Salafiyya Methodology

Salafiyya Methodology IYAKA NA ABUDU WA IYAKA NASTA'IN�

Late Albanin Zaria: A Remarkable Scholar and ICT ExpertMuhammad Auwal Adam was a truly brilliant scholar whose life was ...
22/02/2026

Late Albanin Zaria: A Remarkable Scholar and ICT Expert

Muhammad Auwal Adam was a truly brilliant scholar whose life was dedicated to knowledge, teaching, and service to Islam and society.

🎓 Academic Achievements

He earned numerous qualifications with outstanding distinctions, including:

MSc in Telecommunication Engineering (Distinction)

MSc Telecom Engineering – Digital Bridge University

MA Islamic Studies (Distinction)

BA Islamic Studies – Bayero University Kano (First Class)

BSc Information & Communication Technology – FUT Yola (Second Class)

Diploma in Computer Science – FUT Yola

Diploma in Mass Communication – University of Jos

Diploma in Islamic Shari’ah Law – ABU Zaria

Diploma in Hausa Language – BUK

Certificate in Library Science

Professional Certifications (All with Distinction):

A+ Certification

Network+ (N+)

Linux Certification

MCP

MCT

MCSA

MCSE

CCNA

💼 Professional Profile

Islamic Scholar (Muhaddith)

Da’wah and Teacher

ICT Consultant

Telecommunication Engineer

Information & Communication Technologist

Certified Computer Networking Technician (NIIT)

Certified Computer Repair & Maintenance Technician (NIIT)

Certified Microsoft Engineer

📖 Biography

Name: Muhammad Auwal Adam
Born: 27th September 1960
Died: 1st February 2014 (Aged 54)
Nationality: Nigerian
Ethnicity: Hausa/Fulani
Religion: Islam (Sunni Salafi)
Main Interests: Hadith Studies & ICT

🏆 Award

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Prize (BUK, 1985) under Gaddafi’s Special Intervention Programme on Arabic Literature

🌟 Legacy

He influenced and mentored many scholars, academics, and professionals across Islamic studies, engineering, medicine, and other fields. His impact continues through his students and the institutions he served.

May Allah grant him Jannatul Firdaus and reward him abundantly for his knowledge and service. Ameen.

22/02/2026

KUJI TSORAN ALLAAH KUDENA TARA MUTANE KUNA WAHALAR DASU DON BASU TALLAFI
WANNAN RASHIN AIKI DA ILMINE, A GYARA DON ALLAAH

17/02/2026

ALHAMDULILLAHI
RAMADAN MUBARAK

KUZO KUJI ALBISHIRINKU ABOKAIKo kunsan cewa SUNNAH DATA sunyi fice agurin bada sarin Data, a farashi Mai rahusa da Babu ...
15/02/2026

KUZO KUJI ALBISHIRINKU ABOKAI

Ko kunsan cewa SUNNAH DATA sunyi fice agurin bada sarin Data, a farashi Mai rahusa da Babu kamarsu. katin Kira na waya, da kuma subscriptions na TV irin su GOTV, DSTV, da STARTIMES Kai harma da biyan kudin wuta wato NEPA a farashi dai dai, da ajjuhunku.
MTN 1GB = 300
GLO 1.5GB = 350
AIRTEL 1GB = 290

Ku danna link din dake qasa domin downloading app din SUNNAH DATA a playstore 👇👇👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.sunnahdata

Salafiyya Methodology
ne

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-40Rubutawa: Ahmad Saleh✍️Cigaba daga shafina 546 zuwana 550, kamar y...
14/02/2026

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-40

Rubutawa: Ahmad Saleh✍️

Cigaba daga shafina 546 zuwana 550, kamar yadda muka saba kawo muku:
Wannan sashe yana kokarin kare istighatha da kiran sheihi, yana cewa “niyya ce kawai” ko “hanya ce zuwa Allaah”.

Shafina 546:
النص العربي:
“…وليس ذلك دعاءً لغير الله
وإنما هو توسّل…”
Ma'ana:
“Wannan ba kiran wanin Allaah bane,
tawassuli ne kawai.”

