08/03/2026
YAU NE RANAR MATA TA DUNIYA 2026
Yayin da duniya ke bikin Ranar Mata ta Duniya ta shekarar 2026, masu ruwa da tsaki sun yi kira da a kara bai wa mata dama da karfafa su, musamman mata masu buƙata ta musamman, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa da kuma gina al’umma mai karfi.
Ana gudanar da wannan biki a duk shekara a ranar 8 ga Maris, kuma a bana ya zo ne da taken “Ba da Domin Samu: Karfafa Mata Domin Samar da Duniya Mafi Alheri,” wanda ke jaddada muhimmancin hadin kai, zuba jari, da kuma kuduri wajen bunkasa hakkoki da damar mata da ‘yan mata.
Da take magana a yayin tunawa da ranar, wata Jarumar Addini da Al’adu a Jihar Kano, Bilkisu Ado Zango, ta bayyana cewa bai wa mata dama ya kamata a dauke shi a matsayin jari wanda zai ninka anfani ga al’umma, ba wai asarar albarkatu ba.
A cewarta, idan mutane, kungiyoyi da al’ummomi s**a yi niyyar tallafa wa mata, hakan yana haifar da damammaki da ke karfafa iyalai, al’ummomi da kuma ci gaban kasa baki daya.
Ta bayyana cewa taken “Ba da Domin Samu” yana nuna muhimmancin musayar anfani a tsakanin al’umma, tana mai cewa kasashen da ke fifita daidaito tsakanin maza da mata da kuma hada kowa a cikin al’umma suna samun karin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki. Ta kara da cewa bikin na shekara-shekara yana zama wata dama ta kara kaimi wajen magance matsalolin tsari da son zuciya da mata ke fuskanta a rayuwarsu ta kashin kai da kuma ta aiki.
Zango ta lura cewa mata na taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma da kuma tafiyar da ci gaba. Sai dai ta jaddada cewa mata masu nakasa s**an fuskanci karin kalubale na zamantakewa da na tsari, ciki har da wariya da kuma karancin damar samun anfani, wanda ke bukatar tsare-tsare da matakai na musamman daga gwamnati da al’umma.
Ta ce shirye-shirye irin su Faith and Cultural Champions for Healthy Women and Girls Project an tsara su ne domin magance wasu daga cikin wadannan kalubale ta hanyar wayar da kai kan harkokin lafiya da kuma inganta dabi’u masu kyau a cikin al’umma da za su anfani ‘yan mata da matasa mata.
Wannan shiri da Cibiyar Sadarwa da Tasirin Zamantakewa (CCSI) ke aiwatarwa tare da jagorancin Advisory Faith and Cultural Champions, yana da burin inganta lafiyar ‘yan mata matasa da mata kanana, ciki har da masu nakasa, a jihohin Kano da Kaduna.
A cewarta, shirin yana hada shugabannin addini da na al’adu masu daraja a cikin al’umma a matsayin Individual Faith and Cultural Champions, domin yada sakonni da dabi’u masu kyau da za su karfafa lafiyar ‘yan mata da matasa mata. Shirin yana mai da hankali kan wayar da kai kan muhimman batutuwan lafiya kamar kulawar mata masu juna biyu (antenatal care), haihuwa a cibiyoyin lafiya, da kuma tsara tazara tsakanin haihuwa.
Ta kara da cewa a halin yanzu ana gudanar da shirin a kananan hukumomi shida na Jihar Kano, wato Kano Municipal, Bunkure, Makoda, Dawakin Tofa, Takai da Madobi, inda ake gudanar da wayar da kai da kuma hada kan al’umma.
Zango ta kara bayyana cewa wani muhimmin bangare na shirin shi ne shigar da mutane masu nakasa a matsayin jakadu ko shugabanni a cikin al’ummominsu. Ta ce shirin na kokarin kawar da shinge, yakar kyama da nuna wariya, tare da tabbatar da cewa masu nakasa suna da damar da ta yi daidai wajen shiga harkokin ci gaban al’umma da kuma yanke shawara kan batutuwan lafiya.
Ta bayyana cewa Ranar Mata ta Duniya tana bayar da muhimmiyar dama domin kara bayyana muryoyin mata masu nakasa, wadanda da dama daga cikinsu har yanzu suna fama da wariya da kuma ware su a cikin al’umma.
A cewarta, al’umma mai hada kowa dole ne ta fahimci cewa mata na fuskantar kalubale ta hanyoyi daban-daban, gwargwadon yanayi kamar nakasa, al’ada, shekaru, da kuma asalin zamantakewa.
Don haka Zango ta yi kira ga gwamnatoci, shugabannin al’umma, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki da su inganta manufofin da s**a hada kowa, su karfafa tsarin tallafin al’umma ga mata da ‘yan mata, tare da kalubalantar munanan ra’ayoyi da al’adun da ke takaita damar mata wajen ba da gudummawa ga ci gaban kasa.
Ta jaddada cewa hada kowa cikin al’umma bai kamata a dauke shi a matsayin sadaka ba, sai dai a matsayin muhimmin ginshiki na daidaito da adalci.
Ta ce:
“Karfafa mata masu nakasa na nufin gane hakkokinsu, kara karfin muryoyinsu, da samar musu da damammakin da za su bunkasa rayuwarsu.”Ta kara da cewa hadin gwiwar kowa na da matukar muhimmanci wajen gina al’umma mai hada kowa da kuma adalci.
A karshe, ta bukaci al’ummomi da su yi anfani da wannan rana ta Ranar Mata ta Duniya wajen sabunta kudurinsu na tabbatar da cewa ba a bar wata mace ko yarinya a baya ba a kokarin samar da ci gaba da inganta rayuwar al’umma.