NURA AHMAD

NURA AHMAD Mun bude wannan Shafin domin kawo muku labarai chikin harshan HAUSA da iliman tarwa da Nishadan tarwa B S Y
HAUSA duniya labarai

‎Kamar yadda Muka Saba kawo muku ayau zamuyi bayani dalla dalla anfanin kiwan kunama shin kunsan arziƙin dake cikin kiwa...
31/10/2025

‎Kamar yadda Muka Saba kawo muku ayau zamuyi bayani dalla dalla anfanin kiwan kunama shin kunsan arziƙin dake cikin kiwan kunama wakilimmu dake Australia David na B S Y inda s**a tattauna da wani Mai kiwan kunama mai suna jean ballet inda yace ayanzu a kasuwar duniya ana siyan galan na ruwan Karin kunama akan dala $miliyan 100 kwatan kacin Naira biliyan 150 Amman wakilin B S Y HAUSA ya tanbayeshi ya'aketin kiwan kunama Sai Mai kiwan kunamar yace masa Kafin kacika galan na ruwan Karin kunama Sai katanadi kimanin kunama guda miliyan kacal mun tanbayeshi ana daukar she Kara nawa Kafin s**ai wannan adadin Sai yace zaka iya daukar shekara 10 bayawa inda yace kunama tanada albarkar haihuwa saboda takan yi kwai Sama da 40 daganan Sai yace koyanzu kakawo ruwan Karin kunama za'abaka kudinka take ? To yan Nageriya ga dama tasamu kiwan kunama Wanda mukayimasa lakabi da kiwan yanke talauci?
‎Muna godiya ga mabiyanmu Sai kuyi Following sannan Sai kufadi ra'ayinku
‎Sati Mai zuwa zamuyi muku bayani albarkar dake cikin kiwan muciji
‎Domin Ƙarin bayani:
https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524 👈

Acigaban da wahalar mai da Mali tashiga Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdurahmane Tchiani ya bayar da uma...
30/10/2025

Acigaban da wahalar mai da Mali tashiga Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdurahmane Tchiani ya bayar da umarnin tura tankoki 100 shaƙe da man fetur zuwa Mali domin taimaka wa mahukuntan wannan ƙasar da ke cikin ƙawancensu na AES magance matsalar ƙarancin man da ta ke fuskanta a ƴan kwanakin nan.

Ƙarin bayani: https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524

Dadumi dumi shugaban ƙasar China Xi Jinping ya kammala gana wa da takwaransa na Amurka Donald Trump, a birnin Busan na K...
30/10/2025

Dadumi dumi shugaban ƙasar China Xi Jinping ya kammala gana wa da takwaransa na Amurka Donald Trump, a birnin Busan na Koriya ta kudu, inda s**a yi musanyar ra’ayoyi kan batutuwan da suke jawo rikice-rikicen kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu.

Karin bayani: https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524

Wani babban al'amari Donald Trump Ya Ba Da Umarnin Fara Gwajin Makaman Nukiliya Saboda Barazanar Rasha Da China. Shugaba...
30/10/2025

Wani babban al'amari Donald Trump Ya Ba Da Umarnin Fara Gwajin Makaman Nukiliya Saboda Barazanar Rasha Da China.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar (Pentagon) ta fara sake gwajin makaman nukiliya, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne saboda gasa da ake yi da Rasha da China a fannin makaman kare dangi. Trump ya bayyana hakan ne kafin taronsa da Shugaban China Xi Jinping a Busan, Koriya ta Kudu, inda ya ce “Amurka tana da makaman nukiliya fiye da kowace ƙasa, kuma na sabunta su gaba ɗaya a wa’adina na farko.

Ban so yin hakan ba, amma babu wani zaɓi.” Ya kara da cewa saboda gwaje-gwajen da wasu ƙasashe ke yi, ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta fara gwaji nan take. Amurka ta dakatar da irin waɗannan gwaje-gwaje tun 1992, amma yanzu Trump na neman janye wannan moratorium.

Rahoton SIPRI ya nuna cewa Amurka tana da makaman nukiliya 5,177, Rasha 5,459, yayin da ake hasashen China za ta kai 1,500 nan da 2035. Wannan mataki na Trump ya dawo da tsoron sabon yarjejeniyar makaman nukiliya a duniya.