Kuskure:
Sauya suna ba ya sauya hakika.
Idan an roki bawa kai tsaye duʿah’ ne, ba tawassuli ba.

Gyaran:
Tawassuli halasne:
da Sunayen Allaah,
da aiki nagari,
da duʿa’in rayayye salihi.

Ba da mamaci ko wanda ba yaji ba.

Shafina 547:
النص العربي:
“…والنيةُ لله
فلا يكون شركًا…”
Ma'ana:
“Niyya ga Allaah ce,
don haka ba shirka ba ne.”

kuskure:
Niyya mai kyau bata halatta ibada ga wanin Allaah ba.

Gyara:
Ibada tana bukatar:
1. Ikhlasi (ga Allaah kadai)
2. Ittiba'iʿ (bin Sunnah).
Duk abin da bai zo da hujja ba baza'a karba ba.

Shafina 548:
النص العربي:
“…وهو سببٌ جعله الله
للعباد…”
Ma'ana:
“Hanya ce da Allaah Ya sanya
domin bayinsa.”

Kuskure:
Kiran abu “sababbi” ba tare da dalili ba.
Addini ba ya tabbata sai da wahayi.

Gyara:
Sababbi a ibada:
dole ne suzo da Qur’ani ko Sunnah.
Ba a kirkiri hanyoyi daga zuciya ba.

Shafina 549:
النص العربي:
“…وقد جرّبه الصالحون
فوجدوه نافعًا…”
Ma'ana:
“Salihai sun gwada shi,
sun same shi mai amfani.”

Kuskure:
Kwarewar mutum ba hujja bace a aqida.
Hujja ita ce wahayi, ba labari ba.

Gyaran:
Addini:
ba a gina shi da kwarewa ko labari ba.

Shafina 550:
النص العربي:
“…ومن أنكر ذلك
حُرم البركة…”
Ma'ana:
“Wanda yaki wannan,
zai rasa albarka.”

Kuskure:
Tsoratar da masu rike Tauhidi.
Sanya bidi’a a matsayin alheri.

Gyaran:
Albarka tana cikin:
bin Qur’ani da Sunnah.
Ba cikin abin da bai da hujja ba.

KA’IDA
A ibada:
Ba a kallon niyya kadai.
Ba a kallon sakamako.
Ana kallon:
Shin Allaah Yayi umarni?
Shin Manzon Allaah ﷺ yayi?

Insha Allaah Rubutu na Gaba, littafin zai shiga daga darikar zuwa matsayin “hanyar tsira ta musamman.”

Zamu tashi shafina 551.

AL'FURQAN BAINA AULIYA'U RAHMAN WA AULIYA'U SHAIDAN-0013Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️Cigaba da fassarar littafin Al-Fu...
12/02/2026

AL'FURQAN BAINA AULIYA'U RAHMAN WA AULIYA'U SHAIDAN-0013

Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️

Cigaba da fassarar littafin Al-Furqan Bayna Auliya’ ar-Rahman wa Auliya’ ash-Shaytan na Shaykhul Islam Ibin Taymiyyah (rahimahullah).

Bambanci Tsakanin Karama Da Sihiri:
وَالْفَرْقُ بَيْنَ كَرَامَاتِ أَوْلِيَاءِ الرَّحْمٰنِ وَخَوَارِقِ أَوْلِيَاءِ الشَّيْطَانِ أَنَّ أَوْلِيَاءَ الرَّحْمٰنِ لَا تَحْصُلُ لَهُمُ الْخَوَارِقُ إِلَّا بِسَبَبِ الْإِيمَانِ وَالتَّقْوَى، وَهُمْ مُتَّبِعُونَ لِلرَّسُولِ ﷺ، وَأَمَّا أَوْلِيَاءُ الشَّيْطَانِ فَتَحْصُلُ لَهُمُ الْخَوَارِقُ بِسَبَبِ الشِّرْكِ وَالْفُسُوقِ وَالْعِصْيَانِ.
Ma'ana:
Bambanci tsakanin karaman waliyyan Rahma da abubuwan mamaki na waliyyan shaidan shine:

Waliyyan Rahma basa samun wani abin mamaki sai saboda imani da taqawa,
Kuma suna bin Manzon Allaah ﷺ.

