27/07/2026
DAMAR AIKI A ƘASASHEN WAJE: Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sabon Tsari Don Kare 'Yan Najeriya Daga Damfara
Daga Hayaki Online Hausa
A wani babban mataki na inganta damar aikin yi ga 'yan Najeriya, Gwamnatin Tarayya tare da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ƙungiyoyin masu daukar ma'aikata da sauran masu ruwa da tsaki sun ƙaddamar da sabon tsarin da zai sauƙaƙa wa 'yan ƙasa samun ingantattun ayyuka a ƙasashen waje cikin aminci da bin doka.
An bayyana sabon tsarin ne a wani taro da aka gudanar a Legas, inda aka bayyana cewa manufarsa ita ce kawo ƙarshen damfara, cin zarafi da kuma hanyoyin da ba su dace ba wajen tura ma'aikata zuwa ƙasashen waje.
Muhimman abubuwan da sabon tsarin ya ƙunsa:
1. Samar da tsarin daukar ma'aikata na zamani ta hanyar fasahar zamani (Digital).
2. Kare masu neman aiki daga damfara da cin zarafi.
3. Tabbatar da cewa ayyukan da ake tallatawa na sahihai ne kuma an tantance su.
4. Haɗa ƙwararrun 'yan Najeriya da ingantattun guraben aiki a ƙasashen duniya.
Gwamnati ta ce za ta kuma ƙarfafa wayar da kan masu son yin hijirar aiki, ta ba su horo kafin tafiya, tare da samar da hanyoyin kai ƙorafi idan wani ya tauye musu haƙƙi.
A nata ɓangaren, NLC ta jaddada cewa duk ma'aikacin da ya yi hijira yana da haƙƙin samun mutunci, kariya da adalci ba tare da la'akari da ƙasarsa ko matsayin hijirarsa ba.
Masana sun yi imanin cewa idan aka aiwatar da wannan shiri yadda ya k**ata, Najeriya za ta samu ƙarin damar samar wa matasa ayyukan yi a ƙasashen waje, tare da rage damfara da safarar mutane, da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
🗣️ Me kuke gani? Shin wannan sabon tsari zai taimaka wajen rage damfarar masu neman aiki a ƙasashen waje? Ku bayyana ra'ayoyinku a sashin sharhi.
📰 Majiyar Labari: Vanguard Najeriya