01/05/2026
A cikin Diwanin Shehu Rta yace:
وصول جميع الماسكين بحبليا
Saduwar wadanda sukai ruqo da igiyata...
تحققه من لم يكذب بربيا
Duk wanda baya qaryata lamarin Ubangiji na ya tabbatar da wannan.
وجوبي فياف غي المعارف لم ترم
Yankewata dazuzzuka acikin sanin Allah , ba'a taba neman ta ba.
فقد قصر الاقطاب عن درك شءويا
Haqiqa Manyan Quɗubai sun taqaita ga barin riskar fagena.
بفضل اله الناس جل جلاله
(Na samu wannan ne) da Falalar Ubangijin mutane wanda girman sa ya ɗaukaka.
وحب رسول الله طه نبيىءيا
(Kuma na samu wannan ne) sabida soyayyata ga Manzon Allah mai suna Ɗaha, Annabi na. SAW.
حلفت يمينا اننى لايحبني
Na rantse, rantsuwa gwagwgwaba, ni ɗinnan, babu mai sona...
سوى اسعد والاكس في حال بغضيا
Sai mafi Arziqi, wanda kuma yafi kowa rashin Arziqi, yana cikin halin qiyayyana.
وقد علم الاقوام اني خديمه
Dukkan Mazaje (na Allah) sun san ni Khadimin (Annabi SAW) ne,
فوصل حبيب الله يلفى بوصليا
Saduwa da Masoyin Allah (SAW) ayau, ana samun ta ne da saduwa dani.
وما قلت قولي شاطحا متبجحا
Ban faɗi zancena ba, ina me kirari kokuma mai alfahari ba.
وما مسني سكر يغيب عقليا
Kuma maye bai shafeni ba, da zai bugar da hankali na ba.
وان خطوطي لاانام سعادة
Kuma Rubuce rubuce na arziqi ne ga halitta.
فلم يشق يوما من راني وخطيا
Duk wanda ya ganni, ko kuma yaga rubutu na, bazaiyi rashin arziqi ba koda rana ɗaya.
وما قلت هذا دون اذن وانني
Ban faɗi wannan maganar ba, ba tare da Izina ba, duk dayake ni...
لاكتم سرا لا يباح لغيريا
Ina boye sirri, wanda baya halatta a budeshi ga wani na.
وذا كله من حب سيد مرسل
(Na samu) wannan dukkansa saboda So na ga shugaban Manzanni SAW.
عليه صلاة الله ولتعل شءنيا
Salatin Allah ya tabbata gareshi, Allah ka ɗaukaka sha'ani na.
Allah ya qara ma Shehu Karama ya bamu albarkacin sa.
Barka da JUMU'A masoya BARHAMU