09/06/2023
-Ummu Salma Matar Manzon Allah (S) Ta Ruwaito Cewa: Wata Rana Sayyada Fatima Ƴar Manzon Allah (S) Tazo Wajen Babanta Annabi (S) da Wani Akushi Mai Ɗauke da Abinci A Cikinsa, Sai ta Ajiye Akushin A Gaban Manzon Allah (S).
-Sai Manzon Allah (S) Yace Mata: "Amincin Allah Agareki Ya Sanyin Idanuwana! 'Shin Ina Mijinki da Ƴa'ƴanki Biyu Suke?" Sai Ta Ce: "Ya Ma'aikin Allah Suna Gida." Sai Manzon Allah (S) Yace Mata "Ki Ƙira su." Sai Fatima ta Tafi ta Samu Imam Ali (AS) Ta ce Masa: "Manzon Allah (S) Yana Ƙiran ka da Ƴa'ƴanka Biyu".
-Sai Ummu Salma ta Cigaba da Cewa: "Yayin da Manzon Allah (S) Ya Hango Imam Ali da Ƴaƴansa Hasan da Hussain Suna Zuwa Sai Ya Miƙa Hannunsa Mai Albarka Ya Ɗauko Wani Mayafi Dake Wajen Barci, Sai Ya Shimfiɗa shi, Ya Zaunar Dasu A Kansa, Sannan Ya K**a Gefen Mayafin Huɗu da Hannun Damansa Ya Rufe su Dashi, Sannan Ya Ɗaga Hannunsa Na Dama Sama Yana Cewa:
"Ya Allah! Waɗannan Ne Ahlulbaitina, to Ka Kawar Musu da Duk Wata Dauɗa Kuma Ka Tsarkake su Tsarkakewa.
-Sai Ummu Salma Tace: "Sai Nima Na Ɗaga Mayafin Da Nufin Na Shiga Saboda Nima Na Kasance Tare Da su, Sai Annabi (S) Ya Janye Mayafin Daga Hannuna. Sai Nace Ya Manzon Allah (S) "Shin Nima Ina Tare Daku? Sai Yace: "Ke Kina Tare da Wani Akhairi Mai Girma.
-Allahumma Salli Ala Muhammad Waa Ahli Muhammad!!!!
( ﺇﻧَّﻤﺎ ﻳُﺮﻳﺪُ ﺍﻟﻠﻪ ﻟِﻴُﺬْﻫِﺐَ ﻋﻨْﻜُﻢُ ﺍﻟﺮِّﺟْﺲَ ﺃﻫْﻞَ ﺍﻟﺒَﻴْﺖِ ﻭﻳُﻄﻬِّﺮَﻛُﻢْ ﺗَﻄْﻬﻴﺮﺍً )
"...Allah Na Nufin Ya Tafiyar da Ƙazanta Kawai Daga Gare ku, Ya Ku Mutanen Babban Gida, Kuma Ya Tsarkakeku Tsarkakewa".
(Surar Ahzabi,33:33).
-Haƙiƙa Tafsirai da Ruwayoyi Sun Haɗu Akan Cewa Abin da Ake Nufi da Ahlulbaiti Shine Mutanen Gidan Annabi Muhammad (S) Waɗannan Mutanen Kuma Sune:
-Imam Ali (AS).
-Sayyada Fatima.
-Imam Hasan (AS).
-Imam Husaini (AS).
-Domin Ƙarin Bayani A Duba Littafin Durrul Mansur Na Imam As-Suyudi.
-Allah Ka Ƙara Sanya Zukatanmu Yin Baƙa'i da Fana'i Cikin Soyayyar Manzon Allah (S) da Ahlul-Bait (AS).
-Muhammad Jiddah Nguru.
07037009525