Fadar Dangaladiman Katsina

Fadar Dangaladiman Katsina District Head Palace

Ya Allah, muna roƙonKa da Ka kawo zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a yankin Gundumar Dangaladiman Katsina, ƙ...
30/08/2026

Ya Allah, muna roƙonKa da Ka kawo zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a yankin Gundumar Dangaladiman Katsina, ƙarƙashin jagorancin Hakimin Kafur.

Ya Allah, Ka albarkaci wannan ƙasa da yalwar arziki, lafiya, ilimi da ci gaba. Ka kare al’ummarmu daga fitina, rikici, talauci da duk wani nau’in sharri.

Ya Allah, Ka haɗa zukatanmu, Ka ƙarfafa zumunci da fahimtar juna tsakanin al’ummar wannan yanki. Ka albarkaci shugabanninmu, Ka ba su hikima, adalci da ikon yi wa jama’a jagoranci nagari.

Ya Allah, Ka buɗe mana ƙofofin arziki na halal, Ka sanya albarka a cikin abin da Muke samu, Ka kuma sa yaranmu da matasanmu su zama abin alfahari ga al’umma.

Ya Allah, Ka zaunar da zaman lafiya a gundumar Dangaladiman Katsina, da kasa Baki Daya, Ka ƙara wa al’ummarmu ɗaukaka da ci gaba.

Amin Ya Rabbal Alamin.

Allah ya saka maka da AlheriKhadimul Islam
16/03/2026

Allah ya saka maka da Alheri
Khadimul Islam

Innalillahi wa Inna ilaihi rajiunAllah yayi wa Mai garin kanya Alh. Nasiru Ibrahim rasuwa a yau lahadi 1/3/2026 an gudan...
01/03/2026

Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun
Allah yayi wa Mai garin kanya Alh. Nasiru Ibrahim rasuwa a yau lahadi 1/3/2026 an gudanar da janaizar Sa da karfe 2:00 na rana a garin kanya, Allah ya jikan sa da rahma, Allah ya kyautata karshen mu.

SAKON TA’AZIYYAInna lillahi wa inna ilaihi raji’un.Cike da alhini da jimami muka samu labarin rasuwar daya daga cikin ma...
28/02/2026

SAKON TA’AZIYYA

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.

Cike da alhini da jimami muka samu labarin rasuwar daya daga cikin masu sarauta a fadar Dangaladiman Katsina, Engr. Tukur Hassan Tingilin, wanda ya rasu ranar Alhamis 26/02/2026 sakamakon hatsarin mota a kan hanyarsa daga Malumfashi zuwa Katsina.

Hakika mun yi babban rashi. Marigayin ya kasance haziki, jajirtacce, mai kishi da kishin al’umma, mai taimako, adali kuma mutumin kirki wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa addini da jama’a. Ya kasance mai taimakon matasa, mata da mabukata, yana tsayawa tsayin daka wajen ganin an tallafa wa marasa galihu.
Masarautar Dangaladima ta yi rashi babba, domin ya kasance daya daga cikin masu rike da sarauta ta Walin Dangaladima, mukami da ya rike da gaskiya, rikon amana da kwazo.

Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalai, ‘yan uwa, abokai, masarauta da daukacin al’ummar da wannan rashi ya shafa. Muna rokon Allah (SWT) Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya bai wa iyalansa da masoyansa hakurin jure wannan babban rashi.
Allah Ya kyauta bayansa, Ya maye gurbin wannan rashi da alheri.
Ameen.

Alh. Labiru Musa Kafur minWazirin Kafur
21/02/2026

Alh. Labiru Musa Kafur min
Wazirin Kafur

Fatan alheri
21/02/2026

Fatan alheri

Masha Allah
20/02/2026

Masha Allah

Address

Kofar Fada Kafur
Kafur
832103

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fadar Dangaladiman Katsina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category