Amma waliyyan shaidan suna samun irin wadannan abubuwa ne saboda:

Shirka,
Fasikanci,
Sabo ga Allaah.

Sharhi:
Ibin Taymiyyah yana nan yana koyar da mu mu rarrabe:
Ba duk wanda yake yin abin mamaki bane waliyyin Allaah.

Mutum zai iya:
Yin tafiya a iska,
Yin magana da aljani,
Bayyana abubuwan boye,

Amma hakan ba hujja bane cewa yana tare da Allaah.

Tambaya mafi muhimmanci:
Shin yana sallah?
Shin yana guje wa bidi’a?
Shin yana bin Sunnah?
Shin yana kauce wa shirka?

Idan ba haka bane, to abin da yake yi na iya zama taimako daga shaidan.
Dalili Daga Al-Qur’ani
Allaah yace:
أَلَا إِنَّ أَوْلِيَاءَ اللَّهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ
(Suratu Yunus 10:62-63)

Ma'ana:
Ku sani! Lalle waliyyan Allaah basu da tsoro kuma basu yin bakin ciki.
Sune wadanda s**a yi imani kuma s**a kasance masu taqawa.

Darasi:-
Karama tana:
Karawa mutum kusanci ga Allaah,
Taimakawa wajen tsayuwa a kan gaskiya,
Ba ta sabawa Shari’a.

Amma sihiri ko abin mamaki na shaidan:-
Yana kai mutum ga girman kai,
Yana sa ya sabawa shari’ah,
Yana iya kaiwa ga shirka.

Insha Allaahu a gaba Ibin Taymiyyah zai yi bayani kan:

Yadda shaidanu ke yaudarar mutane,

Da yadda wasu sufi ko masu bidi’a suke fadawa tarkonsu ba tare da sun sani ba.

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-39Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️Zamuci gaba daga shafina 541zuwana ...
10/02/2026

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-39

Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️

Zamuci gaba daga shafina 541zuwana 545, a tsari Shafi bayan shafi kamar yadda muka saba:
Wannan sashe yana karfafa istighatha (kiran taimako) ga sheihi da lafuzza na adduʿa’, abin da yake shirkane a ibada idan ga wanin Allaah.

A Shafina 541:
النص العربي:

“…ونادى المريدُ الشيخَ
عند الشدائد…”
Ma'ana:
“Muridi yana kiran Sheihi
a lokacin tsanani.”

Kuskure:
Kira/roko a lokacin tsanani ibada ce.
ga wanin Allaah kuwa shirkane.

Gyaran:
A lokacin tsanani:
Allaah kadai ake kira.
﴿إِذَا مَسَّكُمُ الضُّرُّ فَإِلَيْهِ تَجْأَرُونَ﴾
A Shafina 542:
النص العربي:

“…وقولُ: يا سيدي
سببٌ للفرج…”
Ma'ana:
“Fadin ‘Ya Sidi ko ya shehu (Ya shugaba)’
yana kawo sauki.”

Kuskure:
Sanya lafazin kiran bawa a matsayin hanyar sauki.
Sauya adduʿa’ ga Allaah zuwa ga bawa.

Gyaran:
Sauki daga:
Allaah ne kadai.
﴿وَإِن يَمْسَسْكَ اللَّهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُ إِلَّا هُوَ﴾
A Shafina 543:
النص العربي:

“…ومن أكثر النداء
نال الإغاثة…”
Ma'ana:
“Wanda ya yawaita kiran (Sheihi),
zai sami taimako Daga gareshi.”

Kuskure:
Yawaita kiran bawa ana dauka ibada ce.
Wannan istighatha ce ga wanin Allaah.

Gyaran:
Istighatha:
ga Allaah kadai.
﴿إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ﴾
A Shafina 544:
النص العربي:

“…ويُستجابُ له
ولو من بعد…”
Ma'ana:
“Ana amsa masa
ko da bayan rasuwarsa.”

Kuskure:
Ikirarin amsar roko daga mamaci.
Wannan ya sabawa Tauhidi da aikin Sahabbai.

Gyaran:
Sahabbai basu taba neman amsa daga Annabi ﷺ bayan wafati ba.
Sun nemi Allaah kai tsaye.

