22/03/2026
Iran Ta Yaudari Duniya
Akwai wani mataki da yaƙi yake kaiwa ta yadda harsashi zai zama ba shi ne babban makami ba. Rudarwa (Deception) ita ce zata zama takobi, ruda tunanin makiyi.
Har yanzu kana kallon labarai Amma idan kana gaskata duk abin da ka gani, to lallai baka fara nazarin yadda duniyar 2026 take juya tunani ba.
Maganar mutuwar Ayatollah da sauran shugabannin Iran ba batu ne na inason nasan asalin gaskiyar ba ne; magana ce ta zamba da dabarar yaƙin da aka shirya wa tsawon shekaru 40.
Ta yaya ƙasar da take da biranen makamai a ƙarƙashin ƙasa (Underground Missile Cities), waɗanda satellite mafi ƙarfi ma ya gaza gano su, za ta kasa kare mutum ɗaya? Iran ba iya ƙasa ce kawai ba; tsari ne (System) da aka gina akan rukunai uku; Addini (Martyrdom), Sojoji (Revolutionary Guard), da kuma Ilimin Injiniyanci (Technology).
Babban abin da ya kamata ka tambayi kanka shi ne: Me ya sa har yanzu ba a binne Ayatollah ba? A al’adar Musulunci, mutum baya wuce sa’o’i 24 zuwa 72 ba a binne shi ba, amma ga shi yau mun kusa kwashe wata guda ana tura ranar jana’iza. Idan har shugabannin soji irin su Ali Larijani za su iya yawo a kan t**i ranar Juma’a suna nuna wa duniya cewa ba sa tsoro, me zai hana su binne jagoransu?
A nan ne dabarar Strategic Disappearance ta shigo ciki. Ta hanyar barin duniya ta yi amanna cewa ya mutu, Iran ta cire babban Target ɗin da Isra'ila take nema. Sun ɓoye shi a cikin rami mai zurfi (Bunker) inda babu na'urar da za ta iya gano numfashinsa, don ya ci gaba da juya yaƙin cikin kwanciyar hankali yayin da maƙiyi yake murnar nasarar ƙarya.
Wani sirrin kuma yana ga yadda Iran take amfani da Martyrdom (Shahada). Kamar yadda tarihin Annabi Isa (A.S) ya nuna, jinin jagora baya zama asara; yana zama makamashi ne da yake ninka ƙarfin mabiya.
Amma lissafin ya ruguje a nan. Idan har Ayatollah ya zaɓi ya mutu a ofishinsa kamar yadda ake faɗa, me ya sa zai tafi da jikoki da matasa? A ilimin yaƙin kwakwalwa, ba a kashe matasa don Symbolism; A cikin tafiyar da ta ginu akan akida, babban burin tsoho (jagora) shi ne ya tabbatar da cewa ya gina matasa waɗanda za su ci gaba da jan ragamar tafiyar. Yin shahada ko mutuwa ga tsoho ba rashi ba ne; hanya ce ta ba wa matasa dama su fito fili su nuna ƙwazonsu, yayin da suke amfani da hasken (ilimi da akida) da tsohon ya bari.
Wannan yana nuna cewa dukkan labarin an tsara shi ne don a yaudari na'urorin leƙen asiri na Yamma. Kalli abin da ya faru da Ahmadinejad da janar-janar ɗin da aka ce an kashe a yaƙin kwanaki 12; kashi 75% na waɗanda aka ce sun mutu sun dawo a raye suna dariya. Wannan ba yaƙin makami ba ne; yaƙi ne na Ghosting, zama fatalwa a idon maƙiyi.
Iran ta nuna cewa ta fi son ta bugi tattalin arziƙin Amurka da kawayenta (Financial Leverage) maimakon nutsar da jiragen ruwansu, don gudun kada talakawan Amurka su fusata su shigo yaƙin. Wannan hikima ce ta Asymmetric Warfare (wato Yaƙi ne na rashin daidaiton ƙarfi).
Sun san cewa idan s**a nutsar da jirgin Abraham Lincoln, za su janyo wa kansu harin nukiliya. Don haka s**a zaɓi su bugi aljihun duniya (Oil refineries & Hormuz Strait). Suna da makaman da za su iya harba wa tsawon watanni shida ba kakkautawa, kuma suna jiran maƙiyi ya shigo gidansu ne don su nuna masa asalin Hypersonic Trap.
Idan baka zama babban mai nazari (Analyst) ba, to za ka zama abincin farfaganda. Kada ka nemi Victory a cikin labaran TV; nemi gaskiya a cikin abubuwan da ba a cika faɗa ba. Gaskiya tana ɓoye a cikin wannan shirun, kuma Iran ta gwanance wajen tayi wannan shiru mai sautin ruguji.
Bayan wannan hawan jinin ya lafa, duniya za ta ga Rayayyun Matattu waɗanda aka ce sun mutu sun fito daga ƙarƙashin ƙasa suna mulkar sabuwar duniya. Domin a yaƙi, wani lokacin mutuwa ita ce hanya ɗaya tilo ta ci gaba da rayuwa.
Shin kana ganin lallai Iran tana da ikon yaudarar duniya na tsawon wannan lokacin, ko kuwa dai muna witnessing ɗin ƙarshen wani zamani ne?