23/12/2025
MANZUMA
(Littafin Shehu Muhammadu Fal Al-alawiy Attijaniy RTA)
Kashi na daya (Falalar Huduri)
Shehin Malamin Yana cewa
1. KA SANI! LALLAI KARANTA WURIDIN NAN ZAI SHIRYAR DAKAI WANI GWADABE DA ZAI KAIKA DAKI CAN CIKI.
Wato Karanta lazumi da wazifa da zikirin juma'a na darikar tijjaniya, zai sadar da mutum zuwa ga wani gwadabe da zai samu qwayar shiriya (Ma'arifa) ba ɓawo ba (Shari'a).
2. BARI MA! ABIN KEWAYAWA GARESU CIKIN ABINDA KE TSARKAKE MUSU ZUCIYA, GARESHI YAKE, BABU TA-BA-BA.
Sufaye wayanda suke neman tsarkin zuciya, a cikin karanta wuridin tijjaniya suke samun haka ɗin.
3. SHARAƊINSA SHINE HALARTO ZATIN TSANIN NAN NAMU DAGA FARKO HAR QARSHEN WURIDIN.
Samun Qwayar shiriya da tsarkin zuciya ta hanyar karanta wuridin tijjaniya, tana da sharadi wanda da ita ne buri yake cika. sharadin kuwa shine Halarto Suffar Shehu Tijjani yayin da kake wuridin.
Abin nufi da halartowa (huduri), shine kaji, ka yarda yana zaune a gabanka yana kallon ka bisa yadda kake yin wuridin tun daga kan ladabin da kayi a zaman ka, har zuwa niyyarka da sanin ma'anar abinda kake faɗi har ka gama.
4. YANA TARE DA KAI ADUK YADDA KAYI ZATONSA, WAYANDA S**A SAMU SHIGA, DA HAKA S**A SHIGE.
Gwargwadon yadda ka halarto shehu tijjani, gwargwadon madadin da zaka samu daga gareshi. In ma baka halarto shi ba, haka zaka gama ka tashi babu riba sai dai ladar niyya. Wayanda S**a samu muradi a tijjaniya, da qarfin huduri s**a samu hakan.
5. SHI HUDURI SHINE RAI GA DUKKAN AIKI, KAR KA SHAGALA DA ABINDA BASHI KAKE KARANTAWA A WURIDIN BA.
Wuridi ko wani nau'in ibada, huduri ne ransa. Dan haka kar ka bari wani abu ya shigo zuciyarka yasa ka manta da ma'anar abinda kake karantawa cikin wuridin.
Misali, Ana so ka karanta Istigfari yayin wazifa kana mai sanin ma'anarta kana bibiya Kamar haka: ASTAGFIRULLAH ina tuba ga Allah ALLAZI wannan da LA ILAHA ILLA HUWA babu kowa da komai sai shi ALHAYYUL QAYYUM shine rayayye kuma tsayayye (tun babu kowa ko tsayayye akan lamarinsa dana bayinsa) ✍️ Dan Lyman NedaiLyman