Zamfara Reporters

Zamfara Reporters Zamfara State home of farming and natural resources

Kalaman Sani Shinkafi ga Matawalle cike suke da hassada da bakin ciki.Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta jihar Zamfara ta...
26/10/2025

Kalaman Sani Shinkafi ga Matawalle cike suke da hassada da bakin ciki.

Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta jihar Zamfara ta bayyana cewa kalaman da Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya yi kan Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr. Bello Muhammad Matawalle (MON), sun samo asali ne daga hassada da jin zafi da bakin ciki saboda rasa tasiri a siyasar jihar.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce ta damu da irin yadda Shinkafi ke fitowa da maganganu marasa kan gado, inda take siffanta shi a matsayin mutum ma ci amana, hassada da neman suna ta kowace hanya. Kungiyar ta ce duk da irin taimakon da Matawalle ya yi masa a baya, yanzu kuma ba abin da zai saka masa da shi sai s**a da kazafi.

Kungiyar ta bayyana cewa kafin Matawalle ya zama gwamna a 2019, Dr Shinkafi ba shi da wani tasiri a siyasa, domin ko a mazaba bai taɓa lashe zaɓe ba, Matawalle ne ya ɗaga shi ya ba shi dama da mukamai, amma daga baya sai ya zama ma ci amana da neman kawo rarrabuwar kawuna a jam’iyyar.

A cewar kungiyar, maganganun Dr Shinkafi na baya-bayan nan kan Matawalle tamkar ihu ne na ɗan siyasar da ya rasa jama’a, domin yanzu babu wanda ke tare da shi, hatta wadanda s**a taɓa ruɗuwa da shi sun bar shi. Haka kuma tarihinsa na tsalle daga jam’iyya zuwa jam’iyya domin neman kuɗi da suna, ya tabbatar da cewa babu ainihin akida, nagarta a siyasarsa.

Kungiyar ta matasan APCn ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga Dr. Bello Muhammad Matawalle, tana mai cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma minista a ma'aikatar tsaron Nijeriya a halin yanzu ya nuna nagarta, kishin ƙasa da aminci ga jam’iyya.

Hakazalika, kungiyar ta kuma gargadi Dr Shinkafi da ya daina amfani da ƙarya da farfaganda don neman kulawa, tana mai cewa lokacinsa a siyasa ya ƙare. Sannan kuma kungiyar ba za ta lamunci irin waɗannan maganganu ba, kuma jam’iyyar ta APC a jihar Zamfara tana nan haɗe ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da Dr. Bello Matawalle.

Daga karshe, kungiyar ta kara da cewa, babu irin maganganu, bakin ciki daga wasu ‘yan siyasa da s**a gaza da za su hana jam’iyyar samun cikakkiyar nasara a zaɓen 2027.

BREAKING: Yanzu haka al'ummar garin jimrawa a Karamar Hukumar Kaura Namoda na Gudanar da Zanga-Zanga a Garin Gusau akan ...
31/07/2025

BREAKING: Yanzu haka al'ummar garin jimrawa a Karamar Hukumar Kaura Namoda na Gudanar da Zanga-Zanga a Garin Gusau akan matsalar Tsaro, suna kira ga Gwamna Dauda Lawal daya dawo cikin jiha ya fuskanci alummar sa ya kuma samar masu da tsaro kamar yadda yayyi alkawali.

Mace 34 Tare da Najimi 1 'Yan Ta'adda S**a yiwa Yankan Rago Garin Banga karamar hukumar ƙauran Namoda. Amma kullum Gwamn...
27/07/2025

Mace 34 Tare da Najimi 1 'Yan Ta'adda S**a yiwa Yankan Rago Garin Banga karamar hukumar ƙauran Namoda. Amma kullum Gwamna Dauda sai siyasa yakeyi da matsalar tsaro. Babban abunda yafi kwarewa dashi shine ta ina kudi zasu fito. Allah ya isa...

Allah ya kawo muna dauki 😭🙏

Innalillahi wa'inna ilaihi Rajiun!!Sarkin Katsinan Gusau, Dr Ibrahim Bello, Ya RasuAllah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau ...
25/07/2025

Innalillahi wa'inna ilaihi Rajiun!!

