25/06/2026
🐔 ME YASA AKE BA KAJI ALLURAR LASOTA?
A kiwon kaji, rigakafi na daga cikin manyan sirrin samun riba. Daya daga cikin muhimman rigakafi shi ne Lasota, wanda ake amfani da shi wajen kare kaji daga cutar Newcastle Disease (Samore).
Amfanin Lasota:
✅ Kare kaji daga cutar Newcastle
✅ Rage mace-macen kaji
✅ Ƙarfafa lafiyar garken kaji
✅ Taimakawa kaji su girma cikin koshin lafiya
Lokacin Ba Da Lasota:
💉 Ana yawan ba kaji Lasota a mako na biyu zuwa na uku bisa tsarin rigakafin gonar.
Bayan An Yi Lasota:
💧 A tabbatar da kaji sun sha ruwa mai tsafta
💧 A rage damuwa (stress)
💧 A ba su multivitamin bayan rigakafi domin ƙarfafa jikinsu
Ka Tuna:
📌 Rigakafi ya fi magani sauƙi kuma ya fi araha.
Kudin rigakafi kaɗan ne idan aka kwatanta da asarar da cututtuka za su iya jawo wa manomi.
💬 Kai a gonarka, kana bin jadawalin rigakafi kuwa?
AJD Hatch & Agro Integrated Farms Ltd 📍 Panisau Rimaye Kuriwa Way
📞 09135676360 | 08134193899
"From Hatchery to Harvest"
Customers Priority is our Concern 🐔🌱