A Shafina 545:
النص العربي:
“…فلا يعدلُ المريدُ
عن هذا النداء…”
Ma'ana:
“Muridi kada ya bar
wannan kira.”

Kuskure babba:
Dorewa a kan shirka.
Kulle muridi daga tuba da gyara.

Gyaran:
Dorewa wajibi ne a:
Tauhidi,
bin Sunnah,
barin abin da Allaah Ya haramta.

KARSHE:
Wannan sashe ya:
mayar da adduʿa’/istighatha ga bawa,
rushe Tauhidi kai tsaye,
sabawa Qur’ani, Sunnah, da aikin Sahabbai.

Ahlussunnah suna tsayawa kan:
“Duk ibada ga Allaah kadai.”

Zamuci gaba insha Allaah daga shafina 546 zuwana 550:
(A nan littafin yana kokarin kare wadannan lafuzza, yana cewa “niyya ce kawai”, wata dabara ta bata Tauhidi.)

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-0038Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️Zamu tashi a shafina 536 zuwana 5...
08/02/2026

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-0038

Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️

Zamu tashi a shafina 536 zuwana 540, kamar yadda muke tafiya:

Wannan sashe yana daga cikin mafi hatsari ga aqida, domin yana magana ne kan tasarrufi (ikon sarrafa al’amura) da taimako bayan wafati.
A Shafina 536:
النص العربي:
> “…وللشيخ تصرّفٌ في الكون
بإذن الله…”
Ma'ana:
“Tijani yana da ikon sarrafa al’amuran duniya
da izinin Allaah.”

Shirka a ayyuka:
Jingina ikon tasarrufi ga bawa.

Wannan iko sifface ta Allaah kadai.

Gyaran:
Allaah ne kadai:
Mai mallakar iko da tafiyar da halitta.
> ﴿أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ﴾
“Da izinin Allaah” ba ya halatta shirka.

A Shafina 537:
النص العربي :
> “…ويقضي حوائج المريدين
حيثما كانوا…”
Ma'ana:
“Tijani yana biyan bukatun muridansa
duk inda suke.”

Kuskure:
Jingina amsar bukata ga bawa.
Wannan shine asalin ibada (duʿa’).

Gyaran:
Biyan bukata:
Allaah kadai Yake yi.
> ﴿أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ﴾
Duk wanda ake roka bayan Allaah, ibada ce aka karkatar.

A Shafina 538:
النص العربي :
> “…ويغيث من استغاث به
بعد انتقاله…”
Ma'ana:
“Tijani yana taimakon wanda ya nemi taimakonsa
bayan rasuwarsa.”

Shirka a ibada:
Istighatha ga mamaci.
Wannan ibada ce ga wanin Allaah.

Gyaran:
Ba a neman taimako sai daga:
Allaah kadai.
> ﴿إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ﴾
Sahabbai basu taba neman taimako daga Annabi ﷺ bayan wafatinsa ba.

A Shafina 539:
النص العربي :
> “…والتوسل به
سببٌ لقضاء الحاجات…”
Ma'ana:
“Yin tawassuli dashi
hanya ce ta biyan bukatu.”

Kuskure (idan bayan wafati):
Tawassuli da zatin mamaci ba tare da hujja ba.
Sauyawa zuwa duʿa’ ga bawa.

Gyaran:
Halattaccen tawassuli:
da sunayen Allaah,
da aiki nagari,
da duʿa’in rayayye salihi kawai.
Ba da mamaci ba.

A Shadina 540:
النص العربي:
> “…ومن تعلّق بالشيخ
نال الأمان والنجاة…”
Ma'ana:
“Wanda ya rataya da Sheihi,
ya samu aminci da tsira.”

Ya rushe Tauhidi:
Rataya zuciya ga bawa.
Sanya tsira a jingina ga mutum.

Gyaran:
Rataya zuciya:
ga Allaah kadai.

> ﴿وَعَلَى اللَّهِ فَتَوَكَّلُوا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ﴾
KARSHE:
Wannan sashe yakai littafin:
daga ghuluwy
zuwa shirka bayyananniya.

