19/06/2025
ZAMU CIGABA DA KAWO MUKU ABUBUWANDA KE FARUWA A YANKIN GABAS TA TSAKIYA.
Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Alhamis ya ce zai yanke shawara ko zai kai hari kan Iran cikin makonni biyu, yayin da Isra’ila da abokiyar hamayyarta a yankin ke ci gaba da musayar wuta tsawon kwanaki bakwai.
“Dangane da gaskiyar cewa akwai babbar damar a fara tattaunawa da Iran nan gaba kadan – ko za a yi ko kuma ba za a yi ba – zan yanke shawara ko zan ci gaba da wannan mataki cikin makonni biyu masu zuwa,” in ji Trump a cikin wata sanarwa da sakatariyar yada labaransa, Karoline Leavitt, ta karanta.