadiyyar mutuwar musulmai da Christa.

ansha ganinsa a bidiyoyi da hotuna lokacin da yake tunzira jama'a da sunan wa'azi. mutane da yawa sun shaida cewa ɗan Amurika ne.

gwamnatin Jos ta shaidawa duniya cewa ta kamma wannan shaiɗanin, saidai kash wasu mutane sun shaida cewa ya gudu yabar kasar. idan hakan ya kasance kenan gwamnatin Jos ƙarya tayiwa al'ummarta.

idan har hakan ta faru tabbas gwamnatin Jos taci amanar kasa, kuma ya cancanci ayiwa gwamnatin Jos tawaye a karon farko. amma kash mutane bazamu iya ba sabo da tsoro ya cika mana zuciya.

kuma abun da zai baku Mamaki har barazana yayiwa shugaban kasa tunubu, amma babu abun da akai. da k**ar mutanen mune s**a soki wani ɗan majalisa, ko wani mai hannu da shuni a gwamnati, da duk inda muke sai an kamomu.

shin mutane wanne mataki zasu ɗauka idan har hakan ta faru?
shin mai Christa zaiyi akan kisan da aka yiwa yan uwansa?
shin mai musulmi zaiyi akan kisan da aka yiwa ƴan uwansu?

wannan faɗa ba iya na musulmi da Christa bane na ƙasane gabaɗaya.

idan zamu farka mufarka idan kuma bazamu farkaba tabbas zamu wuce barzahu daga Bacci.

Tabbas duk malamin da gwamnati ta tsare, akwai wata gaskiya da yake ɗauke da ita basa so mutane su sani:Akwai manya-many...
25/03/2026

Tabbas duk malamin da gwamnati ta tsare, akwai wata gaskiya da yake ɗauke da ita basa so mutane su sani:

Akwai manya-manyan malaman Nigeria da gwamnati ce tayi sana diyyar mutuwa su, kuma kowa ya riga da yasan haka.

idan da zan lissafo malaman da gwamnati ta rusa, da kunsha mamaki duk da mafi yawa daga cikinku sun sansu

Gwamnatin Nigeriya, tana da wani tsari na b@nza wanda bazai taɓa kaisu ga nasaba

idan har malami zai fito duniya yafaɗi aibunta, tabbas zasu san duk yadda zasu domin ganin sun kau da shi.

da za'a ayi binkice akan lamarin malam tabbas akwai abun da ya ƙalu balanci gwamnati da shi.

domin wannan salon da s**a ɗauko tsohon yayi ne mun daɗe da sanin shi.
idan zaku saki malam ku sake shi idan kuma baza kusa ke shi ba wllh babumu babu wannan gwamnatin, tabbas sai mun bawa tunubu mamaki a 2027.

Sadiq sani sadiq ya nuna jarumta A karon farko a kannywood, an samu wanda ya cire tsoro ya cire farga ba ya fito ya faɗi...
25/03/2026

Sadiq sani sadiq ya nuna jarumta

A karon farko a kannywood, an samu wanda ya cire tsoro ya cire farga ba ya fito ya faɗi gaskiya akan gwamnatin tunubu.

yafito yayi kira ga jama'a da su adana katin zaben su waɗan da kuma basu dashi, suje suyi domin ganin anƙifar da a azzalumar gwamnatin tunubu.

ya nuna kishin arewa a filin Allah, yafayyace wariya, da rashin adalcin da akewa yan Arewa

ya nuna yadda tunubu yake kai Legas sama, yanuna yadda yake durƙusar da arewa.

tabbas hakan yaburgeni, ba ma Ni kaɗai ba kaima mai karatu nasan hakan ya burgeka. ba'a taɓa irin wannan ba a tarihin kannywood, mu abun da muka sani akan ƴan kannywood tabbas Mayun wata ne masu ƙarbar shin mafah

mutanene waɗanda s**a yarda da akashemu a basu shinkafah.

saidai kash!! mutane arewa ba'a iya musu dole sai kasamu masu ƙwaƙwalwar dusa
naji wasu suna cewa wai biyan abale akayi, tir da halinku yan Arewa bakwa karfafawa mutum gwaiwa, sai dai ku rusa mai tashi kwarin gwiwar.

tabbas idan muka ci gaba da haka sai an dainaji muryinmu.

innalillahi wa'inna raju'un
25/03/2026

innalillahi wa'inna raju'un

25/03/2026

Tabbas sadiq sani sadiq yayi kori matuƙa wajen ganin yayi videon da wasu s**a kasa.

Address

K. Mazugal
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa mufarka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share