Aliyu Aliyu

Aliyu Aliyu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Aliyu Aliyu, Grocers, Alikazaure Street, Jos.

TARIHIN SHEHUNNAN TIJJANIYYA.:KASHI NA 02.:TAKAITACCEN TARIHIN SHEIKH MUHAMMAD SALGA (RTA).:Nasabarsa Ta Wajen Uba:Sheik...
13/09/2023

TARIHIN SHEHUNNAN TIJJANIYYA.
:
KASHI NA 02.
:
TAKAITACCEN TARIHIN SHEIKH MUHAMMAD SALGA (RTA).
:
Nasabarsa Ta Wajen Uba:
Sheikh Muhammad Salga Dan Alhaji Umar Dan Muhammad Jali Dan Malam Sai'idu Dan Malam Abubakar Kukawa Qasar Borno.
:
Nasabarsa Ta Wajen Uwa:
Sheikh Muhammad Salga Dan Sayyada Fadimatu Yar Malam Jibrilu Dan Malam Muhammad Wanda Akafi Sani Da Wali Dan Masanin Katsina.
:
Shekarar Da Aka Haife Shi:
An Haifeshi 1282Hj/1863M.D
Mahaifarsa: An Haifeshi A Garin Salga Ta Qasar Ghana Lokacin Da Mahaifinsa Ya Tafi Wajen Fatauci.
:
Malamansa:
Malam Abubakar Kashnawy Kaka Na Sheikh Malam Atiku Da Malam Halilu Na Malam Auta Da Malam Abdurrahman Suyudi Babban Malami Na Madabo Da Sheikh Abdussalam Azzanati Atturabulusi Dss.
:
FANNONIN DA YA KARANTA DA MALUMAN DA YAYI KARATU A WAJENSU:
Fannonin Da Ya Karanta Dai Na Fiqhu, Ya Karanta Wajen Malam Suyudi Na Madabo Da Malam Salihu Dansa da Malam Hassan Tagwai, Malam Ya Karanci Fannin Lugga Wajen Malam Umaru Wali Zaria, Fannin Hadisi Da Musdalahunsa A Wajen Sheikh Abdussalam Zanati, Sai Fannin Sufantaka (Tasauwuf) A Wajen Malamai K**ar Su Sharif Ujudud Da Sheikh Muhammadul Alami.
:
MAKARANTARSA DA YADDA TAKE KOYARWA:
Lokacin Da Malamansa Sukayi Masa Izini Ya Soma Karantarwa, Sai Ya Soma A Gidansa Da Yake Unguwar Magoga Cikin Birnin Kano, Dalibansa Suna Fara Zuwa Makaranta Tun Daga Sallar Asuba Bayan An Gama Wazifa Har Zuwa Azahar, Saboda Haka Dalubai Suke Musabaqa, Dan Duk Wanda Ya Fara Zuwa Shi Zai Fara Biya Karatu, Sannan Mai Bi Masa, Don Haka Dalubai Suke Gaggawar Aje Litattafansu A Makarantar Tun Da Asuba, Don Mutum Ya Zama Shine Na Farkon Wanda Za'a Biyawa Karatu.
:
Zamu Tsaya Anan Sai In Allah Ya Kaimu Wani Lokacin, Allah Ya Bamu Albarkar Su Shehi Ya Kuma Ilmantar Da Mu Da Abin Da Su Karanta, Alfamar Annabi Muhammad (Saww)
:
®️ Muhammad Sani Al-Richifawy

ABINDA SHEHUN MU AHMAD TIJJANI RADIYALLAHU ANHU YA KOYA MANA...-Mafi muhimmancin Alkawarin da zamu dauka uku ne1 Mu dauk...
28/08/2023

ABINDA SHEHUN MU AHMAD TIJJANI RADIYALLAHU ANHU YA KOYA MANA...

-Mafi muhimmancin Alkawarin da zamu dauka uku ne

1 Mu dauki Istigifari
2 Mu dauki Salati
3 Mu dauki kiran Allah( Zikiri)

-Mafi Muhimmancin shagala
1 Shagala a soyayyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
2 Shagala da ganin kyawawan aiyuka maimakon yawan ganin aibu

Mafi Muhimmancin zamantakewa
1 Zaman lafiya da kowa da komai
2 Samar da uziri ga kowa a matakin farko
3 Tambayar abinda baka fahimta ba

Mafi muhimmancin aiki shine tsarkake zuciyar kai daga munanan abubuwa kafin fita tsarkake zuciyar wani

Mafi muhimmancin biyayya ita ce kaskantar da kai ga duk wata ni'imar Allah

Ina taya 'yan uwana Yan Darikar Tijjaniya Murnar zagayowar watan Haihuwan wanda Ya koya mana Lazimtar wadannan dabi'u wato Shehun mu Abul Abbas Ahmad Attijany.

Source: ALIYU ALIYU ❤🖊🖊

TUSAMMA "AIBATAL FUQARA" .1. Fa na fara da BismillahiIn zo in biya da HamdillahSalati ma'a SalamillahBisa Ɗaha Rasulilla...
28/08/2023

TUSAMMA "AIBATAL FUQARA" .

1. Fa na fara da Bismillahi
In zo in biya da Hamdillah
Salati ma'a Salamillah
Bisa Ɗaha Rasulillahi
Abin zaɓi na Rahmaniy.

