15/12/2022
DARUSA MASU ZURFI CKN AYOYIN QUR'ANI
A Suratul Yusuf(A.s), Yayi Mafarkin Taurari 11 da Rana da wata duk sun Faɗi a gareshi suna Girmamashi(Wanda hkn alamace ta Ɗaukaka), Amma Sai Mahaifinsa ya bashi umarnin karya Labarta hakan Ga Ya'n Uwansa.
لا تقصص رؤياك على إخوتك
Anan na Ɗauki Darasi, Ya'n Uwanka Sune Farkon Mahassadanka, Bari nai misali da nan media, zaka Samu wani inyai Posting Yana samun sama da (100 likes👍), Amma da zaka duba ckn mutum ɗarin nan Dakyar kaga Ya'n Uwansa 3, kuma bawai Dan Basa Online bane, A'a suna nan suna gani, Koda hotonsa ya Ɗora Saidai na nesa S**e masa "Masha Allah" in Wa'azi yaje ko Faɗakarwa Bazaka Taɓa gani sun yaba masa ba, munafukan nan ko kuskure sukaga kayi Direct Wajen iyaye zasu kai ƙararka Suyi ƙarin gishiri da magi, Har Kaji Mama ko baba na cewa "Ashe abunda kk a Facebook kenan?..." 🥺
Darasi na Gaba, Makusantan Annabi Yusuf Ya'n Uwansa na Jini sukace
اقتلوا يوسف
"(Mu) Kashe Yusuf"💔🥺
Sai Gashi Wani Bare( na nesa da bai Sanshi ba) yace
أكرمي مثواه
"(wa matarsa) ki Karrama Masaukinsa"🥰
Darasin Dana Ɗauka, SOYAYYA arziki ce, Bakasan A Zuciyar wa Arzikinka yake ba.
Darasi na Gaba, Taruwarsu harsu 11 wajen ganin sun Cutar da ƙaramin yaron da sun fishi komai a lokacin😢, hakan ya Ƙara fito mun da hatsarin Hassada da yadda take sa Maiyinta Aikin rashin hankali da Basira duk girmansa da iliminsa.
A ƙarshe na Ƙara Girmama SHA'ANIN Allah, Da ya sanya Hanun data Jefa Annabi Yusuf a Rijiya, Ita wannan hannun ne ta Dawo gareshi ƙasƙantacciya tana masa Maula da Roƙon neman Taimako.
قَالُوا تَاللَّهِ لَقَدْ آثَرَكَ اللَّهُ عَلَيْنَا وَإِنْ كُنَّا لَخَاطِئِينَ
Darasin Dana Ɗauka
القوي لا يبقى قويا، والضعيف لا يبقى ضعيفا
Mai Ƙarfi Baya Tabbata da karfinsa har Abada, Haka Marar Ƙarfi baya Tabbata da Rashin Ƙarfi har abada, Al'amarin na Allah ne Yau da Gobe kuwa ta Wuce Wasa. Dan haka ka Kiyayi karkanci ko wulaƙanci na wani dan kanaga ka fishi yau, mai yuwuwa gobe kai zaka taho gareshi kana mai Roƙo.
Na Barku Lafiya.