Matari soba JBWIS

Matari soba JBWIS Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Matari soba JBWIS, Grocers, Matari soba local government, Zaria.

Dan sheik jaafar Mahmoud Adam wato Salim Ja"afar Mahmoud Adam  kenan tare da Dr Bashir Aliyu Alfurqan.Allahu yajikan mal...
21/03/2026

Dan sheik jaafar Mahmoud Adam wato Salim Ja"afar Mahmoud Adam kenan tare da Dr Bashir Aliyu Alfurqan.

Allahu yajikan malam da rahama.

bayin Allah, malamai magada annabawa Allah ya gafarta muku zunubanku
21/03/2026

bayin Allah, malamai magada annabawa

Allah ya gafarta muku zunubanku

Alhmdllh masha Allah masallacin JBWIS matari soba local government Kaduna state sun gudanar da sallar idi karama lfy, Al...
20/03/2026

Alhmdllh masha Allah masallacin JBWIS matari soba local government Kaduna state sun gudanar da sallar idi karama lfy, Allah ya maimaita mana na Badi lfy

written ✍️ by

IDAN SALLAR IDI TA HADA DA JUMA’A  GASKIYA DA KUSKUREN DA YAKE YADUWAYanzu mutane da yawa suna yawo da wata magana mai h...
19/03/2026

IDAN SALLAR IDI TA HADA DA JUMA’A GASKIYA DA KUSKUREN DA YAKE YADUWA

Yanzu mutane da yawa suna yawo da wata magana mai haɗari suna cewa Idan ka yi sallar Idi babu Juma’a a kanka babu ma Azahar

Wannan magana ba ƙarama ba ce, domin tana shafar ibada mafi girma a Musulunci wato SALLAH

Da farko ya k**ata mu fahimta cewa Allah Maɗaukaki ya wajabta sallar Juma’a a cikin Al-Qur’ani inda Ya ce Ya ku waɗanda s**a yi imani! Idan aka kira sallah ranar Juma’a, ku gaggauta zuwa ambaton Allah
(Suratul Jumu’ah 9)

Wannan aya tana tabbatar da cewa Juma’a farilla ce mai ƙarfi ba a barinta da sauƙi ba

Amma idan sallar Idi ta zo a rana guda da Juma’a me Shari’a ta ce?

Annabi (SAW) ya bayyana mana hakan a fili A hadisi ingantacce, ya ce an haɗu muku a wannan rana Idi da Juma’a wanda ya so ya halarci Juma’a ya halarta wanda kuma bai halarta ba to ya yi Azahar

Wannan hadisi yana nuna abubuwa guda biyu masu muhimmanci

Na farko An ba da rangwame ga wanda ya yi sallar Idi cewa zai iya barin zuwa Juma’a.
Na biyu Wannan rangwame ba yana nufin ya bar sallah gaba ɗaya ba ne sai dai ya koma yin Azahar

Saboda haka, kuskure ne babba mutum ya ce
Na yi Idi, shi ke nan babu sauran sallah a yau

Wannan fahimta ba ta da asali a cikin Al-Qur’ani ko Sunnah

Malamai da dama sun yi bayani a kan wannan batu. Daga cikinsu akwai Ibn Taymiyyah da Ibn Qudamah, waɗanda s**a tabbatar da cewa
Wanda ya halarci Idi yana da zaɓi ko ya je Juma’a ko ya yi Azahar

Amma kuma sun jaddada cewa ba a sauke masa Azahar ba ko da ya bar Juma’a

Haka kuma, limami da wasu daga cikin mutane dole su tsaya su yi Juma’a domin kada wannan ibada ta ɓace gaba ɗaya a gari

Don haka gaskiyar magana ita ce Idan ka yi Idi Kana da zaɓi kan Juma’a amma ba ka da zaɓi kan Azahar

Idan ka bar duka Juma’a da Azahar to ka yi kuskure mai girma kuma ka bar farilla

Ya kai ɗan’uwa addini ba a ɗauka da jin magana kawai ba ana ɗauka ne da hujja da ilimi Yawan magana a kafafen sada zumunta ba ya maye gurbin gaskiya

Allah yasa mudace

INNALILAHI WANNA ILAIHI RAJI'UNYan uwa muna masu neman addu'oinku bisa wannan jarabawan da Allah yayiwa babban Alaramman...
19/03/2026

INNALILAHI WANNA ILAIHI RAJI'UN
Yan uwa muna masu neman addu'oinku bisa wannan jarabawan da Allah yayiwa babban Alaramman mu Alaramman Ahmad Sulaiman Kano yayi hatsari kuma yanzu haka yana Asibiti.
muna Addu'ar
Allah yabashi lafiya yasa kaffarane. Amin

sanarwa daga masallacin JBWIS matari soba local government Kaduna state shuwagabanin masallacin JBWIS matari sun tsayar ...
19/03/2026

sanarwa daga masallacin JBWIS matari soba local government Kaduna state

shuwagabanin masallacin JBWIS matari sun tsayar da Lokacin da za a gudanar da sallar idi karama a gobe juma,a 1 ga watan sallah,1447 Wanda yayi dai dai da 20/3/2026 idan Allah ya kaimu

