AREWA POST TV

AREWA POST TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AREWA POST TV, Grocers, Tudun Wada Gusau, Gusau.

Innā lillāhi wa innā ilayhi rājiʿūn. Wallahi, duniya ta yi babban rashin; Allah ya yi ma Shehu Usman rigirigi na Annabi ...
02/02/2026

Innā lillāhi wa innā ilayhi rājiʿūn. Wallahi, duniya ta yi babban rashin; Allah ya yi ma Shehu Usman rigirigi na Annabi Muhammad S.A.W. rasuwa cikin wannan dare. Jana’iza karfe hudu da rabi (4:30 PM) a filin Locos, wajen da yake yin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W. gobe Litinin, Allah ya yi masa rahama, alfarmar Annabi Muhammad S.A.W. Amin.
Daga Alhaji Nasiru Akilu Kusfa.

Majiya :--- Tijjaniya Online.

Kuyi Following Domin Kasancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 32 a wani hari da ta kai kan gidaje,da tantuna.Hukumar Tsaron Farar Hula a yankin Gaza a w...
01/02/2026

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 32 a wani hari da ta kai kan gidaje,da tantuna.

Hukumar Tsaron Farar Hula a yankin Gaza a wata sanarwa da ta fitar ta na mai bayyana mutuwar mutane galibin su mata da yara 32

bayan wani hari da Isra’ila ta kai a yankin Gaza, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da aka cimma tsakanin bangaroirin biyu.

Majiya Rfi Hausa.

Kuyi Following Domin Kasancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

An K**a Wasu Ma’aurata Bisa Zargin Yi Garkuwa Da Kansu, Tare Da Karɓar Naira Miliyan 10 Matsayin Kudin Fansa.Binciken Ma...
31/01/2026

An K**a Wasu Ma’aurata Bisa Zargin Yi Garkuwa Da Kansu, Tare Da Karɓar Naira Miliyan 10 Matsayin Kudin Fansa.

Binciken Manema Labarai ya gano cewa ma’auratan, masu suna Fred da Goodness, sun ƙirƙiri labarin sacewar a ranar 7 ga watan Janairu domin neman kuɗi ga mijin, wanda ya yi niyyar komawa Amurka saboda rashin tallafin kuɗi.

‎Wani jami’in ’yan sanda da ya yi magana da Jaridar a ranar Alhamis ya ce ma’auratan sun tuntubi ’yan uwa daga danginsu, suna ikirarin cewa an sace su tare da neman kudin fansa.

Dangin sun tattara Naira miliyan 10 cikin kwana uku, suna zaton kuɗin zai taimaka wajen kubutar da su.

Jami’in ya ce ma’auratan sun tsara wurin karɓar kuɗin a wata makaranta da ke Cappa, Mushin.

“Jami’an da ke sa ido sun lura da matar ta shiga wurin ita kaɗai, daga baya mijin ya iso. Amma an fara zargin su bayan sun fito tare da jakar kuɗi. An bincika jakar, aka gano kudin fansa, nan take aka k**a su,” in ji shi.

Matar ta bayyana cewa ita ce ta shawarci mijinta su kitsa wannan shiri.

Tuni dai aka mika su ga ’yan sanda, inda bincike ya tabbatar da cewa su s**a kitsa garkuwar da kansu.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Abimbola Addebisi, ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

----Majiya Inda Ranka Freedom Fm Kano----

Kuyi Following Domin Kasancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

31/01/2026
BABBAN LABARI:----    Majalisar ƙoli kan harkokin Shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake sabunta kiran da ta yi na...
30/01/2026

BABBAN LABARI:----

Majalisar ƙoli kan harkokin Shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake sabunta kiran da ta yi na a tsige Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar (INEC), Joash Amupitan, gabanin babban zaɓen 2027, inda ta bayyana shi a matsayin barazana ga amincin tsarin dimokraɗiyyar Najeriya.

A wata hira da ya yi da BBC, shugaban majalisar, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya bayyana matsayarta kan shugban hukumar inda ya yi gargadin cewa Musulmin Najeriya ba za su amince ko halasta duk wani sak**akon zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Amupitan ba.

Sheikh Umar ya ce matsayar majalisar ta samo asali ne a kan abin da ta bayyana a matsayin abubuwan da shugaban hukumar ta INEC ya aikata a baya, musamman ma wani takaitaccen bayani na shari'a da ake zargin ya rubuta wanda ke nuna cewa ya amince da batun cewa ana yi wa Kirista kisan kiyashi a Najeriya – ikirarin da gwamnatin tarayya ta sha yin watsi da shi.

''Har yanzu muna kan bakarmu, saboda shi shugaban hukumar zaɓe bai fito ya musanta cewa wannan abun ba haka ba ne. Ya na nan kan iƙirarinsa, bai ma ga cewa wannan wani abu ne da zai fito ya yi magana a kai ba,'' in ji shi Sheikh Umar.

Majiya:-- BBC Hausa

Kuyi Following Domin Kasancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

GWAMNA LAWAL YA FARA TATTAUNAWA A FADIN JIHAR ZAMFARA DA MASU RUWAN JAM’IYYAR PDPGwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ...
27/01/2026

GWAMNA LAWAL YA FARA TATTAUNAWA A FADIN JIHAR ZAMFARA DA MASU RUWAN JAM’IYYAR PDP

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya fara tattaunawa a fadin jihar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Zamfara.

