17/12/2025
Wani dattijo yana zaune a bakin wani kogi. Kwatsam sai ya hango wata kunama ta faɗa cikin ruwa, kunamar ta rikice tana ta ƙoƙarin ceton kanta daga nutsewa. Sai dattijon ya yanke shawarar ceto ta; ya miƙa hannunsa don ya fito da ita, amma sai kunamar ta cije shi.
Nan take sai ya janye hannunsa yana ihu saboda tsananin zafi. Amma bai wuce minti ɗaya ba, sai ya sake miƙa hannunsa domin ya ceto ta.
Kunamar ta sake cizon shi a karo na biyu. Ya sake janye hannunsa yana ihu saboda zafi. Bayan wani ɗan lokaci kaɗan, sai ya sake yin ƙoƙarin ceton ta a karo na uku.
A kusa da shi, akwai wani mutum wanda yake zaune yana kallon duk abin da ke faruwa. Sai ya ce:
Malam, shin ba ka ɗauki darasi daga abinda ya faru a karo na farko, ko na biyu ba, ga shi kuma kana ƙoƙarin ceton ta a karo na uku?
Dattijon bai ko kula shi ba, ya ci gaba da ƙoƙari har sai da ya yi nasarar ceto kunamar. Sannan ya tafi wurin mutumin, ya dafa kafadarsa a hankali, ya ce:
Ya kai ɗana, dabi’ar kunama ce cizo, ni kuma dabi’ata ita ce nuna ƙauna da tausayi. Don me kake so in bar dabi’ar kunama ta rinjaye tawa? Ka yi mu’amala da mutane bisa ga halinka, ba wai bisa ga halinsu ba, koma su wane, kuma komai yawan abubuwan da suke yi da za su iya cutar da kai. Kuma kada ka saurari muryoyin da ke neman su rabaka da kyawawan halayenka kawai saboda ɗayan ɓangaren bai cancanci ya samu kyautatawa daga wajenka ba.