I.H Wadata Global Limited

I.H Wadata Global Limited Assalamu Alaikum. An samar da AM & 4H Channel ne domin ilmantarwa da fadakar da al'umma akan muhimm

JAGORA (H) YA GANA DA MATASAN MU'ASSASATU ABUL FADL ABBAS Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) A yau Asabar 5 ga Sha...
25/01/2026

JAGORA (H) YA GANA DA MATASAN MU'ASSASATU ABUL FADL ABBAS

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

A yau Asabar 5 ga Sha'aban 1447 (24/1/2026) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da Matasan Mu'assasatu Abul Fadl Abbas a daidai lokacin tuna Munasabar haihuwarsa.

Jagora ya fara da taya murnar Mauludin Imam Hussain (AS) wanda ya kasance a ranar 3 ga Sha'aban, da na ƙaninsa Sayyid Abul Fadl Abbas (AS) da ya auku a ranar 4 ga Sha'aban, da kuma na ɗansa kuma magajinsa Imam Zainul Abidin (AS), wanda aka haifa ranar 5 ga watan Sha'aban.

Yace, haihuwarsu a shekaru ne daban-daban, amma duk ya fado ne a watan Sha'aban. "Sha'aban dama wata ne na haihuwar Sahibul Asr waz Zaman (AS), wanda ya zo a tsakiyar watan, sai ya zama kuma haihuwar kakanninsa Imam Husaini da Imam Zainul Abidin, da kuma na Babbansa Abul Fadl Abbas (AS).”

Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi bitan darajoji daban-daban na kowanne daga gwarazan na Karbala, inda ya bayyana Imam Husaini (AS) a matsayin abin koyi, wanda ya sadaukar da kansa saboda addini. Yace, “Tsayuwar (Imam Husaini) ya nuna mana mafita shi ne tsayawa kyam a tafarkin Allah. Su wadanda s**a kashe shi, sun dauka sun gama da addini kenan, ashe ba su sani ba, sun raya addinin ne ta yadda basu tsammani.”

Da yake bayani dangane da Sayyid Abul Fadl Abbas, Jagora ya bayyana cewa, shi duk rayuwarsa yana taimakon Imam Husaini (AS) ne. Inda ya kawo kissar yadda Imam Husaini ya ma babansa Amirulmumin (AS) albishir a lokacin da aka haifi Abul Fadl, wanda a karshe Amirulmumin ya shaida ma Imam Husaini cewa, shi ne mataimakinsa. A nan Jagora ya bayyana yadda Abul Fadl ya taimaki Imam Husaini (AS) har ƙarshen numfashinsa.

Haka kuma Jagora ya bayyana Imam Zainul Abidin a matsayin gwarzon Karbala, wanda duk abinda ya faru akan idonsa ya faru. Yace: "Duk abinda ya faru a Karbala akan idonsa aka yi, kuma aka saka masa sarka aka tafi da shi.”

A karshe, Jagora ya yi tuni akan jarabawa da al'adarta. Yace: “In goguwar bala'i ta zo (jarabawa kenan), wasu su dake, wasu kuka su kasa dakewa. To, jarabawa aka ma wadannan bayin, duk s**a dake, s**a zama mana abin koyi.”

Yace: “Musamman muke cewa, shi Abul Fadl Abbas ba kawai abin koyi ne ga matasa ba, abin koyi ne ga dukkanin al'umma, amma musamman matasa. In ana tuna shi, da gwarzontaka irin ta shi, ya kamata ya zama ramzi ne ga matashi, ta yadda zai ba da ransa ya tsaya ƙyam, ba ko gezau, har izuwa cikawa.”






05/Sha'aban/1447
24/01/2026

Imam Khomeini yace "Idan Makiyanmu s**a kewayemu ta fuskar tattalin arziqi, Mu 'ya 'yan RAMADAN NE, Idan kuma s**a keway...
15/01/2026

Imam Khomeini yace "Idan Makiyanmu s**a kewayemu ta fuskar tattalin arziqi, Mu 'ya 'yan RAMADAN NE, Idan kuma s**a kewayemu ta fuskar Soja, Mu 'ya 'yan ASHURA NE".

