Dr. Abba Youth Political

Dr. Abba Youth Political Dr. Abba Youth Political Initiative Forum �

HON. DR. ABBA YA’U YA HALARCI TARON KADDAMAR DA KWAMITIN YAƘIN NEMAN ZAƁEN APCShugaban Ƙaramar Hukumar Roni, Hon. Dr. Ab...
03/11/2026

HON. DR. ABBA YA’U YA HALARCI TARON KADDAMAR DA KWAMITIN YAƘIN NEMAN ZAƁEN APC

Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni, Hon. Dr. Abba Ya’u, PhD, ya halarci taron kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar Majalisar Tarayya na mazabar Kazaure–Roni–Gwiwa–Yankwashi, Engr. Ahmad Rufai Zakari.

Taron, wanda Shugaban Ƙaramar Hukumar Kazaure, Hon. Mansur Dabuwa, ya jagoranta, ya samu halartar shugabannin ƙananan hukumomin yankin, dattawan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki na APC.

An tattauna batutuwan haɗin kai da rawar da kowane ɓangare zai taka a harkokin yaƙin neman zaɓen.

Abubakar Lawan
Director, Media And Publicity
Dr. Abba youth political initiative forum
Thursday,3th November 2026

🎓 SAƘON TAYA MURNA GA SHUGABAN ƘUNGIYA, SADIQ HASSAN AMARYAWAƘungiyar Dr. Abba Youth Political Initiative Forum na miƙa ...
22/10/2026

🎓 SAƘON TAYA MURNA GA SHUGABAN ƘUNGIYA, SADIQ HASSAN AMARYAWA

Ƙungiyar Dr. Abba Youth Political Initiative Forum na miƙa saƙon taya murna ga Shugabanta, Sadiq Hassan Amaryawa, bisa samun nasarar kammala karatunsa na Professional Diploma in Dental Surgery Technician (DST) a Kazaure School of Health Technology, inda ya samu sakamako na Upper Credit a watan Yuli, 2025.

Wannan nasara abin farin ciki ne, kuma tana nuna muhimmancin jajircewa wajen neman ilimi da ƙwarewar sana'a. Muna fatan wannan mataki zai zama sanadin ƙarin buɗe ƙofofin alheri da samun nasarori a rayuwarsa ta gaba.

A madadin dukkan mambobin ƙungiyarmu, muna taya ka murna bisa wannan gagarumar nasara.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya ilimin ya zama mai amfani, Ya ƙara maka basira da nasara, Ya kuma ba ka damar amfani da iliminka wajen taimaka wa al'umma.

Abubakar Lawan
Director Media & Publicity
Dr. Abba Youth Political Initiative Forum
Thursday, 22 October 2026

WELCOME ADDRESS AND APPRECIATION MESSAGE2026 GLOBAL HANDWASHING CAMPAIGN CELEBRATION  RONI LOCAL GOVERNMENT, JIGAWA STAT...
21/10/2026

WELCOME ADDRESS AND APPRECIATION MESSAGE
2026 GLOBAL HANDWASHING CAMPAIGN CELEBRATION RONI LOCAL GOVERNMENT, JIGAWA STATE

On behalf of the good people of Roni Local Government, we warmly welcome Her Excellency, Haj. khadija A. Umar Namadi, the wife of the Executive Governor of Jigawa State, to Roni Local Government for the 2026 Global Handwashing Campaign Celebration.

Your presence at this important occasion is a great honour to our people and a demonstration of your commitment to promoting public health, hygiene, sanitation, and the overall well-being of our communities. We sincerely appreciate your support and the attention you continue to give to initiatives that improve the lives of the people of Jigawa State.

We also extend our heartfelt appreciation to the Chairman of the Occasion, Hon. Colonel Muhammad Alhassan (Rtd.), Honourable Commissioner, Ministry of Water Resources, Jigawa State, and our distinguished guest for their leadership and commitment to the success of this programme.
Our profound gratitude goes to all government officials, traditional rulers, community leaders, health workers, development partners, invited guests, and the entire people of Roni who took time out of their busy schedules to attend this memorable occasion.

