AREWA TAMU CE

AREWA TAMU CE Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AREWA TAMU CE, Grocers, Kano.

13/09/2023

ALLAHU AKBAR: Wata mata ta je gurin Annabi Dauda (AS) cikin fushi, ta ce masa: "Ya Annab Allah.Ubangijinka yana da adalci kuwa? Sai ya ce: "Kwarai kuwa, mai adalci ne, ba ya zalunci.

Menene labarin ki? Sai ta ce: "Ni bazawara ce, ba ni da mai taimaka min, ga 'ya'ya mata guda 3 marayu. Ina ciyar da su ne da sana'anar saka da nake yi.

Jiya na yi sakata mai yawa, na daure a wani jan tsumma, zan tafi kasuwa na sayar, na sami abin da zanciyar da kaina da 'ya'yana, sai wani tsuntsu ya zo ya wafce daga hannuna. Kuma ba ni da komai, ga marayu.
Kafin Annabi Dauda (AS) ya ce komai ga wannan mata, sai ga wasu mutane su 10 sun shigo, kowannen su da Dinare 100 a hannunsa, s**a ce:

Ya Annabi Allah! Muna son za mu yi sadaka da wannan kudi... Sai Annabi Dauda (AS) ya ce da su: Me ya faru?" Sai s**a ce "Muna cikin jirgin ruwa, sai iska mai karfi ta taso, jirgin namu ya bule, sai muka dinga ambaton Allah, kuma muka yi bakancen idan Allah Ya tseratar da mu, za mu yi sadaka da Dinare dari-dari. Muna cikin wannan hali, sai wani tsuntsu ya jeho mana wani jan tsumma, a cikin tsumman akwai wata saka Sai muka toshe bular da wannan sakar, Allah Yatseratar da mu.

Sai Annabi Dauda (AS) ya yi godiya ga Allah, ya fuskanci wannan mata ya ce mata: "Ubangijinki mai adalci ne... Idan kin yi sakar nawa k**e siyarwa?" Sai ta ce: "Dirhami daya" Sai ya ce: "Ga Dinare 1000, Allah Ya sayi sakarki, karbi ki je ki ciyar da 'ya'yanki".

Allah Ya warware Mana Matsalolinmu

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA TAMU CE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category