28/12/2023
INA MAMAKI SOSAI
Yadda shari'a ta yawaita kira akan kame harshe da kuma illar sakin sa, da yadda kyakkayawan abin kwaikwayon mu Annabin rahma Sallal-Lahu alaihi wa sallam ya zamo mai ƙaranta maganar sa, sai abin ya dinga ba ni mamaki yadda sakin harshe ya zamo ruwan dare a al'ummar mu yanzu, musamman cikin mutunci da alfarmar 'yan uwan mu.
Cikin sauƙi mutum zai yanke hukunci akan abinda bai sani ba, cikin sauƙi mutum zai yi fassarar da ya ga dama, cikin sauƙi mutum zai yiwa al'umma da dama kuɗin goro kan wani lamari da ya faru ga mutum ɗaya ko kuma wani ra'ayi na shi, cikin sauƙi mutum zai yaɗa abinda babu tabbas a kan shi har ma ya dinga tada jijiyar wuya a kai, cikin sauƙi za a hau fashin baƙi akan abinda ba a gama sanin haƙiƙanin sa ba!!!
Lallai Manzon Allah Ya yi gaskiya: "Shin akwai abinda ke kifar da mutane akan fusakun su a wuta sama da abinda harsunan su s**a girba"!!!
Mu ji tsoron Allah 'yan uwa mu kiyaye harsunan mu, kada 'yancin tofa albarkacin baki da daɗin media, da neman abin cewa ya sa mu faɗi abinda zai wafce mana alkhairan mu ranar gobe ƙiyama!
Siyasar Kano❤
12th Jimada Akhir 1445A.H
25th December 2023