Da'irar Kontagora

Da'irar Kontagora Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Da'irar Kontagora, Grocers, KONTAGORA, Kontagora.

Da'irar Kontagora (Page) Shafi ne da aka Samar Zaina Kawo maku Labaran Tarukan Harkar musulunci a karkashin jagorancin Sayyid Zakyzaky (H) musamman Yankin Kontagora da kewaye, dama Kasa baki daya

TARON TUNAWA DA SHAHIDAN QUDS 2014 KARO NA 12 A ZARIA Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Jagora Shaikh Ibrah...
25/07/2026

TARON TUNAWA DA SHAHIDAN QUDS 2014 KARO NA 12 A ZARIA

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabi a taron tunawa da waƙi'ar Ƙudus ta 25 ga watan Yulin 2014. Taron ya gudana ne a yau Asabar 25/7/2026 a muhallin Darur Rahma da ke Dambo, a Zariya.

Jagoran ya fara jawabinsa da nuna alhini dangane da waƙi'ar Ashura da kuma wafatin Imam Hassan Mujtaba (A.S). Sannan ya tunatar dangane da arba'in da ake fuskanta, da kuma jana'izar shahidin wannan al'umma, Shahid Sayyid Ali Khamene'i (RH).

Jagora ya jaddada cewa: "wannan taron, taro ne na tunawa da waƙi'ar da ta auku a ranar 28 ga watan Ramadan, 1436 daidai da 25 ga watan Yulin 2014. Shekaru 12 ke nan cif-cif a ƙidayar miladiyya."

Har wa yau, Jagora (H) ya tunatar da yadda aka soma muzaharar Ƙudus a Nijeriya, wadda aka fara gudanar da ita a Juma'ar farko bayan watan Ramadan a Zariya. Daga bisani kuma ta faɗaɗa zuwa sassan ƙasar nan sakamakon ƙaruwa da yawan jama'ar da ke halarta. Haka kuma ya yi bayanin yadda al'amarin Falasɗinu ya samu karɓuwa a tsakanin al'umma.

"Muzaharar Ƙudus na duniya nuna goyon baya ne ga al'ummar Falasɗinu wanda ƴan share wuri zauna ke musgunawa da zaluntar su tsawon shekaru fiye da 70", inji Jagora.

Ya ƙara da cewa: "Ana nuna cewa, ba a yadda da zalunci ba ne."

Har wa yau, a wani ɓangare na jawabinsa, Jagora ya tunatar da al'umma dangane da waƙi'ar da ta auku a rana irin ta yau. Ya ce, muzaharar Ƙudus ta wannan shekarar (2014), a nan ƙasar ne kawai aka auka mata. Ya ce: "wannan abin da ya faru bai ɓoyun ma al'umma ba. Ashe ba su dandara ba bayan shekara guda s**a sake diran mana da nufin share kowa da kowa. Da ma manufar ke nan a waƙi'ar 25 ga watan Yulin 2014 sai ya ƙare kan mutum 34", ya nusasshe.

Dangane da masu afkawa muzaharar Ƙudus domin faranta ran Isra'iliyawa, Jagora (H) ya ce, abu ne mai sauƙi: "tunda mu muna nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Juma'ar ƙarshen watan Ramadan, sai ku ware watarana ba Juma'ar ƙarshen watan Ramadan ba sai ku goyi bayan Isra'iliyawa".

Jagora (H) ya jaddada cewa, ba za a ba mu tsoro da mutuwa ba: "ko ku yi harbi, ko kar ku yi harbi, za mu fito". Sannan ya ce, irin wannan taro, taro ne da ake tuna rayayyu da nassin Alƙur'ani. Ya ƙara da cewa: "idan aka ce an ga shahidi da ido, ba ma shakka", ya lurantar.

Jagora (H) ya ce, ko an kashe mutum ko kuma aka bar shi da rai, a ƙarshe dai zai mutu. Ya ce: "Abin alfahari ne a kashe ka a tafarkin Allah". Jagora ya nanata cewa, muna nan daram a wannan tafarki da aka kashe waɗannan shahidai. Ya ce: "muna nan daram a wannan tafarki da kuka bayar da rai a kai, ko a karrama mu, ko mu mutu a kan wannan tafarki, amma ba za mu sauya ba".

