Inter mian

Inter mian Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Inter mian, Grocers, nigeria kano, Kano.

16/11/2025

"Ba don Burkina Faso kawai muke yaƙi ba, muna yaƙi don Afirka da mutuncin Baƙar fata" — Traóre

Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya gana da Afrodescendants a ranar Juma'a 7 ga Nuwamba 2025 a Ouagadougou a ƙarƙashin shirin "Bienvenue chez vous" wa'inda s**a sake nuna goyon bayansu gare shi da niyyar zuba jari da zama a ƙasar cikin ɗa'a da mutunci.

Traóre ya bayyana su a matsayin “Jakadu 700 na Burkina Faso”, inda ya sanar musu da cewa an cire sharadin kuɗi wajen samun katin zama na dindindin a ƙasar.

Ya jaddada cewa gwagwarmayar da Burkina Faso ke yi ba don ƙasarsu kaɗai ba ce, illa dai gwagwarmaya wadda ya ayyana a matsayin 'yantar da Baƙar fata gaba ɗaya, da kare mutuncin Afirka da walwalar al’umma.

"Muna yaƙi don Afirka. Muna yaƙi don mutuncin Baƙar fata. Muna yaƙi don jin daɗin al’ummarmu," in ji shi.

15/11/2025
14/11/2025

Hukumar da ke kula da tashoshin jiragen ruwa ta lissafa kayayyakin abinci da jirage 20 s**a shigo da su Najeriya daga kasashen waje - Duba bayanin NPA a sashen sharhi.

Hoto: (X)

14/11/2025

YANZU YANZU: Shugaban ƙasar Burkina faso Ibrahim Traore ya Saka dokar Hana Shan giya ko Sh**ha a Bulkina Faso, inda ya bayyana cewa Shan giya ko Sh**ha Ya Saɓa wa a Addinan Muslunci.

Shugaban ƙasar Burkina faso Ibrahim Traore ya Bayyana cewa Shan giya ko Sh**ha yana Gurɓata Tunanin Matasa Maza da Mata Sannan Hakan ya Saɓa wa Addinin Musulunci.

Shigo Shafin Jaridar 👉 Wakiliya 👈 Ta Nan, Ku Yi Following Yanzu Karku Bari Komai Ya Wuceku...

__________________________________
Shashen Tallace tallace.....

Ko Kun San Cewa Kamfanin Freshdata Sun Karya Farashin Datar MTN 1GB ₦520.

Ga yadda tsarikan nasu yake.
👇🏽

(MTN gifted 1GB ₦520)
(Airtel SME 1GB ₦360)
(9mobile 1GB ₦250)

Ga masu buƙatar referral code.
👇🏽
Freshdata

Website, freshdata.com.ng

Abin farin ciki Datar tana da ƙarfin da har sai ya kai kwana 30 kafin ƙarfinta ya ƙare. Hanzarta kayi download App a nan👇🏽
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.msorgdevelopers.freshdata

Idan kayi download sai kayi register, idan baka iya register ba sai ka tuntuɓi Agent a WhatsApp zasu koya maka yadda za kayi rijista kyauta.

07067488964
07035570974

Ga Link Whatsapp group Freshdata
https://whatsapp.com/channel/0029VaAzQRO9Bb61etDBwG0b

14/11/2025

Bayan gudanar da Sallolin Neman Ruwan Sama wato Salat al-Istisqa a jiya a Masallatan Harami, Masjid Al-Haram da Masjid An-Nabawi, yau rahama ta biyo baya, inda ruwan sama ya sauka a garuruwan Makkah da Madina.

Sallar Istisqa, wacce aka yi a safiyar jiya bisa umarnin Sarkin Saudiyya, ta tara dubban musulmi domin roƙon Allah ya saukar da ruwa saboda matsanancin fari da yankin ke fama da shi. A yau, rahama ta bayyana cikin sautin ruwan sama da ya sauka cikin nutsuwa a harabar masallatan biyu.

Masu ziyara da ma’aikatan masallatan sun bayyana farin cikinsu, suna kallon wannan a matsayin amsar addu’a da kuma alamar albarka ga ƙasar Saudiyya.

Shin a ganinku wannan ruwan sama amsa ce kai tsaye ga addu’ar jiya?

📷/: Source/: Haramain [X]

14/11/2025

Victor Osimhen ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, bayan ya barar da wata kwallo mai kyau tin kafin a tafi karin lokaci na (Extra-time).

Inda daga baya kuma yaci kwallo guda biyu bayan ya bawa 'yan wasan Najeriya hakuri kan damar daya barar a baya.

A yanzu dai Victor Osimhen yaci kwallo guda 31 a cikin wasanni 45 daya bugawa tawagar Super Eagles.

14/11/2025
14/11/2025

JOSÉ MOURINHO YA CE:

“Na taɓa yin aiki da wasu Captain da ba shugabanni ba ne. Amma akwai ɗaya a Porto, Jorge Costa.

Ranar da ba zan taɓa mantawa ba, muna buga wasa da ƙungiyar Belenenses, kuma an doke mu 2-0 a rabin lokaci. Ina tafiya zuwa ɗakin canza kaya, kowa ya ga fushina ya kai kololuwa.

Da zan shige ɗakin sai Jorge Costa ya dakatar da ni, ya ce, ‘Malam, don Allah ka tsaya a waje na minti biyu.’ Ya shiga, ya rufe ƙofa, ya yi dukan abin da zan yi da kaina. Ya yi masifa, ya jefa musu zafi, ya tayar da hankalinsu kamar yadda na saba yi. Bayan ya gama, sai ya buɗe ƙofa ya ce, ‘Yanzu malan, shigo ka koyar da mu.’

Mun koma filin wasa, muka yi abin mamaki — muka ci 3-2. Shi kuwa, Jorge Costa ɗanfan tsakiya ne wanda ba ya cin ƙwallo; amma a wannan rana shi kaɗai ya zura biyu! Wannan shi ne bambanci tsakanin ‘cibiyi’ da ‘shugaba’. Banda cewa kana da bandeji a hannu zai sa ka zama jagora.

Jagoranci ba a siya. Ba a ƙera shi. Idan kana da shi cikin tawagarka, to ka riga ka ɗauki mataki guda gaba.”

Wafiyya Hausa

Address

Nigeria Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Inter mian posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category