18/05/2025
"Triangle of Death" ko kuma "Danger Triangle of the Face" wato alwatikan mutuwa, wuri ne a fuska tsakanin kusurwowi uku tsakanin karan hanci zuwa leɓen sama.
Dalilin da ya sa wannan wuri ya zama mafi haɗari a fuska shi ne yadda jijiyoyin jinin da suke wannan wuri suke haɗe kai tsaye da dandazon jijiyoyin jini da suke cikin ƙwaƙwalwa.
Saboda da haka, idan aka samu wata kafa ko ƙofa da ƙwayoyin cutuka s**a shiga ta wannan wuri to suna iya kutsawa kai tsaye har zuwa cikin ƙwaƙwalwa wanda hakan kuma zai iya janyo cutukan ƙwaƙwalwa, kamar sanƙarau, da sauransu.
Bayan haka, a guji ɗabi'ar fasa ƙurjin da ya fito a cikin alwatikan mutuwa, domin hakan na iya janyo shigar ƙwayoyin cutuka zuwa ƙwaƙwalwa, a tuntuɓi likitan fata a maimakon hakan.
Bugu da ƙari, duk wani rauni ko miki a wannan wuri yana buƙatar kulawa ta musamman saboda haɗarin wurin.