24/05/2026
SAKON GODIYA DAGA BABBAN MANAJAN KANO PILLARS FC👇
Ni Ahmed Musa MON Babban Manajan Kano Pillars FC, a madadin Shugaban Kulob ɗin, mambobin Hukumar Gudanarwa, masu horaswa, ‘yan wasa da kuma magoya bayanmu masu cike da ƙauna da kishin ƙungiyar, ina miƙa godiyarmu ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa yadda Ya taimaka mana muka kammala kakar gasar Najeriya ta NPFL ta 2025/2026 cikin nasara.
Duk da yadda muka fara kakar wasa cikin jinkiri da yanayi da ba mu saba da shi ba, ƙaunatacciyar ƙungiyarmu ta Kano Pillars FC ta nuna jajircewa, ƙwazo da ƙuduri wajen ci gaba da kasancewa a gasar NPFL na wata kakar wasa. Wannan nasara ba za ta samu ba face da irin goyon baya, addu’o’i da ƙarfafawar da muka samu daga al’ummar jihar Kano da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin ƙasar nan.
Ina miƙa godiya ta musamman ga manyan masu ɗaukar nauyinmu, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ci gaba da goyon baya da jajircewa wajen bunƙasa da haɓaka harkar ƙwallon ƙafa a jiharmu mai albarka. Haka kuma muna godiya ga masu ɗaukar nauyin tambarin gaban rigarmu, RFI Hausa, bisa amincewa da hangen nesa da martabar wannan babbar ƙungiya.
Haka kuma muna miƙa godiyarmu ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Jihar Kano, daukacin al’ummar ƙwallon ƙafa, magoya bayanmu masu biyayya da ƙungiyoyin magoya baya, masu ruwa da tsaki, abokan hulɗar kafafen yaɗa labarai da duk wanda ya tsaya tsayin daka tare da Sai Masu Gida a lokacin farin ciki da ƙalubalen kakar wasan.
Ga ‘yan wasanmu da masu horaswa, muna gode muku bisa sadaukarwa, jajircewa da ruhin gwagwarmaya har zuwa ƙarshe. Tafiyar ta kasance mai cike da ƙalubale, amma ƙudurinku ya tabbatar da cewa Kano Pillars FC ta ci gaba da kasancewa a inda ta dace.
Yayin da muke duban kakar wasa ta 2026/2027, ina tabbatar wa da dukkan magoya bayanmu cewa za su ga wata Kano Pillars daban kuma mafi ƙarfi. A ƙarƙashin jagorancina, za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin dawo da martaba da ɗaukakar wannan babbar ƙungiya zuwa matsayin da ta dace a cikin manyan kulob-kulob na Afirka.
Mun gode da kasancewa tare da Sai Masu Gida.
Ahmed Musa, MON, OON
Babban Manaja, Kano Pillars FC.