Labari Daga Darazo

Labari Daga Darazo Daga Darazo Zuwa Duniya (📽️ Darazo Online News)

DAGA DARAZO: Daliban Fudiyya Darazo Sun Nuna Alhininsu Kan Ƙananan Daliban Makaranta da S**a Rasa Rayukansu Sakamakon Ha...
24/06/2026

DAGA DARAZO: Daliban Fudiyya Darazo Sun Nuna Alhininsu Kan Ƙananan Daliban Makaranta da S**a Rasa Rayukansu Sakamakon Harin Amurka a Iran, Yayin Zaman Makokin Shahadar Imam Hussain da ake Gudanarwa a Garin Darazo.

KUNGIYAR DYNA TA CIKA SHEKARA ƊAYA DA KAFUWAƘungiyar Darazo Youth Nexus Alliance (DYNA) ta yi bikin cika shekara ɗaya da...
24/06/2026

KUNGIYAR DYNA TA CIKA SHEKARA ƊAYA DA KAFUWA

Ƙungiyar Darazo Youth Nexus Alliance (DYNA) ta yi bikin cika shekara ɗaya da kafuwa, inda ta bayyana wannan lokaci a matsayin shekara ta nasarori, haɗin kai da samar da damarmaki ga matasan Darazo.

A saƙon bikin, ƙungiyar ta gode wa Allah Maɗaukakin Sarki, tare da yaba wa mambobinta, abokan hulɗa da masu goyon baya bisa gudunmawar da s**a bayar wajen cimma nasarorin da aka samu.

DYNA ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da tallafa wa matasa da haɗa su da damarmakin ci gaba domin gina kyakkyawar makoma.

Manufa Ɗaya • Hangen Nesa Ɗaya • Tasiri Mara Iyaka.

DIRKASHI: Bayan s**a da dama daga magoya baya, Cristiano Ronaldo (CR7) ya ci ƙwallaye biyu a gasar Kofin Duniya.Ronaldo ...
23/06/2026

DIRKASHI: Bayan s**a da dama daga magoya baya, Cristiano Ronaldo (CR7) ya ci ƙwallaye biyu a gasar Kofin Duniya.

Ronaldo ya buɗe Asusunsa a gasar Kofin Duniya ta 2026, Portugal ta doke Uzbekistan 3-0

YADDA DUBBAN MUTANE S**A HALARCI JANA'IZAR SHUGABAN IZALA NA JIHAR BAUCHIDubban al’umma ne s**a halarci jana’izar Shugab...
23/06/2026

YADDA DUBBAN MUTANE S**A HALARCI JANA'IZAR SHUGABAN IZALA NA JIHAR BAUCHI

Dubban al’umma ne s**a halarci jana’izar Shugaban Gudanarwa na Izala a Jihar Bauchi, Alhaji Bappah Aliyu Azare, wanda Allah Ya yi wa rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi, lamarin da ya jefa iyalansa, abokansa da daukacin al’ummar Jihar Bauchi cikin jimami

📹 Serbia 15 TV

DA ƊUMI-ƊUMI: Sheikh Sani Khalifa Zaria ya sake gurfana a Babbar Kotun Tarayya Ana tuhumar Malamin ne da hannu wajen yun...
23/06/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Sheikh Sani Khalifa Zaria ya sake gurfana a Babbar Kotun Tarayya

Ana tuhumar Malamin ne da hannu wajen yunkurin juyin mulki, zargin da hukumar DSS ta gabatar a kansa da wasu a watannin baya.

HUTUNA: Yadda Aka Kawata Kabarin Sheikh Dahiru Usman BauchiAllah Ya gafarta masa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama mako...
23/06/2026

HUTUNA: Yadda Aka Kawata Kabarin Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Ameen.

DIRKASHI: Tawagar Magoya Bayan Ƙungiyoyin Kwallon Ƙafa na Real Madrid da Barcelona a DarazoYaya Kuke Hasashen Wasan Zai ...
23/06/2026

DIRKASHI: Tawagar Magoya Bayan Ƙungiyoyin Kwallon Ƙafa na Real Madrid da Barcelona a Darazo

Yaya Kuke Hasashen Wasan Zai Kaya?

DAGA DARAZO: "Duk Tsananin Musibar Karbala Bai Sa Sayyidah Zainab, 'Yar Imam Ali (As), Ta Bar Hijabinta Ba" — Cewar Mala...
23/06/2026

DAGA DARAZO: "Duk Tsananin Musibar Karbala Bai Sa Sayyidah Zainab, 'Yar Imam Ali (As), Ta Bar Hijabinta Ba" — Cewar Malama Ummulkair yayin zaman makokin Ashura a Darazo.

A ranar Litinin, 22 ga Yuni, 2026, an ci gaba da gudanar da zaman juyayin shahadar Imam Hussain (AS) a garin Darazo, Jihar Bauchi.

A yayin jawabinta, Malama Ummulkair ta yi kira ga mata da su ba hijabi muhimmancin da ya dace, tana mai cewa Sayyidah Zainab (AS) ta kasance abin koyi wajen tsayawa kan koyarwar addini duk da tsananin musibar da ta fuskanta a Karbala.

Har ila yau, ta nuna damuwa kan yadda wasu mata ke sakaci da hijabi a wannan zamani, tare da ƙarfafa su da su yi koyi da ɗabi'a da jajircewar Sayyidah Zainab (S.A).

Zafafan hotunan Jami'an kula da daji wanda gwamnatin jihar Bauchi ta ƙaddamar a radar  asabar a garin Bauchi.📸 Al-ihsan ...
23/06/2026

Zafafan hotunan Jami'an kula da daji wanda gwamnatin jihar Bauchi ta ƙaddamar a radar asabar a garin Bauchi.

📸 Al-ihsan Photography

HOTUNA: Jaruman Kannywood ƙarƙashin jagorancin, Dauda Kahutu Rarara sun gudanar da saukar karatu na musamman domin neman...
23/06/2026

HOTUNA: Jaruman Kannywood ƙarƙashin jagorancin, Dauda Kahutu Rarara sun gudanar da saukar karatu na musamman domin neman zaman lafiya da haɗin kai a faɗin ƙasar nan.

Mi za ku ce?

Address

Darazo
Darazo

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labari Daga Darazo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share