Abu Huda

Abu Huda practice make perfect

Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Isa Ali Pantami ya ƙalubalanci masu da’awar cewa a baya ya ce shiga siyasa haramun ne ...
22/02/2026

Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Isa Ali Pantami ya ƙalubalanci masu da’awar cewa a baya ya ce shiga siyasa haramun ne da su kawo shaidar abin da suke iƙirarin.

Sheikh Pantami wanda ya kasance tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, ya jefa wannan ƙalubale ne bayan da ya bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar kujerar Gwamna a Jihar Gombe.

Fitaccen malamin ya yi zargin cewa yawanci mutane s**an yanko wasu maganganunsa su haɗa da wasu su yaɗa, domin cimma wani burinsu.

Pantami ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da BBC Hausa ya yi da shi, inda ya ce, ya shiga siyasa ne domin kawo shugabanci nagari a Najeriya.Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Isa Ali Pantami ya ƙalubalanci masu da’awar cewa a baya ya ce shiga siyasa haramun ne da su kawo shaidar abin da suke iƙirarin.

Sheikh Pantami wanda ya kasance tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, ya jefa wannan ƙalubale ne bayan da ya bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar kujerar Gwamna a Jihar Gombe.

Fitaccen malamin ya yi zargin cewa yawanci mutane s**an yanko wasu maganganunsa su haɗa da wasu su yaɗa, domin cimma wani burinsu.

Pantami ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da BBC Hausa ya yi da shi, inda ya ce, ya shiga siyasa ne domin kawo shugabanci nagari a Najeriya.

A zaman da ta yi a ranar Talata, majalisar ta ce aika sakamakon kai-tsaye ta laturoni zai kasance hanyar farko ta aika s...
10/02/2026

A zaman da ta yi a ranar Talata, majalisar ta ce aika sakamakon kai-tsaye ta laturoni zai kasance hanyar farko ta aika sakamakon.

Amma idan an samu matsalar intanet, INEC za ta yi amfani da takarda a rubuce wajen aika sakamakon kamar yadda aka saba yi a baya.

04/01/2026

GA IRINTA AI DAMA NASAN HAKA ZATA FARU👇👇👇

28/12/2025

A wani mataki da zai faranta ran talakawa, gwamnatin Najeriya ta sanar da dage dokar karbar haraji a farkon shekarar 2026.

Wannan mataki na nufin rage nauyin da ke kan al’umma, musamman ma waɗanda ke fama da ƙarancin kuɗi.
Masu sharhi kan tattalin arziki sun ce, wannan mataki zai ba da damar talakawa su sami ƙarin kuɗi a hannunsu, wanda zai taimaka wajen sayen abubuwan more rayuwa da kuma rage wahalarsu a rayuwa ta yau da kullum. Haka zalika, ana sa ran hakan zai karfafa kasuwanci da kananan masana’antu, domin mutane za su fi yin amfani da kuɗinsu a kasuwanni, wanda zai bunkasa tattalin arzikin ƙasa.

Duk da haka, masana suna gargadi cewa, gwamnati dole ta tanadi wasu hanyoyi na samun kudin shiga ta gaskiya, domin kada a dogara kacokan akan haraji. Idan aka yi hakan yadda ya kamata, matakin zai taimaka wajen rage radadin talauci, ya kawo zaman lafiya, sannan ya ƙara amincewar al’umma ga gwamnati.

practice make perfect

28/12/2025

Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi wata sanarwa ko hukunci daga Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) dangane da ƙorafin da ta shigar, inda take ƙalubalantar halaccin wasu ‘yan wasan Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da aka yi amfani da su a wasan tantancewa na Afirka domin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

NFF ta jaddada cewa batun na nan a ƙarƙashin bincike, kuma har yanzu FIFA na duba ƙorafin da aka gabatar, ba tare da yanke hukunci na ƙarshe ba. Ta kuma ƙara da cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin har sai an samu cikakken bayani daga FIFA.

13/12/2025

Hakuri da kaddara mai kyau ko maras kyau yana daga cikin imani

practice make perfect

AI SHIKENAN😭😭😭😭. watan mijinta 3 da rasuwa,  ga yarta kuma babu lafiya jininta ke konewa. Yarinyar tafi wata daya tana f...
05/12/2025

AI SHIKENAN😭😭😭😭.

watan mijinta 3 da rasuwa, ga yarta kuma babu lafiya jininta ke konewa.

Yarinyar tafi wata daya tana famada larura har kumbura take, saboda azabar ciwo.

Ta rasa wanda zai tallafawa rayuwarta.

Ta rasa wanda zai kai yarta asibiti.

Ita kuka, yarta kukan ciwo.

Kwananta 3 kullum sai tazo kofar gidana tana kuka.

Don Allah yaya zakaji idan wannan yar kace?

Don Allah yanzu wannan ba zalinci bane?

Ina makotansu?

Ina yan uwansu?

Ina shugabanninsu?

Ai shikenan.

DUKKANMU DAI MUTUWA ZAMUYI BAKI DAYA

Insha Allahu gobe zamu kaita asibitin da ya dace.

✍️✍️✍️✍️
SANI ROGO AIKAWA

CEO AIKAWA CHARITY FOUNDATION.

Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina ƙoƙarin tsoratarwa ko takura wa muryar Omoyele Sowore, ɗan gwagwa...
05/12/2025

Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina ƙoƙarin tsoratarwa ko takura wa muryar Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmayar demokiradiyya da ya dade yana s**ar rashin adalci a gwamnati.

A cewarsa, kowanne ɗan ƙasa ko mai goyon bayan gwamnati ne ko mai s**ar ta yana da ‘yancin faɗar albarkacin baki ba tare da tsangwama ba, muddin bai karya doka.

Ya ce ana buƙatar muryoyi masu ƙarfi irin ta Sowore domin su ci gaba da tunasar da gwamnati muhimmancin gaskiya, adalci da shugabanci nagari.

Sarkin ya ƙara da cewa, babu laifi ko kuskure idan ɗan gwagwarmaya ya nuna sha’awar zama shugaban ƙasa.

Ya ce muhimmin abu shi ne tsarin dimokuraɗiyya ya ba kowa dama, kuma ‘yan ƙasa su tantance su zaɓi wanda s**a yarda zai jagorance su cikin gaskiya da rikon amana.

Ya kammala da cewa:

“Najeriya na buƙatar muryoyi masu faɗakarwa, ba a buƙatar a toshe su. Idan Sowore yana da burin shugabanci, to tsarinmu ne ya ba shi damar yin hakan

03/12/2025

Marasa lapiya na gida da asbiti Allah ya baku lapiya

Address

No19 Tudun Makera
Kano
700252

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abu Huda posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category