Abdullahi haruna Tudun wada kd

  • Home
  • Abdullahi haruna Tudun wada kd

Abdullahi haruna Tudun wada kd Dumin fadajarwa dakuma ilimantarwa bisa tirbar iyalan gidan manzan Allah

Permanently closed.
24/01/2026
30/11/2025
Daga hussainiyya Al jawad kawo Kaduna taree DA Sheikh Abdullahi haruna Tudun wada
29/11/2025

Daga hussainiyya Al jawad kawo Kaduna taree DA Sheikh Abdullahi haruna Tudun wada

“KASHE KIRISTOCI BA JIHADI BANE!”__Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)Ta yaya za ka kashe mutum don kawai ba addininku ɗa...
03/11/2025

“KASHE KIRISTOCI BA JIHADI BANE!”

__Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Ta yaya za ka kashe mutum don kawai ba addininku ɗaya ba, ko don kuna da banbancin fahimta, sannan ka ɗauka wai jihadi kake yi? Duk wani mutumin da yake maka da’awa cewa; ɗan uwanka mutum, ko ma meye addininsa kashe shi ake yi, to ba addini yake koya maka ba, don addini ba kisan kai ba ne!

"Lokacin da Manzon Allah (S) ya zo bai samu mushirikan Larabawa suna bautar gumaka ba ne? To sai ya kashe su? Da ya kashe su da ina addinin yake? Kiransu ya yi har s**a musulunta s**a bi addinin! Manzon Allah (S) da kyawawan ɗabi’u ya yi nasara akan maqiya ba da yaqi ba! Dan haka Musulunci ba kisan kai ya koyar ba".

__Mujson Hadejiamedia Daga littafin ZANTUKAN HIKIMA Daga Fasahar Maganganun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) WallafarCibiyar Wallafa da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H) Shafi na 20

Yunƙurin haɗin Kan Malaman addinin Musulunci, Prof. Ibraheem Maqari da tawagarshi sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zak...
02/11/2025

Yunƙurin haɗin Kan Malaman addinin Musulunci, Prof. Ibraheem Maqari da tawagarshi sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yau Lahadi a gidansa dake Abuja.

Bayan gabatar da jawabai da shawarwari akan muhimmancin haɗin kai da kusantar juna tsakanin malaman addini, Jagora (H) ya ƙarfafi wannan ƙoƙari sannan yayi fatan alkhairi da samun nasara.




02/11/2025

02/11/2025
JAGORA (H) YA RUFE MU’UTAMAR DIN MEDIA FORUM A ABUJADaga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Da yammacin Asabar 10 ga Jim...
02/11/2025

JAGORA (H) YA RUFE MU’UTAMAR DIN MEDIA FORUM A ABUJA

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yammacin Asabar 10 ga Jimadal Ula, 1447 (1/11/2025) Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe Mu'utamar da Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci (Media Forum) a gidansa da ke Abuja.

Mu'utamar ɗin wanda Media Forum ta shirya na yini daya a garin Abuja, ya tattaro mahalarta daga dukkan sassan kasar nan, tare da wakilai daga bangarori daban-daban na Media din Harka Islamiyya, inda aka gabatar da jawabai akan Maudu'ai daban-daban da s**a shafi aikin jarida da Nizami Harka Islamiyya.

A yayin jawabinsa, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara da bayyana tarihin yadda al’amarin isar da sako ta hanyar ‘media’ ya faro a Harkar Musulunci da buga ‘yan takardu masu isar da sako, daga bisani aka yi yunkurin samar da Mujallar Turanci mai suna Al-Mizan a farkon shekarun 1980s, inda a farkon shekarun 1990s aka samar da jaridar Hausa ta Almizan mai falle biyu, daga baya ta rika fadada tare da tasiri mai girma dukkan sassan kasar nan.

Harwayau, Jagora ya bayyana yadda aka rika samar da Jaridun Turanci na Pointer, da Pointer Express, da kuma Mujallu irin su Mujallar Gwagwarmaya, Mujallar Mujahida da sauransu, wanda duk daga baya s**a kwanta. Inda ya dauki lokaci yana bayani akan zuwan Intanet, da yadda ya rika cigaba har zuwa ga samuwar ‘Social Media’, wanda ya kunshi rubutu, hoto, da hoto mai motsi, kuma ake amfani da shi wajen yada sakon kaitsaye a cikin lokaci, ba kamar yadda jaridun takarda suke da jinkiri ba.

