Muslims Review Hausa

  • Home
  • Muslims Review Hausa

Muslims Review Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muslims Review Hausa, kano, .

ℹ WUTAR LANTARKI A MASALLACIN ANNABI MAI DARAJA:A Shekarar 1907, Masallacin Annabi ne ya fara samun wutar lantarki ta za...
25/02/2026

ℹ WUTAR LANTARKI A MASALLACIN ANNABI MAI DARAJA:

A Shekarar 1907, Masallacin Annabi ne ya fara samun wutar lantarki ta zamani, wanda ita ce wutar lantarki ta farko da ta shiga ƙasashen larabawa, an girke masa manyan injuna guda biyu masu bashi wutar lantarki, ɗaya na aiki da gawayi, ɗaya kuma da kerosine.

A yanzu haka, fitilu sama da dubu tamanin ne (80,419) suke haskaka Masallacin Annabi Mai daraja idan duhun dare ya shiga, idan gari ya waye kuma sai a kashe na waje a rage adadin na cikin Masallacin.

Suna samun wutar lantarki ne daga manyan cibiyoyi guda biyu da suke bawa masallacin wutar lantarki, da ƙananan cibiyoyi waɗanda adadinsu ya kai goma sha ɗaya (11), tare da na'urorin daidaita wuta guda Arba'in da huɗu (Transformers: 44).

Manyan cibiyoyin guda biyu na kampanin wutar lantarkin Saudiyya ba duka lokaci ɗaya suke aiki ba, ɗaya ne yake aiki, ɗaya kuma yana jiran ko-ta-kwana, idan na farko ya samu matsala na biyun zai karɓi aikin bada wutar kai tsaye (Automatically).

Sannan idan aka ƙaddara duka cibiyoyin guda biyu sun samu matsala (ba fata ba) to akwai tasha ta uku: wacce ita kuma manyan injuna ne guda takwas aka girka masu tashi da kansu (Automatic Power Generators) waɗanda zasu iya wadata Masallacin Annabi da wutar lantarkin da yake buƙata.

Sannan idan aka ƙaddara suma injunan sun samu matsala, to akwai tasha ta huɗu, wacce ita kuma Manyan batira ne aka girke, waɗanda zasu iya bada wutar lantarki ga wurare masu muhimmanci a Masallacin Annabi.

A cikin jarrabawa ta Allah Maɗaukakin sarki, da nuna gazawar ɗan adam, duk irin tanadin nan da aka yi, a daren alhamis 13 August, 2015, wutar lantarki ta ɗauke a Masallacin Annabi na tsawon awa biyu, wanda shi ne karon farkon tun 1984 da aka haɓaka wutar, haka nan a Ranar 20 August, 2022, wutar lantarki ta ɗauke saboda tsananin iska da ruwan sama da aka yi.
Abubuwan da ke jan wuta a Masallacin Annabi suna da yawa, sun haɗa da: Fitilu, A.C, motocin zirga zirgan ma'aikata, liftoci, escalators, kayan sautin sallah

Sheik   as_sudais
24/02/2026

Sheik as_sudais

Yanda zaman tattaunawa kan yanda za'a gudanar da sallar tarawihi na wannan shekarar a harami ya kasance tareda shugaban ...
24/02/2026

Yanda zaman tattaunawa kan yanda za'a gudanar da sallar tarawihi na wannan shekarar a harami ya kasance tareda shugaban limamai Sheikh Muhammad Abdurrahman Sudai da sauran hadiman masallacin na makkah

ALLAHU AKBAR: Wannan ita ce rijiyar Bi'ir Ghars wadda Manzon Allah SAW ya sha ruwanta mai albarka sannan ya yi wanka da ...
24/02/2026

ALLAHU AKBAR: Wannan ita ce rijiyar Bi'ir Ghars wadda Manzon Allah SAW ya sha ruwanta mai albarka sannan ya yi wanka da shi, bayan nan kuma ya bar wasiyya cewa idan ya yi wafati a yi masa wanka da ruwan cikinta.

Rijiyar tana ɗaya daga cikin muhimman abubuwan tarihi da s**a shafi rayuwar Manzon Allah SAW. Rijiyar tana nan a unguwar Al-Awali, a kan titin Qurban, Kudu da masallacin Manzon Allah SAW a birnin Madina.

Allah ya ƙara wa Annabi daraja.

New} 📸 photo 📸 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️
26/11/2025

New} 📸 photo 📸 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️ 🗯️

[Quran 5:87]O you who believe! Make not unlawful the Taiyibât which Allâh has made lawful to you, and transgress not.
25/11/2025

[Quran 5:87]
O you who believe! Make not unlawful the Taiyibât which Allâh has made lawful to you, and transgress not.

13/02/2025

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muslims Review Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Grocery Store?

Share