13/01/2025
Ɓangaren Hadisi:
1. Arba'una
2. Majmu'ul bahraini
3. Riyadus salihin( ko da ba duka ba)
4. Umdatul Ahkam( shima ko da ba'a kammala ba).
Fiƙihu kuma
1. Qawa'idi
2. Ahlari
3. Ishmawy
4. Iziyya
Tajwidi kuma:
1. Kitabuttajweed
2. Hidayatul Mustafida
Tauhidi kuma:
1. Muqarrara
2. Al-Usul Al-thalatha
3. Usuluddinin
4. Kitabuttauheed
Sira kuma:
1. Khulasa (1)
2. Khulasa (2)
3. Khulasa (3)
Arabiyua da kuma sauran fannoni zakaga bakin gwargwado ya iya wani ɓangare a ciki, wanda koda bakace masa malami ba amma bazakace masa jahili ba a addini, Alhamdulillah .
Amma a yanzu zaka samu sau dayawa sanda za'ace yaro yayi sauka a wasu makarantun sai kaga abin mamaki bai iya littafi ko ɗaya cikakke ba a kowane ɓangare da muka ambata, kai Alƙur'anin ma bai iya ba akamr ya da muka ambata.
Ba nan matsalar take ba, kasan meye matsalar? Zo kaji🧏
Ana yin saukar ne yanzu saboda yaro yace a saka shi, ba wai saboda ya ca canta ba, kwarai kuwa, ba dai zai kawo 10k ba ko 20k🙄 ai an gama, ba dai zai kawo free rice ba😌 ai hikenan, ba dai zatayi donut da divlan na ustazai ba😅 ai babu matsala. ( hakane, eh hakane , hakane).
Wata yarinyar ma zakaga tun yan ajin su suna izu 20 akayi mata Aure, amma idan Auren ta ya tashi, sai kaga tazo tace itama a saka ta a cikin yan sauka, sai ta biya 10k ɗin ta shikuma headmaster ya rattaba sunan ta😭
Ba wannan ne babbar matsalar ba, abinda nake kallo na matsala abubuwa ne manya-manya guda biyu:
1. Su wayannan ɗaliban da akace sunyi sauka, har aka basu shaida (Certificate ) wannan fa shaida ce, wacce annabi SAW ya sanya ta cikin manya manyan zunubai, idan anyi hakan a boko kuma sai ayi hakan a islamiyya , kuma kuyi tsammanin kuga dakyau. Ku murje ido addini ba wasa ba, wanda ya iya a tabbatar masa da iyawarsa wanda bai iya ba ya dage ya koya. Sannan duk inda ɗalibi yaje akace ina kayi karatu ya faɗin sunan makarantar ku sannan aka tabbatar da bai iya ba, kune abin zargi kune abin zagi, domin sau dayawa zakaji basu iya ba, ba wai kuskure nake m