Ahlussunnah suna cewa:
Duk abin daya shafi duʿa’, taimako, tsira, da iko. Na Allaah ne kadai.

Zamuci gaba daga shafina 541 zuwa 545?

(A nan marubucin yana karfafa kiran Sheihi a zahiri da kalmomi na istighatha.)

AL'FURQAN BAINA AULIYA'U RAHMAN WA AULIYA'U SHAIDAN-0012Rubutawa: Ahmad Saleh ✍️Haryanzu Muna a BABI NA FARKO,Sheikhul I...
07/02/2026

AL'FURQAN BAINA AULIYA'U RAHMAN WA AULIYA'U SHAIDAN-0012

Rubutawa: Ahmad Saleh ✍️

Haryanzu Muna a BABI NA FARKO,
Sheikhul Islam Ibin Taymiyyah (Rahimuhullah)ya kawo sashen dake rufe babin gaba daya:
Jarabawar waliyai da yadda Allaah ke gwada su, domin kada a rude da abin da ake gani a zahiri.
الباب الأول
ابتلاءُ الأولياء وامتحانُهم
(Jarabawar waliyai da gwajinsu)
النصّ العربي:
> وأولياءُ اللهِ قد يبتليهم اللهُ بأنواعٍ من البلاءِ، في الفقرِ والمرضِ والخوفِ، كما يبتلي الأنبياءَ والصالحين، ليزدادوا إيمانًا وتقوىً وصبرًا.

وأمّا أولياءُ الشيطانِ فيُمدُّون في الغيِّ، وتُفتحُ لهم الدنيا، ويُعجَّلُ لهم بعضُ ما يريدون، استدراجًا وفتنةً.
Ma'ana:
Waliyan Allaah, Allaah kan jarrabe suda nau’o’in jarabawa kamar:
talauci,
rashin lafiya,
tsoro,
wahala,

kamar yadda Ya jarrabi annabawa da salihai,
domin su kara imani, takawa, da hakuri.
Amma waliyan shaidan kuwa:

ana kara musu bata,
ana bude musu duniya,
ana gaggauta musu abin da suke so,

duk wannan jansu ne zuwaga halaka (istidraj), ba girmamawa ba.

Sharhi:
1. Jarabawa alama ce ta kauna,
Mutane da yawa suna tunani:
“Idan Allaah yana son mutum, sai ya bashi sauki.”

Ibn Taymiyyah yace:
Ba dole ba.
Annabi ﷺ yace:

“Mutanen da s**a fi tsananin jarabawa su ne Annabawa, sannan masu kusanci dasu.”
(Tirmidhi,Hasanu Sahih)

Wato:
wahala, fushi.
wahala na iya zama alamar kauna
2. Sauki ba lallai alheri bane,
Wasu suna cewa:
“Ai wane yana da dukiya, yana da mabiya, yana da iko, lalle waliyyi ne.”

Ibin Taymiyyah yace:
Kaji tsoron wannan.

Allaah Yace:
> ﴿فَلَمَّا نَسُوا مَا ذُكِّرُوا بِهِ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ أَبْوَابَ كُلِّ شَيْءٍ﴾
“Lokacin da s**a manta abin da aka tunatar da su, sai Muka bude musu kofofin komai…”
(Al-An‘am 6:44).
Wannan istidraj ne, aja mutum a hankali zuwa hallaka.
3. Bambanci a sakamakon jarabawa

Waliyin Allaah, jarabawa tana kara shi kusanci da Allaah,
Waliyin shaidan, ni’ima tana kara mishi girman kai da bata,
4. Annabawa sun fi kowa wahala.
Nuh (AS),tsangwama.
Ibrahim (AS),wuta.
Musa (AS), tsoro da kunci.
Muhammad ﷺ, yunwa, ciwo, kiyayya.

Shin za mu ce ba waliyay bane? A’a.

5. Ma’aunin karshe
Ibin Taymiyyah ya kammala da ka’ida mai karfi:
Ba a san waliyin Allaah da ni’ima ko wahala ba,
sai da yadda yake tsayuwa kan gaskiya a kowane hali.