Dangane da masu kisan kai kuwa, Jagora (H) ya ce, su tuba, amma idan ba su tuba ba, za su yi hasarar duniya da lahira.

A ƙarshe, Jagora ya jaddada cewa: "wannan taro namu alama ce ta so, muna son waɗanda s**a sadaukar da rayuwarsu a wannan tafarki. Kuma kowannen mu hanƙoransa ke nan. Muna tunawa da wannan, muna ganin muna samun lada ne".

Bayan kammala jawabin, Jagora (H) ya gaisa da malamai, fastoci da sauran baƙin da aka gayyata zuwa taron, tare da iyalan Shahidai. Daga nan sai ya gudanar da ziyarar ƙaburburan Shahidan da ke kwance a Darur Rahma, sannan aka sallami al'umma.

Tun da farko, an fara taron da buɗe shi da addu'a, sannan aka yi karatun Alƙur'ani Mai Girma. Bayan haka aka gabatar da display daga lajanoni, tare da Faretin girmama Shuhada, sai kuma tamsiliyya da ta shafi waƙi'ar. Bayan kammala ziyarorin, Jagora (H) ya rufe taron da addu'a.







11/safar/1448
25th/07/2026

A Jahar Neja, Dandalin Matasa Sun Gabatar Da Daura Ilimiyya A Cikin Garin Kantagora— Daga: Baqeer M. AyubaDandalin Matas...
20/07/2026

A Jahar Neja, Dandalin Matasa Sun Gabatar Da Daura Ilimiyya A Cikin Garin Kantagora

— Daga: Baqeer M. Ayuba

Dandalin Matasan Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaƙub Zakzaky (H), na Imamul Hujjah Zone (Yankin Kontagora), sun gabatar da Daura Ilimiyya a garin Kwantagora da ke Jahar Neja, a ranar Talata, 14—07—2026, domin gyaran ruhi da kusantar Allah (S.W.T).

Malam Yahaya Ahmad Kontagora, ya gabatar da karatu a kan darasin Fiƙihu, inda ya taɓo ɓangarori da dama a cikin karatun, wanda ya fi karkata bayaninsa akan nau'ikin wanka a Musulunci da yadda ake yin su, da hukunce-hukuncen su.

A cikin jawabinsa, da ya ke magana kan sallah, ya bayyana cewar: "akwai buƙatar kowanne mumini ya dawwama wajen gabatar da salloli raka'a 51 a rana, wanda ya haɗa da sallolin farilla da kuma nafilolin da ke tsakaninsu."

A yayin darasi na biyu kan abin da ya shafi Kyawawan Dabi'u (Makarimul Akhlaƙ), ɗan'uwa Shamsudeen M. Ayuba ya ne gabatar da darasin, inda ya yi bayani dalla-dalla kan kyawawan dabi'u, ya kuma ɗauki ɓangaren munanan ɗabi'u ne ya yi bayani akai; abubuwan da ke haifar da su, da kuma illolinsu ga mutumin da ya siffantu da su.

M. Ayuba na cewa: "Mu koyi kyawawan ɗabi'u domin Manzon Allah (S.) ya ce: 'an aiko ni ne domin na cika kyakkyawar ɗabi'a'. Ya ƙara da cewa,
: 'kyakkyawar ɗabi'a wata abu ce da hatta dabba ta na son ta.'”

A gefe guda, Malam Yahaya Ahmad ya gabatar da darasi na ƙarshe, inda ya yi bayani ne a kan ilimin Aƙida (Aƙa'id).

A jawabinsa, ya ayyana abubuwan da s**a dace ɗan Adam ya riƙa tunawa domin ya kasance cikin ambaton Mahaliccinsa a kowane lokaci.

Da ya ke tsoratar da matasan game da aikita mummunar aiki, Malam ya ce: "Ranar ƙiyama Allah zai tayar da mai aikata mummunar ɗabi'a da halitta irin ta dabbar da take aiki irin wannan ɗabi'a ɗin.”

A ƙarshe, an yi Sallah da cin abinci sannan aka yi addu'a aka sallami kowa.

Youth Forum Media Team
Imamul Hujja Zone,
(Kontagora)
1 9 — 0 7 — 2 0 2 6.

