BABA RABIU MULTI Purpose

BABA RABIU MULTI Purpose Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from BABA RABIU MULTI Purpose, Grocers, 2026 Sani Mainagge A, Kano.

Wani jigo a tafiyar Pantamiyyah, Comrade Albishir, ya bayyana cewa al’ummar Gombe za su more ingantaccen tsaro da ci gab...
08/06/2026

Wani jigo a tafiyar Pantamiyyah, Comrade Albishir, ya bayyana cewa al’ummar Gombe za su more ingantaccen tsaro da ci gaba idan s**a bai wa Professor Isa Ali Pantami damar jagoranci.

A cewarsa, Pantami mutum ne da ya nuna kwarewa, gaskiya da kishin al’umma, yana mai jaddada cewa dukiya da rayukan Gwambawa za su samu kariya da kwanciyar hankali a karkashin jagorancinsa.

Comrade Albishir ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi la’akari da irin gudummawar da Pantami ya bayar a fannoni daban-daban, yana mai cewa idan aka ba shi dama, zai kawo ci gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar jama’a a fadin jihar.

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun nuna cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da dattawa kusan 50 daga kauyen Magamin Diddi da ...
08/06/2026

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun nuna cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da dattawa kusan 50 daga kauyen Magamin Diddi da ke yankin Magami/Faru a Karamar Hukumar Maradun.
Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da aka shirya wata tattaunawar sulhu da wani shugaban ’yan bindiga da ake kira Jammo, wanda ake zargin shi ne ya nemi a yi zaman sulhu bayan da wasu daga cikin mabiyansa s**a rasa rayukansu a wani farmakin jami’an tsaro.

Sai dai bayan tawagar dattawan da aka tura domin halartar ganawar ta isa wajen, ‘yan bindigar sun tsare su tare da yin garkuwa da su.

Shugaban Karamar Hukumar Maradun, , ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa dattawan sun shiga tattaunawar sulhu ne ba tare da amincewar ko sahalewar gwamnatin jihar ba.

Ya kara da cewa gwamnatin Jihar Zamfara ba ta goyon bayan duk wani yunkuri na yin sulhu kai tsaye da ’yan bindiga, yana mai jaddada bukatar bin tsarin gwamnati da hukumomin tsaro wajen duk wani matakin tattaunawa ko sulhu.

DOVE NEWS HAUSA

Mukhtar Abubakar Tafawa Balewa, ɗan marigayi Firaministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa, ya bayyana yadda ma...
08/06/2026

Mukhtar Abubakar Tafawa Balewa, ɗan marigayi Firaministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa, ya bayyana yadda mahaifinsa ya gudanar da rayuwa cikin gaskiya da riƙon amana lokacin yana mulki.

A cewarsa, marigayin bai amince a riƙa amfani da kuɗin gwamnati wajen ciyar da iyalinsa ko gudanar da harkokin gidansa ba, domin albashinsa na aiki yake amfani da shi wajen tafiyar da rayuwar iyalinsa.

MA’AIKATAR LAFIYA TA JIHAR KANOA yau, 8 ga watan Yuni, 2026, Mai Girma Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar La...
08/06/2026

MA’AIKATAR LAFIYA TA JIHAR KANO
A yau, 8 ga watan Yuni, 2026, Mai Girma Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya jagoranci wani muhimmin taron tattaunawa da jami’an Ma’aikatar Kula da Saye da Kwangiloli ta Gwamnati (Ministry of Public Procurement), domin ƙarfafa haɗin gwiwa, inganta gaskiya da riƙon amana, tare da bunƙasa kyawawan hanyoyin gudanar da harkokin saye da kwangiloli a fannin lafiya.
Taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a ƙara inganta inganci wajen samar da kayan aikin asibiti, magunguna, da sauran muhimman kayayyakin kiwon lafiya, tare da tabbatar da bin ƙa’idoji da dokokin gwamnati da s**a shafi saye da kwangiloli. Haka kuma, an jaddada muhimmancin ingantacciyar haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da isar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya cikin lokaci ga al’ummar Jihar Kano.
Mai Girma Kwamishinan ya sake tabbatar da ƙudirin Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da ƙarfafa tsarin kiwon lafiya ta hanyar gaskiya, riƙon amana, da ingantaccen amfani da albarkatun gwamnati.
Sa Hannu:
Anas Yusuf Abubakar
Mai Ba da Rahoto na Musamman, Ma’aikatar Lafiya
Ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano.