Majalisar Dattawa ta Najeriya a yau Laraba ta tabbatar da nadin Janar Olufemi Oluyede a matsayin Shugaban Tsaron Ƙasa (C...
29/10/2025

Majalisar Dattawa ta Najeriya a yau Laraba ta tabbatar da nadin Janar Olufemi Oluyede a matsayin Shugaban Tsaron Ƙasa (Chief of Defence Staff - CDS).

Amincewar ta biyo bayan zuwan Oluyede da sauran waɗanda aka ba da sunayensu don tantancewa cikin harabar majalisar ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, inda aka tabbatar da shi bayan awa ɗaya da isowarsu.

Da yake maraba da sabbin hafsoshin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa tantancewar wani muhimmin aiki ne na doka domin tabbatar da cewa an ba wa ƙasar masu cancanta da kishin ƙasa damar kula da tsaron al’umma.

Mai girma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda wadda ke zaman jiran hukuncin kisa bisa samun ...
29/10/2025

Mai girma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda wadda ke zaman jiran hukuncin kisa bisa samun ta da laifin kashe maigidanta.

Wannan na ɗauke a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

A farkon watan Oktoba ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da s**a haɗa da matattu da masu rai.

Bayan kazamin harin Hukumomin lafiya a Gaza sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 63 ciki har da ƙananan Yara, a jerin ha...
29/10/2025

Bayan kazamin harin Hukumomin lafiya a Gaza sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 63 ciki har da ƙananan Yara, a jerin hare-haren da dakarun Isra'ila s**a kai cikin dare, lamarin da ake ganin ya saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla ƙarashin jagorancin Amurka.

Karin bayani: https://www.facebook.com/profile.php?id=100080256788524

Babban kuskure bayan An cire tallafin Man fetur kuma a ci gaba da karɓo bashi -Sarki Sanusi Tsohon Gwamnan Babban Bankin...
29/10/2025

Babban kuskure bayan An cire tallafin Man fetur kuma a ci gaba da karɓo bashi -Sarki Sanusi

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya sake yin kira ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana tambayar dalilin da yasa ake ci gaba da aro, bayan cire tallafin man fetur (subsidy).

Sanusi ya ce cire subsidy da hada kudin Naira da Dala abu ne mai kyau, amma yana da muhimmanci gwamnati ta nuna tsarin gaskiya wajen kashe kudaden da ake samu, domin in ba haka ba, ribar da ake tsammani ba za ta bayyana ba.

A cewarsa:

“Idan ka daina biyan tallafi amma ka ci gaba da aro kuɗi, kamar ka rufe rami ne kuma ka bude wani. Gaskiyar magana ita ce, matsalar tattalin arzikimu tana cikin tsarin kashe kudi, ba wai yadda ake samu ba.”

Sarkin ya kuma tambayi dalilin da yasa gwamnati ke da ministoci 48, da manyan motoci na alfarma, duk da cewa tattalin arzikin kasa yana cikin mawuyacin hali.

Ya ja hankalin gwamnati da ta rage kashe-kashen banza, ta kuma tabbatar da cewa ana amfani da kudaden da aka samu bayan cire subsidy wajen inganta rayuwar talakawa
B S Y HAUSA Duniyar labarai 👈

Firaministan Isra'ila, Netanyahu ya umarci sojojin kasarsa su kai hare-hare masu tsanani a Gaza, bayan ya zargi kungiyar...
28/10/2025

Firaministan Isra'ila, Netanyahu ya umarci sojojin kasarsa su kai hare-hare masu tsanani a Gaza, bayan ya zargi kungiyar Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta jagoranta.
B S Y HAUSA Duniyar labarai

Hamas Ta Mika Gawar Wani Fursuna Yayinda Harin Jirgin Isra’ila Ya Kashe Mutane BiyuKungiyar Hamas ta mika gawar wani fur...
28/10/2025

Hamas Ta Mika Gawar Wani Fursuna Yayinda Harin Jirgin Isra’ila Ya Kashe Mutane Biyu

Kungiyar Hamas ta mika gawar wani fursuna ga ɓangaren Isra’ila a yayin da wani harin jirgin ɗron na Isra’ila ya kashe mutane biyu a Gaza. Rahotanni sun ce an kai harin ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu. Wannan lamari ya ƙara tayar da hankali kan yadda tashin hankalin ke cigaba da ɗaukar rayuka duk da yunƙurin samar da zaman lafiya.

Address

Anuraddeen670@gmail. Com
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NURA AHMAD posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share