26/04/2026
Zuma Charity Foundation
Zuma Charity Foundation na miƙa saƙon jinjina, godiya, girmamawa da kuma ƙarfafa gwiwa ga dukkan waɗanda s**a tallafa da kuɗi da kayan abinci har aka samu nasarar kammala rabon abincin watan Ramadan da ya gabata na shekarar 1447/2026 cikin nasara.
Muna masu miƙa godiya ta musamman ga waɗannan mutane da s**a bayar da gudummawa mai ƙarfi wajen ganin wannan aiki ya gudana cikin nasara:
📌Alh. Lawal Yusuf (A.L.Y)
📌Alh. Maitala Malikanci.
📌Sir Abdulhadi Abdullahi
📌Dr. Haruna Sale Kargi
📌Hon. Dr. Hamza Ibrahim Ikara
📌Dr. Kabir Emergency
📌Alh. Ibrahim Bature
📌Hon. Abba Sayasaya
📌Hon. Ahmad Bello Marafa
Hakika gudummawarku ta taimaka matuƙa wajen tallafawa masu buƙata, kuma Allah kaɗai ne zai iya saka muku da alheri.
Sannan wayanda s**a tura abinda Allah ya h**e musu k**a daga Dari biyar dubu daya da masu Aiko mana da qananan abubuwa daidai qarfinsu Allah ya Saka muku da Alkhairi yasa a mizani.
Haka nan muna jan hankalin sauran al’umma da su ƙara himma wajen bada gudummawa, domin ciyar da mai azumi na da matuƙar muhimmanci, ba kawai a watan Ramadan ba har ma bayan watan.
Har ila yau, muna sanar da al’umma cewa wannan foundation tana aiki ne kaɗai lokacin watan azumi, amma muna da wasu shirye-shirye a ƙasa wanda in Allah Ya Tabbatar zamu gabatar da su domin cigaban al'umma.
A ƙarshe, muna yi wa kowa fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya zaunar da ƙasarmu lafiya, Ya kawo ci gaba da zaman lafiya mai ɗorewa. Ameen. 🤲
Ayuba Kabiru
Public Relations Officer
Zuma Charity Foundation
Zainab Sani Labaran
Founder/C.E.O
Zuma Charity Foundation