Shaikh Zakzaky (H) ya ja hankalin masu bibiyan kafafen sadarwa akan su rika bashi lokacin da za su rika dubawa a kowane rana, domin kar ya rika cinye musu lokaci. Ya ce, “in ka lura da lokacin da kake ci a Social Media, za ka kuma tambayi kanka, awa nawa na yi a karatun Alkur’ani da Sallah da sauransu. Kamata ya yi kowane abu ka bashi lokacinsa, in ba haka ba sai ka bannata lokacinka, domin shi wannan abin na da cin rai.”

Ya kuma bayyana yadda Yammacin Duniya ke kokarin sarrafa kakafen, wanda dama mafi yawa mallakinsu ne. Yace, wanda ma ba nasu din ba ne, to s**an yi kokarin kutse a cikinsa don su samu cikakken daman iko da shi. Inda ya bayar da misali da yadda Tiktok ya rika fallasa ta’addancinsu, alhali suna iya ‘control’ din sauran kafafe irin su Facebook, wanda hakan yasa yanzu s**a yi kokarin sayen ‘share a Tiktok din, don su rika sa ido akan wadanda suke ‘posting’ abinda bai yi daidai da ra’ayinsu ba kamar yadda suke yi a sauran kafofin.

Jagora ya kuma jaddada muhimmancin kafafen na sadarwa, inda ya bayyana cewa sun fi kowane kafa isar da sako a yanzu, saboda su suna zuwa ga mutane ne nan take.

Ya nuna takaicinsa matuka, akan yadda ganin amfaninsa mai kyau, sai kuma makiya ke amfani mare kyau da shi wajen kirkiran farfaganda da karairayi, da kuma kirkiran rigingimu da hayaniyar da wasu da gangan suke tado maganar da za a yi ta musu da musayar raddodi, in an kammala akan wani abin saisu kara kunno wani daban. Ya ce: “Kamar wasu sun dauka idan suna surutai irin wannan ana ta zuzutasu, kamar yana daukaka sunansu ne. Suna son su yi kaurin suna ne.”

Yace: “Kar wannan masu neman su yi kaurin suna su dauke ma mutane hankali, ya kamata a yi banza da su ne, a yi kokari a gina abin kirki, wanda kuma shi ke wahala.

Jagora ya nuna takaicinsa akan yadda makiya addini ke ta kokarin sai sun baiwa ‘yan uwa Musulmi sunan kungiya, ya ce: “Tunda su sun ce su kungiya ne, wai ala dole mu ma kungiya ne. Kuma yanzu ma suna wani yayi, wai suna neman su yi kungiya, su ce wai har da mu a ciki. Nace haba! Ai linzami ya fi karfin bakin kaza! wani bai isa ya ce ya yi kungiya ya saka mu a ciki ba, mu mun wuce nan! Ba dai akan addinin nan ba.

“Mutane yanzu kowane na ta fito da wani abu, wai mu kungiya ce. Wa ya ce maka? Mu mun ce muna addini ne, mu muke ‘representing’ din addinin. Amma sai s**a ce wai har da kungiyar kaza, wai kungiyar Mazhaba. A kafafen watsa labaru, wai kungiyar Mazhabar Shi’a, ko ‘yan Shi’a, ko kaza. Wai ala dole, tunda su sun yi kungiya, to ku ma kungiya ne. To ku kuke da kungiya, mu muna addini ne, mu bamu da wata kungiya, mu abinda muke yi sunansa addini ne. Ku ku yi ta kungiyoyinku!” Inji Shaikh Zakzaky (H).

Ya kara da cewa: “Na’am, ku kungiya ne, amma mu ba kungiya ba ne, ba kuma za mu taba zama kungiya ba. Ba kuma za a taba saka mu a cikin kungiya ba. Mu addini muke yi. Addinin Musulunci. Tun farko bamu taba ce muku addinin Musuluncin kuma ya kasu kashi-kashi ba, ba mu taba ganinsa a kashi-kashi ba, mu mun san addinin Musulunci bai kasu kashi-kashi ba! Abu daya ne rak! Sakon da Manzon nan ya zo da shi daga wajen Allah. Illa-iyaka, zance ya kare.”

Harwayau, Jagora ya ja hankali akan kokarin gina Fikira Sahihiya na sanar da mutane mene ne addini a hakikarsa, da kuma yunkurin dawo da ikonsa ya tabbata daram a doron kasa, wanda yace makiya kan kasa fahimtarsa, su yi ta masa fassara daban-daban.

