Ayris Onion Farm

Ayris Onion Farm Onion farming, trading, and consultant. Onion Distribution & Export.

Nasarar noma ta na farawa ne daga yadda ka fahimci bukatar abinda kake nomawa.Jama’a ku nemi ilimin noman albasa akwai a...
15/03/2026

Nasarar noma ta na farawa ne daga yadda ka fahimci bukatar abinda kake nomawa.

Jama’a ku nemi ilimin noman albasa akwai alfanu a ciki.

Barkan mu da Jumma’a babbar rana tare da fatan alkhairi
20/02/2026

Barkan mu da Jumma’a babbar rana tare da fatan alkhairi

Barkan mu da Jumma’a babbar rana tare da fatan alkhairi
23/01/2026

Barkan mu da Jumma’a babbar rana tare da fatan alkhairi

16/01/2026

Onion 🧅 Transplanting 2026

Success is not always built from the office, sometimes you must bend down and touch the soil.Onion 🧅 transplanting 2026.
14/01/2026

Success is not always built from the office, sometimes you must bend down and touch the soil.

Onion 🧅 transplanting 2026.

Buda ruwa zuwa fangali yana nufin bude kofar arziki, rayuwa da cigaba.
11/01/2026

Buda ruwa zuwa fangali yana nufin bude kofar arziki, rayuwa da cigaba.

🟢 Yau Litinin — tushen aiki!⏰ 09:00 na safeDa zarar ka yi amfani da irin albasa ta rani mai kyau, kuma dashen/ shukar ya...
24/11/2025

🟢 Yau Litinin — tushen aiki!
⏰ 09:00 na safe

Da zarar ka yi amfani da irin albasa ta rani mai kyau, kuma dashen/ shukar ya fito da ƙarfi, abin da ya rage shi ne:
ciyarwa akan lokaci, da shayarwa akan lokaci.

Za ka tabbatar komai yana tafiya daidai ne idan duk bayan kwana 7 kana ganin bambancin girman shuka a fili.

Sai mun haɗu a darasi na gaba.
Albasa alheri ce. 🌱🧅

Zaman banza shike kawo tunanin banza, har ya kai ka ga aikata aikin banza.Mukama sana'a Yan uwa.Barkan mu da hutun karsh...
21/11/2025

Zaman banza shike kawo tunanin banza, har ya kai ka ga aikata aikin banza.

Mukama sana'a Yan uwa.

Barkan mu da hutun karshen mako.

🧅 Dalilai 6 da Ya Kamata Ka Fara Noman Albasa👇👇1️⃣ Kasuwarta Bata Karewa– Albasa tana cikin kayan miya da ake amfani da ...
18/11/2025

🧅 Dalilai 6 da Ya Kamata Ka Fara Noman Albasa👇👇

1️⃣ Kasuwarta Bata Karewa– Albasa tana cikin kayan miya da ake amfani da su kullum a kowanne gida da masana’antun dafa abinci da magani da sabulu da kayan kwalliya, kasuwarta tana tafiya ko da yaushe.

2️⃣ Riba Mai Tsoka – Noman albasa yana iya bayar da riba har sau biyu zuwa sama daga abinda aka zuba na jari, musamman idan an kula da ita da kyau, Farashinta yana tashi musamman a lokacin da babu sabuwar albasa.

3️⃣ Ana Bukatarta a Kowane Sashe na Duniya
Ba kamar wasu kayan gona da ke da kasuwar yankin gida kawai ba, albasa tana da kasuwa a cikin gida da kasashen waje. Kasashe kamar Ghana, Niger, da Benin suna sayen albasa daga Najeriya a kai a kai.

4️⃣ Dacewa da Yanayi – Yanayin Najeriya musamman Arewa ya dace da noman albasa sosai, saboda suna da zafi da sanyi da kuma hasken rana mai yawa wanda albasa take bukata.

5️⃣ Za a Iya Adanawa da Sarrafawa – Ana iya busar da ita ko mayar da ita f**a don ƙarin riba.

6️⃣ Sauƙin Fara Noma – Ba ta buƙatar manyan kuɗi da fili mai yawa; kadan ya isa ka fara, tana da saukin kulawa idan ka san tsarin shuka, ban ruwa da sarrafawa.

Idan kana sha’awar fara noman albasa ko kasuwancinta ka cigaba da bibiyar wannan shafi domin ganin yadda ake aikin albasa daga farko har karshe da ikon ALLAH, da kuma koya muku dabarun yadda za ku fara noman albasa mai riba.

“A nan ne arziki ke farawa.Wannan shi ne farkon tafiyar da za ta kai mu ga noman albasar rani na shekarar 2026, In sha A...
13/11/2025

“A nan ne arziki ke farawa.

Wannan shi ne farkon tafiyar da za ta kai mu ga noman albasar rani na shekarar 2026, In sha Allah. A wannan tafiyar ne burin kamfaninmu — Ayris Onion Farm & Consulting — zai cika na zama ɗaya daga cikin manyan kamfanonin noman albasa da kasuwancinta a matakin ƙasa da ƙasa, In sha Allah.

Noman albasa dama ce ga mai hangen nesa, kuma hanya ce ta ƙarfafa tattalin arzikin aljihunsa.

Wannan lokaci ne na jajircewa, sadaukarwa, addu’a, da neman albarka da yardar Allah.

Noma shi ne ginshiƙin cigaban ƙasa, kuma manomi jarumi ne na gaskiya.

Ku biyo mu cikin wannan tafiya ta noman albasar rani — daga yafa iri har zuwa girbi — domin mu nuna muku cewa noman albasa hanya ce ta arziki, ci gaba, da yaki da talauci da zaman banza.

Ayris Onion Farm & Consulting 🌱

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ayris Onion Farm posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share