Hausa novel

Hausa novel Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausa novel, Grocers, Dandaura, Abuja.

15/07/2024

____ME MAGANI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- -----
**★*PART (29) **★**.
Abinci ne gashi Nan iri iri na Alfarma Ummi ta shiryo shi,Dinning s**a zauna,Khairat zata zuba komai daban daban,Hunaif yace Haka ake cin abinci Mata da miji? Shuru tayi tana murmushi har Tea a cup daya tal ta hada musu,tana Zama a kujerarta yace ba Haka akeyi ba,hannunta ya riko ta mike tsaye ya daura ta saman Cinyarsa,Khairat kunya ta rufe ta, kasa ko tari tayi,tana gani ya Shiga ci Yana Bata a Baki,dole ta hakura har s**a Gama ci.
Bari naje wurin Ummi cewar Hunaif, Khairat ta kalleshi tare da cewa pls ka tafi Dani idan ka tafi tsoro zanji,Ga Yan Aiki ko Ina sannan ma kince zakiyi gyare gyare Kinga sai ki zauna kiyi kafin na dawo,ok Khairat ta Furta tare da mikewa tsaye ta raka shi Compound Allah ya dawo da Kai lfy,Ameen ya Furta Yana Murmushin Jin dadin Adduar ta.

Dawowa tayi ta fara gyaranta Shara,Mopping tare da wanke wanke ko ina ta gyarashi tsaf ya dauki kamashi,har ta Gama Hunaif Bai dawo ba,wayarta ta dauka tana dannawa har 1:30pm Shuru,Bayan tayi Sallah taji shugowar motarsa,dauke da Basket din Abinci ya shigo dashi daga wurin Ummi,Sallamar ta amsa Masa tare da karbar kayan hannunsa tana Sannu da zuwa? Ya Ummi?

Lfy take ya Furta Yana kallonta Yar yarinya da ita Wai shine ya aure ta,ita Kuma a ranta farin ciki takeyi ta Zama matar aure duk girman Namiji Bai wuce Matarsa ta aikeshi ba,yanzu yarinya da ita zata Iya Aiken Hunaif Kuma yaje,kanta taji ya Kara girma har wani yanga takeyi tace bari ya huta ta aikeshi ta gani zai je,Abinci s**a ci tare, shi dai Hunaif Bai dauki Khairat wata me hankali ba ganin Shekarunta kadan,Kallonta yake kamar Kanwarsa sabanin Matan daya aura tsofaffun guzumaye, da kuma kalar macen da yake so wacce tayi hankali 25yrs zuwa sama.

Suna Gama cin Abinci Bayan sun huta Suna Kallon Tv Khairat ta Kira Hunaif tace Mijin Khairat? Dariya yayi ba tare da ya shirya ba sannan ya amsa

Address

Dandaura
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa novel posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category