15/01/2026

SAYYID QA’EED (H)

Daga jagora (H)

Hotuna: Da yammacin ranar  Laraba 25 ga watan Rajab 1447 (14/1/2026)  Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da j...
15/01/2026

Hotuna:

Da yammacin ranar Laraba 25 ga watan Rajab 1447 (14/1/2026) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabi dangane da shahadar Imam Musal Kazim (AS), a gidansa da ke Abuja.






25/Rajab/1447
14/01/2026

"Shi Imam Musa bai musu laifin komai ba, illa kawai shi mai yawan ibada ne, ya tsaya kyam, kuma zukatan al’umma na tare ...
14/01/2026

"Shi Imam Musa bai musu laifin komai ba, illa kawai shi mai yawan ibada ne, ya tsaya kyam, kuma zukatan al’umma na tare da shi. Kuma wannan ne abin da (azzalumai) basu so, suna son al’umma zukatansu ya zama tare da mahukunta ne, in s**a ga zukatan al’umma na tare da wani, wannan sai ya zama barazana a wajensu, sai su ce an yi gwamnati a cikin gwamnati.”

-Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).

أعظم الله أجورنا وأجوركم بمناسبة ذكرى شهادة إمامنا الإمام موسى بن جعفر الكاظم عليه السلام الخامس والعشرين من رجب






25/Rajab/1447
14/01/2026

JAGORA (H) YA RUFE MU’UTAMAR DIN SHAHIDAI MASU RAIDaga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Da yammacin ranar Lahadi, 22 g...
12/01/2026

JAGORA (H) YA RUFE MU’UTAMAR DIN SHAHIDAI MASU RAI

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yammacin ranar Lahadi, 22 ga watan Rajab 1447 (11/1/2026) ne Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe Mu’utamar din Shahidai Masu Rai na Harka Islamiyyah a gidansa da ke Abuja.

A yayin jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya jawo hankalinsu akan fahimtar sadaukarwa a matsayin muhimmin abu a kokarin raya tafarkin Allah Ta’ala. Yace: “Wannan tafarki na sadaukarwa a tafarkin Allah, wani abu ne zaunanne, wanda yake da shi ne ake samun manya-manyan darajoji.”

Ya bayyana yadda Allah Ta’ala ke gwada sashen bayinSa Muminai da sashen fajirai ma’abota duniya. Yace: “Ana gwada mu da juna ne, aga cewa ko za mu daure.”

Harwayau, Jagora ya yi sharhin aya ta 155 a cikin suratul Baqara, da ke bayanin albishir din Allah Ta’ala akan jarabta Muminai. Yace: “Za mu gwada ku da wani abu na tsoro, da yunwa, da tawayan dukiya, da na rai da jiki ‘anfusi’, da ‘thamarat’”

Yace: “Kamar Shahidai masu rai kenan, wani ya rasa hannu, a rasa ido, a rasa kafa, a rasa kunne, a yi fama da rashin lafiya. Shi ma tawaya ne na ‘Nafs’. Da kuma ‘thamarat’, natijoji, kasuwanci ne mutum yake yi, ko kiwo ne, duk dai ya zama ya samu tawaya a rayuwarsa. To amma wannan ita ce hanyar, don haka aka ce, ka yi ma masu dauriya albishir.”

Jagora yace: “Dama gwaji ne, lamuhalata. An gwada na farko, kuma za a gwada na karshe. Duk lokacin da kace za ka yi addini lamuhalata za a gwada ka. Dole gwaji zai zo.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana takaicinsa akan yadda wasu s**a dauka zaman lafiya tare da azzalumai shi ne addini. Yace: “Mu mun gode ma Allah muna makarantar Imam Husaini (AS). Makarantar Imam Husaini (AS) ta nuna mana cewa sadaukarwa ake yi a tafarkin Allah Ta’ala.”