As we bring this memorable gathering to a close, we wish Her Excellency and all our distinguished guests a safe and peaceful journey back to their respective destinations. May the Almighty Allah protect you throughout your journeys, grant you His blessings, and bring us together again on future occasions.
Once again, thank you all for honouring Roni Local Government with your presence.

Long live Roni Local Government!
Long live Jigawa State!
Long live the Federal Republic of Nigeria!

Wed.21st.Oct.2026

HON. DR ABBA YAU RONI
EXECUTIVE CHAIRMAN
RONI LOCAL GOVERNMENT
JIGAWA STATE

Tabbas
19/10/2026

Tabbas

Wannan haka yake APC ce zamu yi tun daga sama har ƙasa babu maganar yin Anti-party
19/10/2026

Wannan haka yake APC ce zamu yi tun daga sama har ƙasa babu maganar yin Anti-party

LOKACI YAYI DA ZAMU SAKA ALKHAIRI DA ALKHAIRI WAJAN SAKE ZABAR MAI GIRMA ADALIN GWAMNA BISA IRIN AYYUKAN DA YAYI NA RAYA...
17/10/2026

LOKACI YAYI DA ZAMU SAKA ALKHAIRI DA ALKHAIRI WAJAN SAKE ZABAR MAI GIRMA ADALIN GWAMNA BISA IRIN AYYUKAN DA YAYI NA RAYA BIRNI DA KARKARA A FADIN JAHAR JIGAWA.

MAI GIRMA ADALIN GWAMNA, GWAMNAN TALAKAWA MALAMIN GWAMNA,YAYI AYYUKA BILA ADADIN A FADIN JAHAR SA,

IRIN AYYUKAN DA YAYI NA RAYA BIRNI DA KARKARA.

SAMAR DA TITINA A BIRNI DA KARKARA DOMIN SAMUN INGATTATUN HANYOYI A FADIN JAHAR SA.

SAMAR DA RUWAN SHA A KO INA A FADIN JAHAR SA.

DAUKAR MA AIKATA A FADIN JAHAR SA.

DAUKAR NAUYIN KARATUN DALIBAI BILA ADADIN A FADIN JAHAR SA.

BADA KAYAN DOGARO DA KAI, MUSSAMMAN KAYAN NOMA DA KIWO.

GINA ASIBITOCI DOMIN SAMAR DA INGATTATUN LIKITOCI A FADIN JAHAR SA.

DA WANNAN KADAI YAKAMATA A YABA WA MAI GIRMA ADALIN GWAMNA.

HIS EXCELLENCE ALHAJI DR.MALAM UMAR NAMADI DANMODI.

MAI GIRMA ADALIN GWAMNA NE YA KAWO ADALIN CHAIRMAN HON.DR.ABBA YAU RONI.DON HAKA DOLE ALUMMAR KARAMAR HUKUMAR RONI SU YABAWA MAI GIRMA ADALIN GWAMNA.BISA IRIN AYYUKAN DA MAI GIRMA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR RONI YAYI.

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR RONI SHINE SHUGABA MAFI KUSANTAR ALUMMAR SA.

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR RONI SHINE SHUGABA MAFI KOKARI WAJAN TAIMAKON ALUMMA, SHINE SHUGABA MAFI DAUKAR NAUYIN KARATUN A FADIN KANANAN HUKUMOMIN JAHAR JIGAWA.

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR RONI SHINE SHUGABA MAFI GINA TATTALIN ARZIKIN KARAMAR HUKUMAR SA,A FADIN KANANAN HUKUMOMIN JAHAR JIGAWA.

DA WANNAN KADAI YA ISA MUSAKE ZABAR SU A KARO NA BIYU DOMIN CIGABA DA BUNKASA AYYUKAN ALUMMA.