Ya bayyana yadda Alkur’ani ya kawo tarihin Annabawa da s**a zo s**a kirayi al’ummarsu daban-daban, yace sam ba a kan kungiya ko mulki ko sarauta suke ginawa da’awarsu ba. “Ana ce mutane su zo su bauta ma Allah a bisa ka’idar da aka saukar ne, abinda ake ce ma mutane kenan. Ba an ce musu su zo su shiga wata kungiya ne ba.”

Yace: “To mu ma mukan ce, tunda mun yi sa’a mu dama al’ummar Musulmi ne, abinda muke cewa, al’ummar ta dawo bisa addininta. Illa iyaka. Amma sai s**a ce ku kaza ne.”

Jagora ya ja hankali akan kar mu daka ta mutane wajen amsa sunan ‘yan kaza da suke saka ma mutane. Ya bukaci “a dora mutane ne akan Fikira Sahihiya na cewa, addini ake yunkurin tabbatarwa, addinin nan kuma sunansa Al-Islam, shi kuma Al-Islam din nan ‘shaamil’ ne, karkashinsa ne aka sami fahimta daban-daban. Fahimta daban-daban ba addinai ne daban-daban ba, fahimtar shi wannan addinin ne. Kuma ana batun in addinin ya kafu, to shi zai tafi ne bisa shi ka’idan addinin, ba son ran wani ba, ba fahimtar wani ba.”

Jagora ya jadda jan hankalin ‘yan uwa akan kar su bari a rika shagaltar da su da wasu abubuwan da ba shi ke gabansu ba. “Na san wasu janibobi da s**an fada tarko, in an zage su su yi zagi, ka ga an yi batsattsale a ciki. Kuma abinda wadancan suke so kenan. To kai kar ka yarda a kautar da kai daga abinda kake kai. Ka yi ta fadan abinda yake shi ne daidai. Mai zagi ya yi ta zage-zagensa, kai kuma ka yi ta yi, in ka daka tasa, za ka koma ne ka zama kana bashi amsa, kuma abinda yake so kenan. To mu kar mu daka tasu, ya zama kullum kokarin kwakkwafa mutane akan abinda yake shi ne daidai, da kuma tsayawa kyam, da yi domin Allah, yi don Allah, yi don Allah, insha Allah.”

Ya karkare jawabinsa da nasiha kamar yadda ya saba akan yin komai saboda Allah. Ya ce: “Ana yi ne saboda Allah. Yi don Allah, yi don Allah, yi don Allah, ba don ka yi suna ba. Kuma in ana tare ana aiki kar ka dauka kowa zai ba da hadin kai a yi lafiya lau a tafi, a’a dabi’an mutum ne, in aka tara mutane, sai an ji abubuwa, sai an ce, wannan shi ya yi kane-kane, ko kuwa wannan dan bani na iya, wancan in ba shi aka ce ba rigima za a yi. Wannan an dinga yi kenan, dama dan Adam ba a raba shi da wadannan abubuwan. Kai dai ka yi abinka kawai, in kana yi saboda Allah ne. In kana yi saboda mutane ne, sai ka bari in dominsu ne, amma in kana yi domin Allah ne sai ka yi.”

A karshe, Jagora ya rufe da addu’ar, Allah Ya ba mu ladan abubuwan da muke yi, kuma ya kai mu ga kyakkyawan natija.





01/11/2025

ISLAMIC MOVEMENT  NIGERIA REFUTES  FALSE CLAIMS OF CHRISTIAN  GENOCIDEThe Islamic Movement in Nigeria, under the leaders...
01/11/2025