An fara wannan taron masu ruwa da tsaki ne a ranar Talata a Rescue Hall da ke Gidan Gwamnati, Gusau.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa wannan tattaunawa ta masu ruwa da tsaki taro ne na yau da kullum da ake yi domin tsara dabaru da kuma tattauna al’amuran da s**a shafi jam’iyya da kuma jihar baki ɗaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa jerin tarukan na farko sun fara ne da masu ruwa da tsaki daga Kananan Hukumomin Gummi da Maru.
“Wannan tattaunawa tana ba da dama ga gwamna ya tattauna muhimman batutuwan siyasa da ke tasiri ga jam’iyya da kuma jihar.
“A cikin makonni masu zuwa, Gwamna Lawal zai karɓi baƙuncin masu ruwa da tsaki na PDP daga dukkan kananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.

“A yayin tarukan, Gwamna Lawal yana sauraron damuwar masu ruwa da tsaki, shawarwarinsu, da kuma nazari mai zurfi kan halin da al’ummominsu ke ciki.
“Irin wannan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na nuna cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ci gaba da kasancewa jam’iyya mai ƙarfi da tasiri a fadin jihar.”

Majiya:-----

SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
27 ga Janairu, 2026

Kuyi Following Domin Kasancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

BABBAN LABARI A BANGAREN YADA LABARAIMajalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara ta amince da kashe naira biliyan 3.6 domin sabu...
26/01/2026

BABBAN LABARI A BANGAREN YADA LABARAI

Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara ta amince da kashe naira biliyan 3.6 domin sabuntawa da sake kayan aikin Gidan Rediyon AM na Jihar Zamfara.

An yanke wannan shawara ne a zaman majalisar da Mai Girma Gwamna Dauda Lawal ya jagoranta a Gusau, da nufin zamanantar da kafafen yaɗa labaran gwamnati da kuma inganta isar da sahihin bayani ga al’umma.

An ba kamfanin ECALPEMOS Technologies aikin, wanda ya ƙunshi samarwa da girka sabbin kayan aikin watsa shirye-shirye na zamani cikin kwanaki 90.

Ana sa ran wannan sabuntawar za ta inganta ƙarfin sigina, ingancin watsa shirye-shirye, da kuma bai wa jama’a—musamman ma mutanen karkara—damar samun sahihan bayanai, tare da tallafa wa sadarwar gwamnati, gaskiya a mulki, da bunƙasar tattalin arziki da zamantakewa.

Kuyi Following Domin Kasancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

25/01/2026

Musician/band

Gwamnatin Sokoto za ta haramta 'almubazzaranci' yayin aure a jihar.Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ce gwamnatina za ...
25/01/2026

Gwamnatin Sokoto za ta haramta 'almubazzaranci' yayin aure a jihar.

Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ce gwamnatina za ta gabatar da dokokin haramta abin da ya kira almubazzaranci a lokacin aure a faɗin jihar.

Ahmad Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin ƙaddamar da masallaci da mak**arantar zawiyyar Sheikh Aliyu Bunza da aka sabunta.

''Matakin ya zama wajibi saboda aydda ake samun ƙaruwar wahalhalun da ake ɗorawa mutanen da ke shirin yin aure ta hanyar tsara abubuwan da ba za zama wajibi ba, lamarin da ya sa matasa maza da mata da s**a isa aure ke shan wahalar yin aure'', in ji gwamnan.

Gwamnan ya ce waɗannan wahalhalu na taimaka wa wajen ƙaruwar yawan marasa aure maza da mata a jihar.

''Wanda kuma hakan ke taimakawa wajen ƙaruwar rashin tarbiyya tsakanin matasa, waɗanda s**a gaza yin aure saboda tsadar buƙatun da ake gabatarwa gabanin auren'', in ji gwamnan.

Matakin na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan wani bidiyon wata yarinya a jihar ya ɓulla da aka yi wa kayan lefe na gomman akwatina da motar hawa, lamarin da ya janye ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.Gwamnatin Sokoto za ta haramta 'almubazzaranci' yayin aure a jihar.

Kuyi Following Domin Kancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

Source:-- BBC Hausa

Mata da yara na daga cikin wandada s**a fi fuskantar cin zarafi a yaƙin SudanMata na daga cikin wadanda aka fi cin zaraf...
25/01/2026

Mata da yara na daga cikin wandada s**a fi fuskantar cin zarafi a yaƙin Sudan
Mata na daga cikin wadanda aka fi cin zarafinsu a yaƙin Sudan, inda suke fuskantar cin zarafi da sauran laifukan da aka aikata ba tare da an hukunta masu aikata hakan ba, in ji Sulaima Ishaq al-Khalifa wata mai fafutukar kare hakkin bil'Adama wacce ta zama ministar harkokin zamantakewa ta gwamnatin da ke samun goyon bayan sojojin Sudan.

Source. Rfi Hausa

Kuyi Following Domin Kancewa Tare Damu Arewa Post tv Tsintsiya Daya. 07065517311

Address

Tudun Wada Gusau
Gusau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA POST TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category