Masoyyan kowa

Masoyyan kowa Ya Allah kamagan cemana masalamu Ameen ya Allah

24/10/2023

🌴 FALALAR TUBA DA ISTIGFARI🌴

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Yaku mutane ku tuba zuwa ga Allah, domin lallai ni ina tuba a wuni sau ɗari".
📚 صحيح مسلم ٢٧٠٢

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Madalla ga wanda aka samu Istigfari mai yawa acikin takardarsa".
📚 صحيح ابن ماجه ٣٠٩٣

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Babu wani mutum da zai aikata wani zunubi, sannan ya tashi yayi tsarki (Alwala), sannan yayi sallah raka'a biyu, ya nemi gafarar Allah, face Allah ya gafarta masa".
📚 حديث حسن ، رواه الترمذي ٤٠٦

▪️Malamai s**a ce
"Idan mutum ya nemi gafarar Allah ya tuba gareshi, tuba ingantatta, kuma ya ciratu zuwa ga zunubi, Allah zai karɓi tubansa, kuma zai gafarta masa. Idan ya sake komawa zuwa ga zunubi sannan ya nemi gafarar Allah kuma ya tuba, tuba ingantatta kuma ya ciratu zuwa ga zunubi, Allah zai karɓi tubansa, kuma ya gafarta masa. Kamar haka, laifin zunubin da yawuce ba zai dawo ba, tare da tuba ingantatta. Allah maɗaukaki yace
(وَإِنِّي لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا ثُمَّ ٱهۡتَدَىٰ) طه ٨٢ ، وقال : (إِنَّ رَبَّكَ وَاسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ) النجم"
📓 فتاوى اللجنة الدائمة ٣١٩/٢٤

▪️Ibnul Qayyum رحمه الله yace
"Abubuwa huɗu suna jawo arziƙi: (i) Tsayuwar dare (ii) Yawaita istigfari lokacin safiya (iii) Yawaita sadaka (iv) Ambaton Allah a farkon yini da ƙarshensa".
📘زاد المعاد ٣٧٨/٤

▪️Ibn Kathir رحمه الله yace
"Duk wanda ya siffanta da siffar Istigfari Allah zai sauƙaƙa masa arziƙinsa, zai sauwaƙa masa al'amarinsa, zai kiyaye sha'aninsa da ƙarfinsa".
📙تفسير ابن كثير ٣٢٩/٤

▪️ Ibnul Qayyum رحمه الله yace
Wanda ya dauwama yana Tasbihi sirrikansa zasu warware (buƙatunsa zasu biya). Wanda ya dauwama yana Tahamidi (Godiya ga Allah) alkhairai zasu bibiyeshi. Wanda ya dauwama yana Istigfari za'a buɗe masa abubuwan da s**a kulle mashi".
📕الداء والدواء ١٨٨

▪️Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai

Yakai Ɗan-uwa mai Albarka ka yaɗa wannan saƙo, zaka samu lada. Domin lallai duk wanda yayi nuni kan aikin alkhairi kamar ya aikata ne

Allah Ka bamu ikon tuba ingataciya..🤲

21/10/2023
18/10/2023
18/10/2023

Masha Allah

16/10/2023

Masha Allah

Address

Eh Mana
Kano

Telephone

+19035096962

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masoyyan kowa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category