15/08/2025
Pi Hackathon 2025: Ƙara Amfanin Pi a Sabon Zamanin Open Network
Pi Network ta sanar da kaddamar da Pi Hackathon 2025, shi ne hackathon na farko bayan an buɗe Open Network. Wannan gasa za ta haɗa masu haɓaka manhajoji (developers) don ƙirƙira da kaddamar da manhajojin Pi da za su samar da amfani na gaske ga jama’a ta amfani da Pi, tare da samun damar lashe kyaututtuka har zuwa Pi 160,000.
Dalilin Hackathon ɗin
Bayan buɗewar Open Network, yanzu an sami damar haɗa Pi da ayyuka na waje don ƙara amfani da shi ta hanyar ƙirƙira aikace-aikace masu amfani a rayuwar yau da kullum, musamman ga waɗanda ba su taɓa haƙa Pi ba.
Wannan Hackathon ɗin na 2025 yana ƙarfafa developers su ƙirƙiri kayan aiki, manhajoji da ƙwarewa da za su sauƙaƙa amfani da Pi a duk duniya.
Kalubalen da aka bayar
Ƙirƙiri Pi App da zai ƙara amfani da Pi, ya sa mutane su shiga cikin tsarin tattalin arzikin Pi. Jigon gasar ba shi da ƙuntatawa sosai—domin baiwa kowa damar nuna fasaha da kirkira.
Developers za su iya:
Yin ƙirƙira bisa bukatun masu amfani na gaskiya;
Amfani da Pi Open Source (PiOS) don ginawa da haɗa al’umma;
Amfani da Pi App Studio da Brainstorm App don ƙirƙirar manhajojin nasu;
Yin amfani da fasahar AI wajen gina manhajoji.
Kyaututtuka
🏆 Na 1 – Pi 75,000
🥈 Na 2 – Pi 45,000
🥉 Na 3 – Pi 15,000
🏅 Ƙarin lambar yabo (har zuwa ƙungiyoyi 5): Pi 5,000 kowanne.
Lokutan Muhimmanci
15 ga Agusta: Rajista da haɗa ƙungiyoyi ya fara
21 ga Agusta: Hackathon ya fara aiki
19 ga Satumba: Dubawa a tsakiyar lokaci (Midpoint check-in)
15 ga Oktoba: Ranar ƙarshe na mika aikin ƙarshe
Yadda ake shiga
1. Yi rajista ta Hackathon Registration Form.
2. Yi amfani da Pi App Studio, Developer Portal don gina app ɗinku.
3. Miko:
Demo Video (gajeren bidiyo mai nuna aikin app ɗin ku, bai wuce mintuna 3 ba).
App ɗinku ta hanyar Developer Portal.
Sharuddan Nasara
Aikin ku ya bi ka’idar Mainnet Listing
Ya ƙara amfani da Pi a aikace
Ya kasance mai inganci, mai amfani da kyau (UI/UX)....