TIME: karfe 9: 00 na safe ,dai dai za a ta da sallah
A babban masallacin idi Wanda yake kudu da garin matari , hanyar kajan

ga duk Wanda yake so ya Sami sallar idi a wannan masallaci ba a Kara Koda 1 minutes akan Lokacin da aka Saka ,

Allah ya kaimu da rai da lfy
written by

Alhmdllh  A yau laraba  29 ga Ramadan Wanda yayi dai dai 18/3/2026 , masallacin JBWIS matari soba local government Kadun...
18/03/2026

Alhmdllh A yau laraba 29 ga Ramadan Wanda yayi dai dai 18/3/2026 , masallacin JBWIS matari soba local government Kaduna state ta rufe tafsir din AlQUR'ANI Mai girma, Wanda sheikh Adamu zakariyya matari yake Gabatarwa, Allah ya kaimu na Badi lfy
written ✍️ by

Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya haɗawa marayu sama da miliyan (70) a wurin tafsirinsa na wannan shekarar:Kungiyar ...
17/03/2026

Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya haɗawa marayu sama da miliyan (70) a wurin tafsirinsa na wannan shekarar:

Kungiyar Izala karkashin Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau ta karbi tallafin marayu daga hannun Al-ummar Annabi (SAW) tun daga 1 ga Ramadan 1447 zuwa 20 ga Ramadan kimanin Naira 76,615,425 (miliyan saba’in da shida da dubu dari shida da sha biyar da dari hudu da ashirin da biyar).

Kungiyar Izala ta sayo shinkafa mai 25kg guda 1500, atamfofi 750 da shaddoji 750 da kudin naira 5k ga marayu 1500, wanda ta kashe kudi kimanin Naira 66,055,000 (miliyan sittin da shida da dubu hamsin da biyar).

A ranar 21 ga Ramadan 1447, Kungiyar Izala ta ba wa kowanne maraya cikin mutum 1500 maza da mata shinkafa 25kg, atamfa ga mata, shadda ga maza da naira dubu biyar (5k) kudin dinki.

Idan Allah ya nuna mana bayan Ramadan, Kungiyar Izala za ta koyar da iyayen marayu 200 sana’a tare da ba su jari, wanda za a kashe kudin kimanin miliyan goma (10M) domin wannan aiki.

Allah ya saka wa dukkan wadanda s**a bada tallafin ga marayu da mafificin alkhairi. Allah ya saka wa masu tara wannan kudin da rabawa marayu suma da mafificin alkhairi. Allah ya karba ya bada lada. Ameen.

Allah ya sakawa Malam da Alkhairi.🙏🙏

*Da ka san irin ƙima da mutuncin da kake gina wa kanka ta hanyar kaucewa roƙon abin hannun mutane, da ba za ka sake tamb...
17/03/2026

*Da ka san irin ƙima da mutuncin da kake gina wa kanka ta hanyar kaucewa roƙon abin hannun mutane, da ba za ka sake tambayar abin hannun kowa ba.*

*Ku guji roƙo, ku k**a sana'a. Idan Allah ya yassare maka ka taimaki mutane ba tare da sai sun roƙe ka ba.*

*Allah ya sa mu dace.*
kuyi following and like na wannan page domin fadakarwa da wa,azantarwa
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

Maza ankwanta dama 😭 Allah ya haɗa fuskokin Mu a gidan aljannah fiirdausii 🤲 •Sheikh Abubakar Mahmoud gumi 🤲 •Sheik alba...
17/03/2026

Maza ankwanta dama 😭
Allah ya haɗa fuskokin Mu a gidan aljannah fiirdausii 🤲

•Sheikh Abubakar Mahmoud gumi 🤲

•Sheik albani zaria Rahimahullah 🤲

•Sheik Ja'afar Mahmud Adam Kano 🤲

• Sheikh Ahmed B.U.K 🤲

• DR IDRIS ABDUL AZIZ DUTSEN TANSHI RAHIMAHULLAH 🤲

Allah yaji kansu da rahama

17/03/2026

kissan annabi Musa da fir,auna

Darasi Na 06 Akan Tsarkin Mata.(Alakar Jinin Haihuwa Da Azumin Mace)✍️To Jinin Haila Hukuncin sa Daya Dana Haihuwa Wajen...
17/03/2026

Darasi Na 06 Akan Tsarkin Mata.
(Alakar Jinin Haihuwa Da Azumin Mace)

✍️To Jinin Haila Hukuncin sa Daya Dana Haihuwa Wajen Hana Ayyukan Ibadah.

✍️Sanna Shi Jinin Haihuwa Yafi Jinin Haila Dadewa Bai Dauke Ba Kamar Yanda Bayanai Sun Gabata A Baya.

✍️Kuma Koda Ranar Da Mace Ta Haihu Jinin Ya Dauke To Zatayi Wanka Taci Gaba Da Sallah Idan Ma Bata Tsoron Danta Ya Rasa Nono To Zata Ci Gaba Da Azuminta .

✍️Kuma Idan Har Ya Wuce Kwanakinsa Na Shara'a Wato Kwana 40 To Zatayi Wanka Taci Gaba Da Sallahrta Da Azumi Domin Lokacin Ya Zama Jinin Cewo.

Allahu A,alamu

Address

Matari Soba Local Government
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Matari soba JBWIS posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category