30/07/2025
Gamaiyar Matasan Gaida Sun Yi Zaman Musamman Akan Cigaban Unguwar Gaida
A yau, Gamaiyar Matasan Gaida ta gudanar da wani zaman musamman domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen kawo cigaba da ci gaban rayuwa a unguwar Gaida. Taron ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da halartar matasa da dama daga sassa daban-daban na unguwar.
A cikin taron, an tattauna kan batutuwa da s**a shafi:
Hanyoyin samar da ayyukan yi ga matasa
Tsaftar muhalli da kare lafiyar jama'a
Inganta harkokin ilimi da wasanni
Haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al'umma
Shugaban gamaiyar ya bayyana cewa, "Cigaban Gaida yana hannunmu, kuma matasa sune ginshikin kowanne al'umma."
A ƙarshe, an yanke shawarar kafa kwamitoci na musamman da za su kula da aiwatar da shawarwarin da aka cimma.
Domin Jin tsare tsaren tafiyar a tuntube mutane Kamar Haka
Ibrahim Muhammad Ashfa
+234 704 543 9464
Salisu Saidu Musa
+234 706 788 2923
waheed Gaida
+234 808 190 5596