ISLAMIC MOVEMENT NIGERIA REFUTES FALSE CLAIMS OF CHRISTIAN GENOCIDE

The Islamic Movement in Nigeria, under the leadership of Sheikh Ibraheem Zakzaky, has always stood firmly for peaceful coexistence, justice, and unity among all Nigerians, irrespective of religion, ethnicity, or political leaning. The Movement regards Islam and Christianity as two great faiths of divine origin that call humanity to righteousness, compassion, and justice. It believes that both Muslims and Christians have far more in common in their moral teachings than in the superficial differences that have been exploited for selfish political ends.
At the heart of the Movement’s message is the conviction that Nigeria’s crisis is not religious but moral and political it is a crisis born of corruption, greed, and a deliberate manipulation of the masses by a morally bankrupt elite. While Muslims and Christians are often incited to hate and suspect each other, the real enemies of the nation are those who plunder its resources and perpetuate injustice but remain united in their corruption. As Sheikh Ibraheem Zakzaky has repeatedly declared, “The poor Christian and the poor Muslim have no conflict; their common enemy is the unjust system that enslaves them both.”
It is against this backdrop that the Islamic Movement views with deep concern and disapproval the recent allegations by U.S. President Donald J. Trump, who accused the Nigerian government of allowing or supporting “genocide against Christians,” and threatened to redesignate Nigeria as a “Country of Particular Concern.” Trump’s claims, echoed by a few pro-war voices in the U.S. Congress, suggest that “radical Islamists” are carrying out “mass slaughter” of Christians in Nigeria, and that U.S. troops might be deployed to protect them.
The Islamic Movement in Nigeria categorically rejects these allegations as false, inflammatory, and dangerous, describing them as a continuation of Western propaganda designed to sow discord and justify foreign interference in African affairs. Such sweeping and unfounded accusations ignore the complex socio-political realities of Nigeria and reduce its multifaceted challenges to a simplistic and divisive religious narrative.
In reality, both Muslims and Christians have been victims of insecurity, banditry, terrorism, and government repression in equal measure. Villages in the predominantly Muslim North have been wiped out by armed groups just as churches and Christian communities have suffered attacks elsewhere. These tragedies are not the result of an Islamic war against Christianity, but the consequence of a failed political order that thrives on corruption, poverty, injustice, and impunity.
The Islamic Movement finds it deeply hypocritical that Western politicians who have supported wars, occupations, and bombings in Muslim countries, killing millions of innocent people now pretend to be defenders of human rights and religious freedom in Africa. The Movement believes that the so-called concern for Christians in Nigeria is not born out of compassion, but out of a geopolitical agenda to divide Nigerians, weaken their unity, and pave the way for foreign manipulation of the nation’s resources and policies.
Supporting this position, the Nigerian government itself, through a statement by Kimiebi Imomotimi Ebienfa, spokesperson for the Ministry of Foreign Affairs, has rejected the U.S. President’s claims, affirming that “Nigerians of all faiths have long lived, worked, and worshipped peacefully.” The government reaffirmed its commitment to “fighting terrorism, strengthening interfaith harmony, and protecting the lives and rights of all its people.” The Islamic Movement welcomes this official stance and urges the government to complement words with sincere action by ensuring justice, fairness, and equity across the nation. These are conditions which are indispensable for genuine peace.
The Islamic Movement in Nigeria further warns that foreign powers have historically used religion as a weapon to destabilize nations and create excuses for intervention. The labeling of Nigerian Muslims as “radical Islamists” is part of a long-standing Western narrative that equates Islam with violence and demonizes Muslim communities globally. This narrative not only misrepresents Islam but also endangers interfaith relations, as it fosters suspicion, fear, and hostility among ordinary citizens who have lived peacefully side by side for centuries.
For decades, the Movement has worked tirelessly to promote interfaith dialogue and mutual respect. Its members have visited churches during Christmas and Easter, and Christian leaders have been received at Islamic Movement gatherings in gestures of brotherhood and solidarity. The Movement has condemned every attack on churches, just as it has condemned attacks on mosques and processions. Its guiding principle remains that any attack on innocent lives, regardless of religion, is an attack on humanity and a violation of divine law.
The Movement continues to stress that true peace cannot exist without justice. Nigeria’s leaders must abandon the politics of deceit and division and focus on eradicating corruption, poverty, and insecurity. The people must realize that religious conflict serves only the interests of those who loot public funds and exploit national disunity. When the masses are divided, the corrupt elite remain secure in their power; when the masses unite, tyranny crumbles.
In conclusion, the Islamic Movement in Nigeria calls on both Muslims and Christians to reject the poisonous narratives being promoted by foreign powers and local opportunists. Nigerians must refuse to be pawns in the game of global politics. Instead, they should draw strength from their shared faith in God, their common suffering under bad governance, and their collective hope for a just and peaceful nation.
The Movement’s message is clear: our unity as Nigerians is stronger than the falsehoods that seek to divide us. The real war is not between Christians and Muslims, rather it is between truth and falsehood, justice and corruption, sincerity and deceit. And until we unite to confront that reality, the cycle of manipulation will continue. The Islamic Movement stands firmly for peace, justice, and unity, rejecting every attempt be it foreign or local to turn Nigerians against one another in the name of religion.

's Newroom
free
Palastine

for palastine
Ibraheem


Professor Abdullahi Danladi
Resource Forum
Islamic Movement Nigeria

Address

Ecbogha Cricent Shi A Clus

Telephone

+2348101771565

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdullahi haruna Tudun wada kd posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abdullahi haruna Tudun wada kd:

  • Want your business to be the top-listed Grocery Store?

Share