Ya ba mahalartan kissoshin Shahidai masu rai daban-daban, da darussan dauka daga sadaukarwarsu. Inda yace: “A daure, kuma a dake. Maganin kenan.”

Da yake tsokaci dangane da halin da ake ciki a Jamhuriyar Musulunci a wannan tsakanin, Jagora (H) ya bayyana abin a matsayin shirin makiyan waje. Wanda kuma yace, Alhamdulillah tun yanzu sun fara gane sun yi asara.

Ya kuma yi tsokaci akan halin da muke ciki a wannan kasar na kai hare-hare da sunan ta’addanci, da kuma yadda Trump ya fara kawo hari a Sakkwato da sunan ceton Kiristoci. Yace: “Shin akwai ‘record; din ana kashe Kiristoci ne a Sakkwato? Akwai ma ‘record’ din ana kashe kiristoci a Nijeriya ne ma? Su wadanda ake ce ma ‘yan ta’addan nan, Amerika s**a yi su. Kayansu ne, su s**a assasa su suke ka* she mutane. Kayansu ne, amma kuma wai za su zo su cece ku daga gare su.”

Ya bayyana cewa, abu mafi muni shi ne cewa wai Kiristoci ake kashewa. “Da zai zo yace, zai ceci kasar nan daga ta’addanci. Za mu ce shiri ne, su s**a yi ‘yan ta’addan. Amma wai a’a, wai zai ceci kirista ne daga Musulmi.”

Shaikh Zakzaky ya nuna takaici akan yadda mutane s**a yi tsit da bakinsu akan wannan, amma kuma suna tsoma baki akan Iran.

Yace: “Shi Shaidan ba bari yake ba, za a cigaba ne. Yadda kuka ga ba su kyale Jamhuriyar Musulunci ba duk da cika shekara 47 da samunta a bana … Su ma fa kenan. Ballantana kuma kullum tunanin da suke yi akanmu shi ne, haka fa s**a yi wasa da abinda ya d**o a Iran, don haka (s**an ce) kar ku yi wasa da wadannan. Shi yasa kullum suke nufinmu, suna cewa, (in aka bar mu wai) sai mun kwace kasar.

“Har suna cewa, za mu kwace Abuja. To ai dama kayanmu ne! Shirmensu kawai, wai ba za a yi ‘program’ a nan ba. To sun taba hana wani ‘program’? Sai dai su hana a wani wuri a je a yi a wani wuri ko? To sun ci riban mene? Akwai lokacin kuma da ba zai yiwu ba. Yana nan zuwa kuma. Hanya guda ne, za su bude wuta, illa iyaka.”

Ya bayyana yadda bara wancan aka yi Nisfu Sha’aban a sansanin sojojin sama da ke Abuja, aka gama lafiya lau, amma bara da aka zo yi a wurin, sai ga mota 41 na soja da ‘yan sanda s**a zo s**a yi barazanar bude wuta akan sai an tashi. Yace: “Kullum kishin ruwan za su bude wuta ne, aikin kenan kullum.”

Yace: “Muna fadin wannan ne don a san cewa, ba wai al’amura sun kawo karshe ba ne, za a cigaba ne. Kuma sadaukarwa za a cigaba da yi ne, insha Allahu har izuwa ga nasara.”

A karshe, Jagora ya rife da addu’ar Allah Ta’ala Ya karbi Shahadar Shahidanmu, Ya ba da lafiya ga Shahidai masu rai da marasa lafiya, Ya gaggauta kwato wadanda suke tsare. Ya bamu sabati har izuwa karshen al’amari, da nasara ko muna raye ko bamu raye.






22/Rajab/1447
11/01/2026

Address

Kano Nigerian
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when I.H Wadata Global Limited posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share