22/10/2025
FAƊAKARWA
Bismillahir Rahamanir Raheem.
A 'yan kwanakin nan, wasu da muke kyautata zaton 'yan uwa ne, kuma masu kyakkyawar nufi, suna amfani da fasahar' Artificial intelligence (AI)' suna ƙirƙiran hotuna iri daban-daban, suna yaɗawa a kafafen sadarwa.
Hotunan na ɗauke da wasu alamomin Harka Islamiyya, k**ar hoton Jagora (H) a cikin wasu gurare, irin su dakin gwaje-gwaje, ko dakin yaƙi, ko filin daga da sauransu. Ko kuma su kirkiri hoton wasu mutane su saka musu kayan soja, suna tirenin a wani waje, tare da sanya musu Logo din Harisawa. Ko kuma canzawa hoton Jagora (H) fasali, zuwa wani abu mai k**a da wargi da wasa, tare da sanya Logo din Ofishin Jagora a jikin hoton, sai ya zama k**ar Ofis din ne ya fitar da hoton a haka.
Lallai wadannan ayyukan ba abu ne kyakkyawa ba, ba kuma sunansa cigaba ba, abu ne wanda yake da illa, k**a daga rashin wayewa, da mayar da Jagora (H) ko Harka Islamiyya a matsayin wasa da wargi a idon duniya, zuwa baiwa maƙiya iri daban-daban kafar cutar da Harka ta fuskoki daban-daban yanzu ko nan gaba.
Bisa haka, muna kira ga 'yan uwa da suke yin irin wannan, su bari. Waɗanda s**a yi a baya, su goge a shafukansu. Har ya zama in an ga wani ya cigaba ƙirƙira ko yaɗa irin waɗannan zanen, an san cewa da wata mummunar manufa yake yin hakan a nan gaba, kuma 'yan uwa ba za su biye masa ba.
Muna fatan Matasan Harka Islamiyya, - ma'abota basira da sadaukarwa - za su duƙufa wajen binciken hanyoyin samar da cigaba na haƙiƙa ga tafarkin gwagwarmaya, ba tare da shagaltuwa da abubuwan da s**a fi k**a da wasa ba.
H-Central.
— Hurrasul Harakatil Islamiyya
29/4/1447 / 22/10/2025