02/04/2026
Masana sunyi nazari kan siyasar Ganduje:
Yan siyasa da dama na ci gaba da bayyana Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dattijo mai dattako da kwarewa a fagen siyasa, musamman wajen tafiyar da al’amura cikin natsuwa da hikima.
Wannan ra’ayi na fitowa ne a daidai lokacin da ake tambayar dalilin da ya sa Ganduje bai fito fili ya zargi Nasiru Yusuf Gawuna da cin amana ba, duk da sauye-sauyen siyasa da s**a faru kwanan nan.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun nuna cewa salon Ganduje ya sha bamban da na Rabiu Musa Kwankwaso, wanda aka san shi da furta ra’ayinsa kai tsaye. A wasu lokuta, Kwankwaso ya taba yin kalamai masu zafi kan Abba Kabir Yusuf, lamarin da ya jawo cece-kuce a siyasar jihar Kano.
Sai dai masana na ganin cewa Ganduje yana amfani da dabarar siyasa mai cike da kwarewa, inda yake kaucewa furta kalamai masu tada husuma, musamman ga wadanda s**a taba aiki tare da shi. Sun kara da cewa irin wannan salo na taimakawa wajen rage rikici da kuma kiyaye martabar siyasa.
Haka kuma, ana ganin cewa shiru ko kaucewa magana kai tsaye wani bangare ne na dabarun shugabanci, domin a wasu lokuta magana na iya kara dagula al’amura.
A ƙarshe, masu lura da al’amuran siyasa sun jaddada cewa kwarewar Ganduje da salon tafiyar da siyasa cikin natsuwa na daga cikin dalilan da ke sa ake kallonsa a matsayin dattijo mai hikima a siyasar Najeriya, musamman a jihar Kano.
REAL SULTAN MEDIA AMBASSADOR