15/08/2025
Chapter 01
بسم الله الرحمن الرحيم
_______A zaune nike a kan tabarma cikin baranda isaka na kad'a bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gidan mu Ganyen ta na fad'owa 'kasa gunin burgewa Dambu ne a gabana cikin wata 'yar samira inaci ina sud'e yatsun hannu na saboda dambun yayi min dad'i banason ya'kare
Kawata Ladiyo. Ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da jini koda na d'aga kaina na kalle ta bance mata komai ba Na maida kaina kasa na cigaba da cin dambu na, Saida na cinye dambun tas Sannan na kora da ruwa, Baki na bud'e iya 'karfi na Nayi wata katuwar gyatsa tarashin mutunci, Irin wacce idan yaya Sadee'k ya na guri nayi yake buge min baki.
Kallan Ladiyo nayi Na ta'be baki nace "Ladiyo lafiya kika zo ki ka tsaya min a kai ko aiko akayi?".
Ladiyo. Dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana iya fad'a min na bata kunya tana kuka take fad'a min abinda ya faru.
Tace "Kinsan yaron da jiya muka barar mai da markad'e ai Dazun Umma ta ta aike ni gidan su Zulai anso mata kud'in zubin a dashi,bayan na anso kud'in na had'u da yaron akan hanyata ta dawowa Ni bansani ba a she nan ne layin da yaron yake, shine yayi taimin ruwan duwatsu tako ina har wasu abokan sa s**a taya sa Allah ya temake ni Baban
Ramma Yazo wucewa sai yaga abinda ke faruwa, nan take ya tsawatar musu shine s**a 'kyale ni amma wallahi inaga da sai dai a d'auko gawa ta saboda jifan da s**a min bana wasa bane Ko gida banje ba nayo nan saboda ya bani sa'ko". Yace in fad'a miki "wallahi kema saiya fasa miki goshi".
Nace "Kan uban_nan yanzu dama acikin' kauyen nan a kwai wanda zaija dani har ni zaice zai fasama goshi To wallahi kaf kauyen Dande. Banga mai fasamin goshi ba amma tunda yace haka muzuba ni dashi shege ka fasa kafin ya fasa min ni zan fara zuwa gidan su in fasa na Babar sa inya so kinga yaji dad'in fasa min nawa da hujja".
Inna da fitowar ta kenan da Buta ri'ke a hannun ta da alama daga ban d'aki ta fito Tace "ke da wa siddi'ka. Ki ke yin wa