BAYAN SHEKARU UKU DA KISAN WAKILIN 'YAN'UWA NA BANGI, 'YAN'UWA SUN ZIYARCI MAKWANCINSA​— Daga Khalid Haruna Bangi​A shek...
19/07/2026

BAYAN SHEKARU UKU DA KISAN WAKILIN 'YAN'UWA NA BANGI, 'YAN'UWA SUN ZIYARCI MAKWANCINSA

​— Daga Khalid Haruna Bangi

​A shekaranjiya Juma'a, 17/07/2026, 'yan'uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) na garin Bangi sun kai ziyarar ban girma zuwa makwancin Marigayi Malam Abdullahi Umar (wakilin 'yan'uwa almajiran Sayyid Zakzaky na garin Bangi), wanda ke babban makabartar garin Bangi a Jihar Neja.

​A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka cika shekaru uku (3) daidai da kisan gillar da aka yi masa. Wasu ɓata-gari ne dai s**a tabbatar da kisan nasa a yayin da ya ziyarci gonarsa da ke bayan garin Bangi.

​An shirya wannan ziyarar ce jim kaɗan bayan an tashi daga masallacin Juma'a domin tunawa da wannan rana. Daga masallacin, an nufi Markas ne domin shiryawa da kuma haɗuwa da sauran 'yan'uwa kafin a wuce zuwa makabartar.

​An hau sahu cikin tsari da nizami kamar dai yadda aka san almajiran Sayyid Zakzaky (H) da tsara al'amuransu. Bayan isar su makabartar, an gudanar da ziyarar tare da yi wa Marigayin addu'o'i, uwa-uba da sauran al'ummar Musulmi da ke kwance a wurin.

​Allah ya ƙarawa Jagora (H) lafiya da nisan kwana.

​Kontagora Media Forum

19/07/2026

MUZAHARAR ASHURA A GARIN SALKAYan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), na garin Salka da kewaye sun...
03/07/2026

MUZAHARAR ASHURA A GARIN SALKA

Yan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), na garin Salka da kewaye sun gudanar da Muzaharar Ashura a yau Juma'a 18 ga Muharram, 1448 daidai da 3—7—2026. A cikin garin Salka dake karamar hukumar Magama a jihar Neja.

Mahalarta muzaharar sunyi tafiya a cikin tsari tare da rera baitocin Juyayin Shahadar Aba Abdullah Imam Hussain (AS).

18/Muharram/ 1448
3—July—2026




Kontagora Media Forum

Hotunan| Sashen yan Traffic na Hurras da Jasaz a lokacin gudanar da Muzaharar Ashura ta gudana a garin Kontagora jihar N...
30/06/2026

Hotunan| Sashen yan Traffic na Hurras da Jasaz a lokacin gudanar da Muzaharar Ashura ta gudana a garin Kontagora jihar Neja, a ranar Juma'a 26—06—2026.

An dauki hotunan ne a lokacin da suke tsakiyar gudanar da aikin su na kiyaye ababen hawa, da kuma basu hannu a kan junction, da kuma tsallakar da masu tafiyar kafa, da kokarin ganin sun ba a samu cunkoson ababen hawa ba.

—Auwal M. Tukur
30—06—2026

Karin hotunan da baku gani ba na Muzaharar Ashura da ta gudana a garin Kontagora jihar Neja a ranar Juma'a 26—06—2026 da...
29/06/2026

Karin hotunan da baku gani ba na Muzaharar Ashura da ta gudana a garin Kontagora jihar Neja a ranar Juma'a 26—06—2026 daidai da 11/Muharram/1448.

—Auwal M. Tukur
29—06—2026.

Zaman Makokin Ashura Ranar Goma Ga Watan Muharram A Garin Kontagora.Yau Alhamis 10/muharram 1448, yan'uwa musulmi Almaji...
25/06/2026

Zaman Makokin Ashura Ranar Goma Ga Watan Muharram A Garin Kontagora.

Yau Alhamis 10/muharram 1448, yan'uwa musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Zakzaky (H) na garin Kontagora sun gabatar da salloli ziyarori tareda addu'o'i na ranar goma ga watan muharram a muhallin fudiyya dake gidan wakilin yan'uwa na garin Kontagora.

10/muharram 1448
25 June, 2026





Nusayberh Ibraheem

25/06/2026

Tattakin ashura ranar 9 ga watan muharram a garin Kontagora.

Da'irar Kontagora

Address

KONTAGORA
Kontagora

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Da'irar Kontagora posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category