24/08/2025
GASKIYA GOMA SHA BIYAR GA YARON SHAGO. ( Note 🚫 Wannan rubutu ba lallai ba ne komai na sa ya dace da kai, amma za ka iya samun abunda ya dace da kai.)
1- Duk wanda ya ɗauke ka a shagon sa, abunda yake so daga gare ka shi ne; ka kawo cigaba, da kuma inganta kasuwancin sa, domin ya ƙara samun riba, kasa yin haka daga gare ka, neman a sallame ka ne.
2- Shagon Mai Gidan ka, ba na ka ba ne, a kowane lokaci za ka iya barin sa, kuma za a iya sallamar ka, da dalili ko ba dalili, don haka ka nutsu.
3- Ba a zama da Mai Gida da niyyar ya ba ka jari, ko kuma don ya sallame ka wata rana, hakan ba tabbas ba ne, tunanin hakan yana haifar da ha'intar Mai Gida idan bai ma hakan ba.
4- Babbar ribar ka a shago, shi ne; laƙantar kasuwanci, da kuma samun "connections", zama da mutane lafiya, da kuma fahimtar yadda kasuwa ta ke, wannan shi ne mafi girman riba, kuma ita ce mafi ƙarfin jari.
5- Masu sayan kayan mai gidan ka a wajen ku, ba na ka ba ne ba, ka da ka yi yunƙurin mayar da su na ka, akwai matsala, masu sayan ka na wajen Mai Gidan ka, ba na sa ba ne ba, ka da ka mayar da su na sa, akwai kuskure.
6- Tun ranar farko da ka zo kasuwa, ka zo da shiri uku; na farko; yadda za ka inganta kasuwancin mai gidan ka, ta haka ne za ka iya inganta na ka, ranar da ka zama Mai Gidan kan ka. Na biyu yadda za ka bi ka sallami kan ka. Na uku yadda za ka bi wajen samun halattaccen jarin ka. Idan ya sallame ka kusa, alheri ne, idan kuma ka ga an jima, sai ka nemi tafiya da kan ka, sai a rabu cikin mutunci.
7- Kuɗin sallama na shekara, kuɗin haɗa jari ne, ba kuɗin sutura, waya da kayan alatu ba, kuɗin sallamar kullum, kuɗin ajiya ne, fafutukar ka ta gefe, idan ka samu dama, su za ka kashe, idan babu ka raba kuɗin sallamar biyu, ɗaya ka kashe, ɗaya ka ajiye.
8- A yayin zaman shago, ka nisanci duk wani abu da ke nuna kana da kuɗi, misali; waya mai tsada, tufafi akai-akai, abun hawa.... Koda kuwa kuɗin gadon ku ne, lallai akwai matsala.
9- Mai Gidan ka ba zai ma ka aure ba, wannan ba nauyin sa ba ne, kyautatawa ce kawai, mai gidan ka ba zai gina maka gida ba, wannan kyautatawa ce kawai....waɗannan duk akan ka ne, kada ka zama cima zaune. Ka saki jikin ka ka fahimci harka kawai.
10- Ko ta wani hali, kada ka cuci Mai Gidan ka, hakan zai ɗebe maka albarka, kada ka ha'ince shi, hakan zai ba ka matsala, idan ka ji daɗin zama da shi, ka yi ƙoƙarin samun na ka ka tafi, in ba haka ba, wata rana ya'yan sa su gaje ka, su kuma ba lallai ba ne, sun san darajar ka, idan kuma ba ka jin daɗin zama da shi, ka hanzarta barin sa cikin lissafin ka.
11- Ka sani, kyautatawa Mai Gida ba ta hana ya kore ka, munana ma sa ba ya hana ya zauna da kai, komai akwai dalilin sa, amma yin abunda ya dace wannan nauyin ka ne.
12- Matsagaicin shekarun zama a shago, shekara biyar ne, mafi ƙaranta shekara biyu ne, mafi yawa shekara goma ne, amma fa lallai ka sani: Kasuwancin mai gidan ka ba na ka ba ne, ribar sa kuma ba ta ka ba ce, amma shekarun da ka yi a tare da shi, wannan daga rayuwar ka ne, ka taimaki kan ka, Allah zai taimake ka, ka guji abun hannun mutane, sai ka samu damar neman na ka.
13- A zaman shago sai ka yi haƙuri sosai, sai ka yi rayuwa ta cancane, abu ne na lokaci, ka ji a ran ka jami'ar kasuwanci ka ke yi, yadda Ɗan Jami'a ke haƙuri da rayuwa Saboda ya san akwai ranar gama makaranta, haka kai ma za ka yi da rayuwa saboda akwai ranar sallama, ko dai ka sallami kan ka, ko kuma ya sallame ka.
14- Da yawan Masu Gida ba sa lissafi da buƙatun yaron su, don haka wannan na ka ne, Lallai ina gaya maka, ka nemawa kan ka Mafita ta halal. Duk wata buƙatar da Mai Gidan ka yake da ita, kai ma ka na da ita, Bawan Allah idan ba ka yiwa kan ka gata ba, wa kake jira ?.
15- Ka sani, yaron shago, ba wata takarda da kake da ita, ba wani "authority" da ka yi registration da shi, ko ya san da kai, ballantana idan an kore ka haka kawai, ko an sallame ka ba dalili ya bi maka haƙƙin ka. Zaman shago ya fi k**a da zaman shahada, ko dai ka hanzarta ka fahimci abunda kake, kafin a kamo ka, ko ka shantake wata rana katsam a kamo ka, a ranar sai ka gane, ka fa dawo farkon rayuwar ka.
✍️. Bukhari Alhawari