Sarkin Katsinan Gusau, Dr Ibrahim Bello, Ya Rasu

Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau a jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello, rasuwa yana da shekaru 71.

Marigayin ya rasu ne a yau, bayan ya jagoranci masarautar Gusau na tsawon shekaru goma. An nada shi a matsayin Sarkin Katsinan Gusau ranar 16 ga Maris, 2015, a lokacin mulkin tsohon Gwamna Abdul'aziz Yari.

A shekarar 2016, an taɓa yada jita-jitar rasuwarsa wadda daga bisani aka gano ba gaskiya bace, kamar yadda gidan rediyon tarayya FRCN ya tabbatar a wancan lokaci.

Dr Ibrahim Bello ya shahara da kishin al’umma da zaman lafiya a masarautarsa, kuma ana masa kallon shugaba mai hangen nesa da saukin kai.

Allah Ya jikansa da rahma, Ya ba masarautar Gusau hakurin jure rashin sa.

AN SAKE ZAUNA TEBURIN SULHU DA BELLO TURJI A KARAMAR HUKUMAR SHINKAFI JIHAR ZAMFARA. Daga Abdulmumeni Muhammad Kwaren Sh...
04/01/2025

AN SAKE ZAUNA TEBURIN SULHU DA BELLO TURJI A KARAMAR HUKUMAR SHINKAFI JIHAR ZAMFARA.

Daga Abdulmumeni Muhammad Kwaren Shinkafi

Kasawar Gwamanatin Najeriya kan Harkokin tsaro tare da Nazari akan Matakan da Dan Binding Bello Turji ya dauka bayan K**a Bako Wurgi

Al'umma Yankin Shinkafi sun Sake daidaitawa Tsakanin su da Kasurgumin Dan Ta'adda Bello Turji bayan yayi Barazanar Tarwatsa wasu Yankunan Zamfara, Sokoto da Katsina.

Kasa da Mako biyu da Bello Turji ya fitar da Faifan Bidiyon da yake ikirarin Zaa Shiga sabuwar Shekara ta 2025, Cikin Hare -haren Ta'addanci, Bello Turji yayi Garkuwa da Sama da mutane Dari da Hamsin (150) da raunata wasu da dama a garuruwan Shinkafi, Badarawa, Maberaya da Shanawa duk a Karamar Hukumar ta Shinkafi.

Al'ummar Yankin Sun Zargi Hukumomin Najeriya da Nuna Halin Ko inkula da Lamarin Bello Turji Lura da tun Ranar da ya fitar da Faifan Bidiyon babu wani matakai da aka dauka na dakile yiyuwar Hare Haren Turjin.

Wannan ya sake Jefa al'ummar Wannan yanki Cikin Tashin Hankali da firgici.

Saboda Nuna Halin Ko inkula da Daukar mataki da Hukumomi S**ayi Yau Assabar 4/01/2024 An sake Zama Teburin Sulhu da Bello Turji da wasu daga Cikin Shugabbnin da Malammai a garin Shinkafi Kuma Ancimma daidato Akan Bello Turji ya jaye maganganunsa Kuma bazaasake kamawa Ko Kai Hare hare a yankunan Tare da Sharadin Suma Fulani Zasu cigaba da Yawata Lungu da Sako Batare da Tsangwama ba.

26/10/2024

Breaking: Jihar Zamfara ta kashe N12bn akan harkan tsaro a Wannan Shekarar Ta 2024?

Kuna ganin ankashe wadannan makuddan kudi?

INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN 😪 Ayau talata 02/7/2024Anyi jana'izar Askarawan da Allah yakarbi rayuwar su mutun uku, ...
02/07/2024

INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN 😪

Ayau talata 02/7/2024
Anyi jana'izar Askarawan da Allah yakarbi rayuwar su mutun uku, DAN IGGE GAMBANDA, ABUBAKAR ABULE GAMO da kuma LAUWALI DAN HAURE GUMMI.

Muna rokon Allah yayimusu rahama Allah yakarbi bakunchinsu Allah yasa mutuwa hutuce agaresu ya kuma kyautata bayan su.

