Abdul Azeez lawal

Abdul Azeez  lawal Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abdul Azeez lawal, Gada biyu gusau zamfara. . state, Gusau.

03/01/2026

*Aure Yayi Alaji Kana Kwance Za'a Zo A Durkusa Ace Honey Me Za'a Dafa Maka Sai Kadan Murtuke Fuska Ka Juyo Kace Jollof 🤷‍♂️😂🥴*

03/01/2026

Ladubban Hira da Mutane

1- Ka guji ƙarya, da gulma, da yi da mutane, da yi musu tonon silili.

2- Yawaita amfani da kalmomin kyautata zance: "Don Allah", "in ba damuwa", "na gode", "madalla!"

3- Kada ka shagaltar da abokan hirarka da yawan faɗa musu matsalolinka. Ka zama mai yakana.

4- Kada ka riƙa tambayar abokin hirarka keɓantattun abubuwa da s**a shafi rayuwarsa.

5- Idan wani yana ba da labarin da ka sani, kada ka katse hanzarinsa, bari ya kai gaci, kana mai nuna labarin ya shige ka.

6- Kada ka wawantar da ra'ayin wasu, ka wulakanta su.

7- Kada ka nuna ra'ayinka shi ne ƙololuwar gaskiya. Ka riƙa cewa: A ganina.

8- Ka riƙa rarraba dubanka ga waɗanda kake zantarwa, kada ka sa mutum ɗaya a gaba kana yi masa kallon ƙurilla.

9- Ka guji gamammen hukunci a kan mutane, kamar ka ce "Duk mutane sun lalace.."

10- Kada ka ce wa mai zance: "ƙarya kake" haka gatsal. Ka koyi cewa: Ni kuma na ji an ce kaza ne ya faru.

* Umar bn Khattab (RA) ya ce: "Idan aka wurgo kalmar da za ta ɓata maka rai, ka sunkuya ta wuce ta samanka."

* An tambayi Abbasu ɗan AbdulMuɗɗalibi (RA): Da kai da Manzon Allah (SAW) wane ne babba?
Ya ce: "Shi ne babba, amma an haife ni kafin haihuwarsa."

* Aɗa'u ɗan Abu Rabahi ya ce: Mutum yakan zantar da ni wani labari, sai in nutsu, ina sauraronsa, duk da tun kafin a haife shi, na san wannan labarin da yake gaya mini."

* Ma'amunu ya tambayi sunan wani mutum da ake kira: Sayyid ɗan Anas, ya ce: "Kai ne Sayyid?"
Mutumin ya ce: "A'a, Sarkin muminai shi ne sayyid (shugaba), ni ɗan Anas nake."

03/01/2026

Alhmdllh

24/10/2025

A duniya kanada ido 👀 a lahira kuma zaka tashi makaho, idan baka ambaton Allah domin Allah yana cewa

( وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى 124 ) [طه: 124]

*(Duk wanda ya kau da kai ga barin ambaton Allah mai rahama, to yana da rayuwa mai qunci, kuma za mu tashe shi ranar alqiyama a makaho).*

24/10/2025

*Hawaye na magana da zuciya idan harshe ya kasa*

*A wasu lokuta babu kalmar da zata iya bayyana zafin da zuciya keji Sai hawaye su zamo masu fassara abin da ke cikin rai Amma abin takaici shine Wasu suna amfani da harshensu wajen yin karya sauran kuma suna amfani da hawaye wajen yaudara Ka zama mai gaskiya ko da hawaye ne ke zuba...*

24/10/2025

*Kana yin haƙuri ko? To, ka kwantar da hankalinka, lada ma ba da daɗewa ba zaizo In shaa Allah..❤️*

Address

Gada Biyu Gusau Zamfara. . State
Gusau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdul Azeez lawal posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share