SING.............
COMRD SADIK HASSAN AMARYAWA

Mai Girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni, Hon. Dr. Abba Ya’u, PhD, na daga cikin waɗanda s**a halarci taron ƙaddamar da k...
15/10/2026

Mai Girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni, Hon. Dr. Abba Ya’u, PhD, na daga cikin waɗanda s**a halarci taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, wanda ya gudana a jiya a Abuja.

Taron, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa, ya haɗa manyan jiga-jigan siyasa da masu ruwa da tsaki domin ƙaddamar da kwamitin tare da tsara matakan gudanar da ayyukan da s**a shafi yaƙin neman zaɓen.

Kasancewar Hon. Dr. Abba Ya’u a wannan taro ya ba shi damar kasancewa cikin sauran mahalarta wajen tattauna muhimman batutuwan siyasar ƙasa, tare da bayyana kasancewar Ƙaramar Hukumar Roni cikin manyan harkokin siyasar Najeriya.

SAKON TA’AZIYYA GA MANSIR MUSAINNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN.Shugabanni da mambobin Dr. Abba Youth Political Initia...
14/10/2026

SAKON TA’AZIYYA GA MANSIR MUSA

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN.

Shugabanni da mambobin Dr. Abba Youth Political Initiative Forum Karkashin Jagorancin Comr Sadiq Hassan Amaryawa suna miƙa saƙon ta’aziyya ga ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar, Mansir Musa, bisa rasuwar mahaifinsa.

Mansir Musa, wanda yake riƙe da muƙamin Treasurer a cikin ƙungiyar, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan mahaifinsa da rahama, Ya gafarta masa

kurakuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Haka kuma, muna addu’ar Allah Ya ba iyalansa da ‘yan uwa da abokan arziki haƙurin jure wannan babban rashi.

Allah Ya sa mu cika da imani idan tamu ta zo. Amin ya Rabbal Alamin.

TARON ƘADDAMAR DA ’YAN TAKARAR KAZAURE EMIRATE: ENGR. AHMAD RUFAI ZAKARI DA HON. DR. ABBA YA’U SUN HALARTA A ranar Asaba...
11/10/2026

TARON ƘADDAMAR DA ’YAN TAKARAR KAZAURE EMIRATE: ENGR. AHMAD RUFAI ZAKARI DA HON. DR. ABBA YA’U SUN HALARTA

A ranar Asabar da Lahadi, an gudanar da babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na yankin Kazaure Emirate, wanda ya haɗa ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi, domin ƙaddamar da ’yan takarar jam’iyyar da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin shugabanni da masu ruwa da tsaki.

Taron ya samu halartar Engr. Ahmad Rufai Zakari, ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Kazaure–Roni–Gwiwa–Yankwashi, tare da Mai Girma Hon. Dr. Abba Ya’u, Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni, da sauran jagorori da jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar.

Taron ya kasance wata dama ta haɗuwar shugabannin APC domin tattauna batutuwan da s**a shafi tafiyar jam’iyyar, ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da fahimtar juna tsakanin shugabanni da magoya baya a matakai daban-daban.

Halartar Engr. Ahmad Rufai Zakari da Hon. Dr. Abba Ya’u na daga cikin abubuwan da s**a ƙara fito da muhimmancin haɗin kai da hulɗa tsakanin jagororin jam’iyyar a yankin, domin ƙarfafa fahimtar juna da tattauna makomar APC a Kazaure Emirate.

Taron ya kuma samu halartar sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar da wakilai daga ƙananan hukumomin da s**a haɗa yankin.

Abubakar Lawan
Director Media & Publicity
Dr. Abba Youth Political Initiative Forum
Sunday, 11 October 2026

Asiwaju Falle Biyu Ce
08/10/2026

Asiwaju Falle Biyu Ce

Address

Roni

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr. Abba Youth Political posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share