03/07/2024
INDA RANKA: Budurwa ta saki matar saurayinta ta Whatsapp da izinin mijin
A wani yanayi mai matukar daure kai da ya faru, wata matar Aure Ameera (mun boye sunan) ta fallasa yadda mijinta ya rubuta takardar saki ya baiwa budurwasa Ummi (mun boye sunan) da nufin cewa duk sanda matar tasa ta nemi tada mata hankali to ta sake ta a madadinsa,
Majiyarmu ta Jaridar A Yau ta ruwaito Matar wacce ta tura a shafukan neman shawara ta ce "A bata shawara domin ji take yi kamar ta ka$he kanta, Mace yar uwata ta ci
min mutunci, Ya Allah kabi min hakkina
wallahi takardan sakina ta turo
min a WhatsApp. Kuma da rubutun (Handwriting) din mijina ya Allah, Wayyo ni"
Sai dai a nata martanin budurwar ta shaidawa majiyar A Yau cewa ita Ameera ce ta fara takalar ta inda kullum sai ta kira ta a waya da dandalin sadarwa ta ci mata mutunci kuma tana hadawa da iyayenta tana gargaɗinta ta rabu da mijinta, a cewar Ummi duk yadda ta kai ga haƙuri sai da ta kule ta,
"Kuma abun takaici ba ni nace ina son mijin Ameera ba, shi ya ƙwallafa ransa a kaina, amma har bina a boye take yi, har watarana ta ganni da ATM din mijinta shine ta bi ta kara daga hankalinta"
To sai dai A Yau ta ruwaito daga bisani Ameera ta baiwa Ummi (budurwar saurayin nata) hakuri sannan ta roƙi jama'a su yi wa Allah su daina zagin Ummi, "Matsala ce ta cikin gida kuma muna kan tattaunawa domin samun maslaha" inji Amira
Bayanai sun nuna daga nan ne mijin ya dauki mataki inda ya baiwa budurwar umurni ta turawa matar tashi takardar saki duk sanda ta sake takalar ta wanda kuma hakan aka yi....✍️