24/03/2022
Ana kin daukar daliban kasashen waje a guraban ayyuka a yankin Wales na Birtaniya saboda ba a 'aminta' da su ba kamar yadda masu neman aikin s**a bayyana.
Sherifat Abubakar, mai shekara 33, ta kashe duk kudadenta domin zuwa Wales yin digiri na biyu, amma ta gaza samun aiki a bangaren lafiya na dindindin.
Kungiyar BAME Health Support (BMHS) ta ce irin wannan ba sabon lamari ba ne, wanda a cewarta yana janyo asarar mutane masu basira a kasar.
Ministan Tattalin Arzikin kasar, Vaughan Gething ya ce har yanzu Wales na fama "wasu matsaloli."
A kididdigar shekara-shekara ta Cibiyar Higher Education Statistic (HESA) ta ce kashi 50 na daliban Birtaniya da s**a yi karatu a jami'o'in Wales su fara aiki na dindindin wata 15 bayan sun kamala digirinsu na farko.
Amma kason daliban kasashen waje kashi 34 ne.
Bambancin da ke tsakani na dalibai masu karatu digiri na biyu ne ko uku, amma kididdigar na nuna daliban da s**a kammala karatu ne kafin annobar coronavirus-ajin 2018-2019-wanda hakan ya sa ake tunanin watakila annobar ce ta kara tsananta lamarin.
'An ki daukata aiki ba tare da kwakkwaran dalili ba'
Sherifat Abubakar ta bar 'yarta tare da iyalanta a Najeriya da niyyar samar musu rayuwa mai kyau baki dayansu a Wales.