TAKAITACCEN BABI NA FARKO (AL-FURQAN):

Waliyyin Allaah = Imani, Takawa,
Karama tana kara biyayya ga Allaah,
Fitina, tana rushe shari’a.
Ibada ba tare da Sunnah ba rudani ce.
Taimakon shaidan ta hanyar sabo.
Jarabawa, alamar kaunace ga Allaah,
Ni’ima, na iya zama istidraj.

KARSHEN BABI NA FARKO KENAN.

Zamuci gaba:
Zamu shiga
BABI NA BIYU:
“Bayani kan al-wala'u’ wal-bara’ da tasirinsa a walittaka.”

insha Allaah zamu ci gaba da wannan fassara mai albarka har mu kammala littafin gaba daya, Kila Nan da shekara Daya ko biyu inmun dage😅

06/02/2026

INA BADA HAKURI YAU BABU KARATU UZIRI YAMIN YAWA

AL'FURQAN BAINA AULIYA'U RAHMAN WA AULIYA'U SHAIDAN-0011Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️Har yanzu muna babi na farko: Ibi...
05/02/2026

AL'FURQAN BAINA AULIYA'U RAHMAN WA AULIYA'U SHAIDAN-0011

Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh ✍️

Har yanzu muna babi na farko: Ibin Taymiyyah ya shiga maballin da yake warware rudani gaba daya:

Bambanci tsakanin karamar waliyin Allaah da abin mamakin shaidan.
Wannan shine zuciyar littafin Al-Furqan.
الباب الأول
الفرقُ بين كراماتِ أولياء الله وخوارقِ أولياء الشيطان

النصّ العربي:
> فكراماتُ أولياء اللهِ إنما تكونُ بسببِ إيمانِهم وتقواهم، وهي تُعينُهم على طاعةِ اللهِ ورسولِه، وتزيدُهم هدىً واستقامةً.

وأمّا خوارقُ أولياء الشيطانِ فإنما تكونُ بسببِ شركِهم أو فسوقِهم، وهي تُعينُهم على معصيةِ اللهِ ورسولِه، وتزيدُهم ضلالاً وطغياناً.
Ma'ana:
Karamar waliyan Allaah tana zuwa ne saboda:
imaninsu,
takawarsu,

kuma tana:
taimaka musu wajen biyayya ga Allaah da ManzonSa,
Tana Kara musu shiryuwa da tsayuwar kai a addini.

Amma abubuwan mamakin waliyan shaidan kuwa:
suna zuwa ne saboda shirka ko fasikanci,
kuma suna taimaka musu wajen sabon Allaah da ManzonSa,

Tana kara musu bata da girman kai.

Sharhi:
1. Karama tana kara biyayya, ba sabo ba,

Ibin Taymiyyah ya kafa ka’ida:
Duk abin daya saka ka kusanci Allaah, karama ce.
Duk abin daya saka kai nesa da Allaah fitina ce.

2. Karama bata karya shari’a,
Karamar waliyyin Allaah:
ba ta halatta haram
ba ta rushe farilla
ba tasa abar Sunnah,

Idan “ikon” yace:
“Kai ka wuce sallah.”
“Kai ka wuce shari’a.”
Ibin Taymiyyah yace:
“Wannan shaidan ne, ba Allaah ba.”

3. Abin mamaki ba ma’auni bane,
Tafiya a ruwa,
Tashi a iska,
Sanin asiri,
Kawo abu daga nesa.

duk na iya fitowa daga shaidan.

Amma:
tsoron Allaah
bin Sunnah
tawali’u.
wadannan ba shaidan ke bayarwa ba.

4. Halin zuciya bayan “ikon”

Ibin Taymiyyah ya lura da wani abu mai zurfi:
Karama tana kara tawali’u,
Fitina tana kara girman kai,
Idan mutum bayan “al’ajabi”:
yace “ni nafi kowa”
ya raina mutane,
ya dauki kansa sama da shari’a,
wannan alamar wilayyar shaidan ce.

5. Qur’ani ya riga ya fayyace
Allaah Ya ce:
> ﴿إِنَّ الَّذِينَ اتَّقَوْا إِذَا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِّنَ الشَّيْطَانِ تَذَكَّرُوا فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ﴾
“Masu takawa idan shaidan ya shafe su, sai su tuna, nan take su gane gaskiya.”
(Al-A‘raf 7:201)

Waliyin Allaah yana farkawa,
waliyyin shaidan yana kara nutsewa.