2. Da Alai har Sahabbansa
Kaza Zuriya da matansa
Da masu biyar Adininsa
Da dukkan masu begensa
Da dukkan masu Imani.

3. Ina roƙonka ya Rabbiy
Mu'iniyna aya Hasbiy
Kasa haske cikin Ƙalbiy
Kaban Ikon yabon Ƙuɗbiy
Mumidduhun kauni Tijjani.

4. Ala Ya Sahibal Fasi
A mai Ƙadamai ala Ra'asi
Ala ya Shaikhu Nibrasi
Ka dubo zuciyar ƙasi
Ta haskaka du da Nurani.

5. Kaban madadinka ya ƙuɗbu
Aya Shaikhiy kayo Jazbu
Ga zatina a ya Hibbu
Kasani inzo cikin Sahabu
Waɗanda ka binka Tijjani

6. A domin Rabbu ya baka
Yawan Fadhala ya keɓeka
Da Khatmul Auwaliya'u duka
Fa ba Khatmi a bayanka
Da zai cika Ahli Irfani.

7. Fa kaine Khatmu ba Shakka
Ashe kuma talikai dukka
Fa babu fa wanda yasan ka
Fa sai Mukhtaru kakanka
Habibullahi Adnani

8. Karamominka na da yawa
Fa basu ƙidayuwa a yawa
Fa bani iya su ni niwa
Fa domin naji kam da yawa
Sukan ɗimauta yaƙzani.

9. Da wanda ya gaakac ran jumu'a
Da ran Ithnaini naji ma'a
Masau ya tsare dukkan sa'a
Ya samu shiga cikin jama'a
Su je Jannatu Ridhwani.

10. Salatul Fathi an baka
Da Jauharatul K**ali duka
Kaza Asma'ul Maulaka
Rasulullahi ya baka
Ina ya k**arka Tijjani.

11. Yana a cikin karamunka
Aya Shaikhinmu an baka
Ka cece mutun zamaninka
Gare su Hisabi babu duka
Su je Jannati Rahmani.

12. Fa Ƙarnu guda fa an baka
Tamanin Shekarurunka
Da Ɗay Ishriyna a bayanka
A Sheikhiy nayi roƙonka
Ka sani cikin su Ikhwani.

13. Kazalika munji anyi faɗi
Gareka a Sheikhu Faltu'uɗi
K**a li Bilali an ka faɗi
K**ar kuma yadda anka fazi
Ga mai Mulki Sulaimani.

14. Kazalika Auwaliya'u duka
Ka kaine shugabansu duka
Su sha madadinka naji duka
Gurinka su zam a bayanka
Wa Hattal Ƙuɗbu Kailani.

15. Faɗar Ƙadamaya hatani
Fa illa Anta Tijjani
Abin fa nufa ga Milani
Mutanen nasa zamani
Fa kai kuwa kulla zamani

16. A don

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA😭   "Idan duniya tazo Qarshe za'ayi wani dare mai tsawo wanda saboda tsananin duhunsa tsoro zai k...
27/08/2023

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA😭

"Idan duniya tazo Qarshe za'ayi wani dare mai tsawo wanda saboda tsananin duhunsa tsoro zai k**a mutane sai su fita zuwa Masallatai suna ta addu'a suna rokon afuwa awajen Allah..
Chan za suga alamar ketowar alfijir, rana zata fito amma ta mafa'darta (wato ta yamma).
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!.
Wannan chanjin yanayin da aka samu shine babbar alamar dake bambanta tsakanin Qarewar rayuwar duniya da kuma ainahin tsayuwar nan ta tashin Alqiyamah.
Da zarar rana ta fito daga mafa'darta (wato yamma) nan take za'a ji kira daga wata murya mai Qarfi..
Tana sabar da mutane cewa "AN RUFE QOFAR TUBA!". Daga lokcin nedukkan wata sha'awa zata fiche daga dukkan zukata, Kuma nadama zata yawaita..
Domin kuwa tuba ba zatayi amfani ga masu yinta ba.. Imani ba zai yi amfani ba, sai ga wadanda suke dashi tuntuni..
Abubuwan dake rike da duniyar dama su hudu ne : - ALQUR'ANI. - KA'ABAH. - MUSULUNCI. - MUMINAI. -
Za'a wayi gari aga Alqur'anai baki daya sun zama farar takarda babu rubutu ko daya.. -
Wani Babban Kafiri zai zo ya rushe Ka'abah (ZUS SAWEEQATAINI) Kuma zai wawashe kayan alatun dake cikinta.. (SUBHANALLAH).
Haka Annabi (saww) ya fa'di sunansa. - Za'a yi wata iska mai dadi wacce zata zama dalilin ficewar rayukan dukkan Muminai..
Su koma zuwa ga rahamar Ubangijinsu. - Za'a wayi gari babu sauran Musulmi ko Muminai aduniya baki daya.
Babu sauran mai cewa "ALLAH! ALLAH!!". - Za'a yi Qarni guda (100 yrs) wanda acikinta babu sauran 'dan halal.. Duk sai Mazinata da 'Ya'yan Zina. Zasu rika yin zina akan layi da bakin tituna.. . Cikinsu babu wanda yasan Allah b***e ya bauta masa.
Sune mafiya sharrin halittu abayan Qasa. Kuma akansu ne Alqiyamah zata tashi.. HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL!!
Ya Allah ka kyautata Qarshenmu kasa mu cika da imani Ameen.

Kai jama ar kasan nan hhhh 🙄🤔🤔1- Hoto na farko kafin ta fara kallon AREWA 24 cikin shirin mata a yau.2- Hoto ba biyu bay...
27/08/2023

Kai jama ar kasan nan hhhh 🙄🤔🤔1- Hoto na farko kafin ta fara kallon AREWA 24 cikin shirin mata a yau.

2- Hoto ba biyu bayan ta fara kallon AREWA 24 kuma shirin mata a yau ,.�Ta gano wasu haƙoƙinta zata amsa.🤔🤔🤔🤔🤔

Address

Alikazaure Street
Jos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aliyu Aliyu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category