Ubangiji Allah yasa gwamnan Zamfara ya taimaki iyalan da s**a bari akan kokarin su na kariyar alumma. Shi kuma gwamna da yat shiga gidan radiyo na BBC Hausa yacce an samu tsaro kaso 75 cikin 100 kuma har yaci "A", Allah kayiwa yan uwan mu sakayya gareshi dashi da masu jin dadi.

INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN 😪 Sübhanallah 😭 Mutanen Duhuwar Adabka Kenan Dake A Karamar Hukumar Mulkin Bukkuyum Da ...
01/07/2024

INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN 😪

Sübhanallah 😭 Mutanen Duhuwar Adabka Kenan Dake A Karamar Hukumar Mulkin Bukkuyum Da Yan Bindiga Sunyiwa Mutane 6 Kisan Gilla A Lokacin Suna Aikin Gona 😭 A Yau Muna Rokon Ubangiji Allah Yakarbi Shahadarsu Yakuma Bamu Kariya.

Ubangiji Allah ya isarwa alummar jihar Zamfara ga Gwamna Dauda Lawal Dare akan cew jihar Zamfara an samu tsaro da kashi 75 cikin 100.

INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN 😪 Yanzu Yanzu yan bindiga sun kashe Police kwara biyar a garin Magarya dake karamar huk...
05/06/2024

INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN 😪
Yanzu Yanzu yan bindiga sun kashe Police kwara biyar a garin Magarya dake karamar hukumar mulkin Zurmi.

Innalillah WainnaIlaihi Rajiun!!Munfi ganin kima da darajar wadannan gawawwakin alummar fiye da titunan da Gov. Dauda La...
05/06/2024

Innalillah WainnaIlaihi Rajiun!!

Munfi ganin kima da darajar wadannan gawawwakin alummar fiye da titunan da Gov. Dauda Lawal yayyiwa kwaskwarima a Gusau. An Kammala sallatar gawarwarki 22 da 'yan ta'adda na yiwa kisan gilla a garin ruwan dawa Dake Karkashin Gundumar Magami a karamar hukumar mulkin Gusau Dake jahar Zamfara.

Ubangiji Allah Ka gafarta maku da rahama, Allah shi Karbi shahadar ku, Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gare ku.

Allah kayi muna arzikin wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Cikin Jummami muna sanar da al’ummar mu cewa Jiya cikin dare wasu Mutane da ake kyautata ceawa bandits ne sun shigo Ungu...
30/05/2024

Cikin Jummami muna sanar da al’ummar mu cewa Jiya cikin dare wasu Mutane da ake kyautata ceawa bandits ne sun shigo Unguwar mu Motorgaje nan Gusau,

Sun kashe Dan Dan Alh Musa Mallaha Abdulmunaf tare da Garkuwa da Mu’awwiyya Lawali Mallaha da wasu diyan Makwabtan mu,da kuma kashe Maigadi Guda.

Allah ya Jikan shi da Rahama,
Allah ya yi wa waddan da aka dauka da duk wanda ke hannun waddan mutane mafita,

Ya Allah ka kawo muna saukin wannan Mussiba.

23/05/2024DAGA ANKA ZUWA MAYANCHI BARAYIN DAJIN SUN TARE HANYA.Innalillahi Wainnailaihi Rajiun X3Barayi Daji Sun Budema ...
23/05/2024

23/05/2024

DAGA ANKA ZUWA MAYANCHI BARAYIN DAJIN SUN TARE HANYA.

Innalillahi Wainnailaihi Rajiun X3

Barayi Daji Sun Budema Tawaga Mai Girma Chairman Zamfara State Universal Basic Education Board UBEB Wuta Akan Hanya su Daga Anka Zuwa Mayanchi Yanzu.

Daga Ciki Tawaga Hon. Nasir Anka Garba Wanda Aka Halba Alhaji Sha'aibu Engineer Anka Amma Cikin Ikon Allah da Sauki Don Babu Hasara Rai ko Daya.

Muna Rokon Allah ka Bamu Zaman Lafiya Mai Dorewa a Jahar Zamfara da Kasa Baki Daya Allah Shikara Tsaremu Daga Sherin su a Duk Inda Muke Don Daraja Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S A W) Ameeen.

Address

Gusau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamfara Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category