Tsohon mai bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bay...
06/06/2026

Tsohon mai bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa tsohon gwamnan na fama da matsanancin ciwon ido yayin da yake tsare a hannun hukumar ICPC.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya ce El-Rufai ya shafe sama da kwanaki 100 a tsare, yayin da hukumar ke tuhumarsa da zargin almundahanar wasu kuɗaɗen gwamnatin jihar a lokacin da yake kan mulki.

Adekeye ya zargi hukumar da tauye haƙƙin El-Rufai na samun kulawar lafiya, duk da cewa an gabatar mata da umarnin kotu da ya ba shi damar ganin likita.

Ya bayyana cewa alamun rashin lafiyar idon tsohon gwamnan sun bayyana a fili, inda ya ce idon ya kumbura tare da yin ja, amma duk da haka ba a ba shi damar samun cikakkiyar kulawar likitocin da s**a dace ba.

A cewarsa, an kai El-Rufai asibiti a ranar Alhamis, sai dai daga baya yanayin lafiyarsa ya ƙara tsananta. Ya kuma yi zargin cewa jami’an hukumar sun hana a sake kai shi asibiti ko kuma a kawo masa likita domin duba lafiyarsa.

DOVE NEWS HAUSA

04/06/2026
Duk matashin da yake da karamin jari, kuma Allah ya dora masa daukar nauyin iyayensa da kannensa... ina son ya saurari w...
25/05/2026

Duk matashin da yake da karamin jari, kuma Allah ya dora masa daukar nauyin iyayensa da kannensa... ina son ya saurari wannan sakon da kyau.

​Na san irin lissafin da kake yi a zuciyarka. Kowane karshen wata, idan ka tara 'yar riba da burin ka kara wa jarin sana'arka don ka fadada ta, sai ka samu kiran gida. Ko mahaifiyarka ba ta da lafiya, ko kudin makarantar kannenka ne s**a taso, ko kuma kawai gidan ne ya waye babu abincin da za a ci.

​Sai ka hadiye wani daci, ka dauki kudin da ka sha wahalar nema, ka tura gida. Idan ka koma daki kai kadai, sai kaji kamar kwalla za ta zubo maka. Ba don ba ka son yin hidimar ba...sai don kana ganin kamar burinka na kafa kanka yana kara yin nisa daga gare ka. Kana jin kamar kana dibar ruwa ne da kwando.

​Idan ka kalli sa'anninka, za ka ga suna canza wayoyi masu tsada, suna sayen tufafi na gani-fada, suna fadada nasu kasuwancin. Wasu ma suna yi maka kallon gaza wa ko wanda bai san yadda ake juya kudi ba. Ba su san cewa jarin da kake juyawa, shi yake daukar nauyin mutane biyar ko shida a kowace rana ba.

​Dan uwana, kada ka taba bari shaidan ya raɗa maka a zuciya cewa wannan nauyin shine yake hana ka ci gaba.

​Kasuwancin da jarin sa yake ci gaba da narkewa wajen ciyar da iyaye da tallafawa marasa karfi a gida, ba zai taba durkushewa har abada ba. Wataƙila ba za ka yi kudin dare ɗaya kamar yadda ka tsara a takarda ba... amma albarkar da take fita daga bakin mahaifiyarka a lokacin da ka kawo mata dauki, ita ce ainihin jarin da babu wata guguwar talauci ko tsadar rayuwa da za ta iya ruguza shi.

Ka ​Ci gaba da sadaukarwar nan a boye. Ka bar wa wasu gasar gudu; kai kana yin ginin da ko karni nawa zai yi, ba zai rushe ba in sha Allah.

​UMAR ALIYU DAHIRU

Address

2026 Sani Mainagge A
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BABA RABIU MULTI Purpose posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category