AL FURQAN a takaice (KA’IDOJI 5):
Karama tana karawa mutum bin shari’a
Fitina tana rushewa,
Karama tana kara tawali’u,
Fitina tana ƙara girman kai
Ma’auni Qur’ani da Sunnah.

Matsayarmu:
Mun riga mun rufe: Alamomin waliyan Allaah,
Alamomin waliyan shaidan,
Ibada tare da rudani,
Taimakon shaidanu,
Bambanci tsakanin karama da fitina,

Rubutu na gaba:
Zamu shiga sashen karshe na wannan babi:
“Jarabawar waliyai da yadda Allaah ke gwada su.”

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-0037Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh✍️Insha Allaah Zamu tashi Daga shafi...
04/02/2026

JAWAHIRUL MA'ANI WA BULUGUH AL AMANI JUZU'I NA BIYU-0037

Rubutawa: Auwalu Ahmad Saleh✍️

Insha Allaah Zamu tashi Daga shafina 531 zuwana 535, kamar yadda muka saba:

A wannan sashe, Tijani yana daure “karamomi” da tabbacin tsira, yana daga labarai marasa hujja zuwa matsayin aqida.

A Shafina 531:
النص العربي:

> “…وظهور الكرامة
علامةُ القَبول عند الله…”
Ma'ana:
“Bayyanar karama
alamar karbuwa ce a wurin Allah.”

Kuskure:
Sanya karama a matsayin ma’aunin karbuwa.

Gyaran:
Ma’aunin karbuwa shi ne:
imani, taqwa, bin Sunnah.
Karamomi ba hujja ba ne ga karbuwa.
> ﴿إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِندَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ﴾
A Shafina 532:
النص العرب

> “…ومن كثرت كراماته
عَظُم مقامُه…”
Ma'ana:
“Wanda karamominsa s**a yawaita,
matsayinsa yafi girma.”

Kuskure:
Auna matsayi da yawan abubuwan al’ajabi.

Gyaran:
Sahabbai sunfi kowa matsayi,
ba don karamomi ba,
sai don imani da biyayya.

A Shafina 533:
النص العربي
> “…ولا ينال هذه المقامات
إلا أهل طريقتنا…”
Ma'ana:
“Ba wanda ke kaiwa wadannan matsayai
sai mutanen darikarmu.”

kuskure:
Kebance falala ga kungiya guda.
Ware sauran Musulmai daga alheri.

Gyaran:
Falala tana tare da:
duk wanda yabi Allaah da Manzonsa ﷺ.

A SHAFI 534:
النص العربي
> “…وأهلها آمنون يوم الفزع الأكبر…”
Ma'ana:
“Mutanenta suna cikin aminci
a ranar tsoro mafi girma.”

Kuskure:
Ikirarin aminci na tabbata ga ƙungiya.

Gyaran:
Aminci a Lahira:
ga wanda Allaah Ya yarda da shi,
baga duk mai jingina kansa da darika ba.

A Shafina 535:
النص العربي

> “…فمن لزمها
فقد ضمن النجاة…”
Ma'ana:
“Wanda ya manne mata,
ya tabbatar da tsira.”

kuskure:
Tabbatar da tsira bisa jingina ga darika.
Rushe ma’aunin Qur’ani da Sunnah.

Gyaran:
Tsira tana ga:
wanda ya mutu a kan Tauhidi da Sunnah.

“Duk wanda ya aikata abin daba ya cikin al’amarinmu, an ki shi.”(Bukhari & Muslim)

DARASI:
Ahlussunnah:
suna girmama waliyyai,
amma basa dora aqida kan labaran al’ajabi,
kuma basa bada tabbacin tsira ga kowa sai da hujja.

ZaMuci gaba daga shafina 536 zuwana 540 insha Allaah?

(A nan littafin yana shiga batun tasarrufi/ikon sarrafa al’amura,abin da yake da matukar hatsari ag aqidar Musulmi.)

Address

Kano
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Salafiyya Methodology posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category