Mohammad Aliyu jamilu

Mohammad Aliyu jamilu student of politics

19/09/2025
31/08/2025
DA DUMI-DUMI: Abdullahi Rogo ya mayar da naira biliyan 1.1 zuwa asusun ICPC bayan zargin almundahanaAbdullahi Ibrahim Ro...
26/08/2025

DA DUMI-DUMI: Abdullahi Rogo ya mayar da naira biliyan 1.1 zuwa asusun ICPC bayan zargin almundahana

Abdullahi Ibrahim Rogo Daraktan Harkokin Fada na Gwamnatin Kano, ya mayar da kuɗi har ₦1,109,230,000 zuwa asusun dawo da dukiyar gwamnati na ICPC, bayan da aka zarge shi da karkatar da kuɗin gwamnati.

Hukumar ICPC da EFCC sun ce Rogo ya yi amfani da wasu kamfanoni don cire kuɗi daga asusun gwamnati ba tare da an yi wani aiki ba. An gano cewa an karkatar da ₦6.5 biliyan domin ayyukan bogi da ba a taba yi ba.

Rogo ya amsa cewa ya aikata laifin a gaban EFCC, amma daga baya ya shigar da kara a kotun jihar Kano (reshen Bichi) domin hana sake kamashi ko gurfanar da shi.

A cikin shaidar da s**a gabatar a kotu, ICPC da EFCC sun ce suna da hujjoji masu karfi da ke nuna laifin.

Wani jami’in ICPC, David Nelson Efut. ya roki kotu da ta yi watsi da karar Rogo, yana cewa:

“An shigar da karar ne da mugun nufi domin hana mu gudanar da bincike yadda doka ta ba mu dama.”

Lamarin yana kara daukar hankali a jihar Kano, inda jama’a ke jiran hukuncin da za a yanke.

C Vanguard Hausa

26/08/2025

Gwamnatin Jihar Kano ta yi shiru yayin da wasu ƙungiyoyin farar hula s**a buƙaci ta dakatar da manyan jami’abta da ake zargi da almundahana ta biliyoyin naira tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Wani rahoto na kafar yaɗa labarai ta Daily Nigerian ya bayyana cewa hukumomin ICPC da EFCC masu ya ki da almundahana sun gano badaƙalar Naira biliyan 6.5 da ake zargin Abdullahi Ibrahim Rogo, Darakta Janar na Al’amuran Kula da Baƙi a Fadar Gwamnatin Kano.

Takardun da kafar ta ambato cewa ta samu suna zargin almundahanar ta faru ne tsakanin watan Nuwambar 2023 da Fabrairun 2025 ta hanyar kwangilolin bogi da sunan kamfanonin H&M Construction Nigeria Ltd, A.Y. Maikifi Petroleum da Ammas Oil & Gas Ltd.

Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar ya ci tura, yayin da Kwamishinan Watsa Labarai, Ibrahim Wayya da Sakataran Gwamna ba su ɗauki kiran waya ba, kuma Darakta Janar na Watsa Labarai na Gwamnan, Sunusi Bature ya yi bukaguro zuwa ƙasar waje.

Wannan dambarwar na zuwa ne bayan rahoton jaridar Nigerian Tribune a watan Yuli 2025, wanda ya bayyana cewa ICPC ta kammala bincike kan badaƙalar Naira biliyan 1.02 da ake zargin jami’an Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC).

A wata sanarwa da wasu ƙungiyoyin fararen hula 20 s**a sa hannu, sun yi gargaɗi cewa zarge-zargen na iya ɓata amincewar jama’a da gwamnati, tare da sare gwiwar masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma durƙushewar da ci-gaban jihar.

“Wannan ba ƙaramin lamari ba ne. Ya nuna tsarin almundahana ta hanyar amfani da muƙaman gwamnati don amfanin kai,” in ji ƙungiyoyin.

Sun kuma buƙaci a dakatar da duk jami’an da ake zargi tare da gudanar da bincike mai zaman kansa kan dukkanin ma’aikatun gwamnati.

Haka kuma sun buƙaci Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ƙarfafa aikin sa ido tare da kafa dokar kare waɗanda ke fallasa rashawa.

“Zaɓi yana a hannunmu: ko mu yaƙi rashawa mu dawo da martabar shugabanci ko kuma mu bari ta ƙara zurfi har ta kai ga rugujewar cibiyoyinmu da makomar ’ya’yanmu,” in ji sanarwar.

Address

Tarauni By Maiduguri Road
Kano Outlying
700223

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mohammad Aliyu jamilu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category